WATA RANA Romantic hausa novels complete

Cikin wani irin sauti gaba dayan su suka mai da hnkalin su inda su kejin sautin.
“Ido biyu yyi daita cikin wani tattausan less Wanda fadin kudinsa baxa fadi ba fuskarsa tasha make up!!
Kallo daya zakayi mata kaga amarya ..bbu laifi tana da kyau na ban mmki..
Kai tsaye ta tun karesu da sauri hajja ta dauke kanta itakam Allah ya gani bata son Aliya da jikanta .” nan ina tarbiya take??”
Wannan rashin tarbiya har ina ace amarya ta biyo ango har gidan su.”
Barka da gida hajja!
Aliya tayi saurin katse ma hajja tunani ,tareda yin masauki dae daga cikin kujorun dake ,xagaye da falon kannan mahaifinsa kuwa ko kallonsu batayi ba.” Aunty salma da Aunty sadiya sae sakon harara suke aika mata Allah ya gani basa son Aliya da Abdul jabbar!
“Jabbar !!
I want to speak yhu in Private !
Not now Aliya!
Muyi mgana xuwa anjima mganar yana da muhimmanci honey dama A……stop it !
I don’t wan’t to hear all of dis.”
I don’t want 2 plzzzzz leave me a lone….ya fada in a angrily voice nasa ,just gooooooo out of my side “A fusace Aliya tabar part din na hajja cikin wani irin fushi…
Asmy????
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu.
©Haske Writer’s Association.????
3
Alh. Sameer meera haifaffen Dan garin Bauchi ne hka kuma dan siyasa Dan kasuwa yyi ya rika mukamai da dama ya rika mukamin senate Dan majalisa hka aka gangaro kan governor ya xauna a kujerar governor. ”
Bayan ya sauka ya fada harka kasuwan ci inda ya buda wani babban company na motoci da sunan sa ( *Sameer meera motors*)
(( *Sameer meera petroleum*)) da sauran companies waya’ndda ake ji dasu a kasar nan Alh. Sameer meera yyi fice a kasar nan Nigeria da wajen ta hka mutunen mai tausayin gaske ,Sam Sam baya kyankyamin tallakka A kullum gidan sa cike yake dam da mutanen Arziki.
Haka yana da manya-manyan gonakki wandda a duk shekara yake nome amfanin gona mai yawan gaske ,anan take ake lodasu a fita dasu kasuwan ci garuruwa daban-daban
Masu karatu zakuyi mmki idan nace maku duk wannan dukia dake da Sameer meera ,shi daya ne dal A gurin mahaifinsa Wandda yake a matsayin da namiji ,sae mata kwaya biyu da suke bimasa sadiya itake bima Sameer meera akwae shekara 5 a tsakanin su sannan Salma wadda take bima sadiya ita kuma shekara 2 ne a tsakanin su ” xo kuga yarda Dan uwansu ke nuna masu so tun suna yara Dan maifin sameer meera ya rasu tun yana da shekera goma sha takwas a dunia.”
Bbu laifi muha’d meera yabar masu dukia shema ba ‘a hka yake bane shahararren Dan kasuwa ne ,hka ya mallaki gonakki ” tun kaka da kakan ni bayan rasuwar mahaifin su ,mahaifiyar su Hajia Asma’u macce mai sanin ya kamata mai kokarin hada kan ya’yanta ta cigaba da basu tarbiya inda sameer meera a UK. Yyi karatunsa inda ya karatu a fannin kasuwanci…
A gurguje Sameer meera yana da matar aure kwaya daya Hajia laila ,asalinta barabiya CE ya’r kasar misra A saudiya suka hadu da Sameer meera a nan suka fara soyayya bayan dawowarsa ,gida Nigeria ya tuntubi hajiar sa da xancen Duk da yana fargabar hajjah dinsa baxata amince masa ba .”
Amma ga mmkinsa sae yaga tayi masa fatan Alkhairi hka ma su sadiya da salma lokacin ita sadiya tana aji shidda na secondary skull.” Yyinda salma take aji ukku na secondary ..
Bayan Auren sameer da lailah ,ya daukota cikin ya’n uwan ta ya kawo ta garin Bauchi inda ya Gina wani babban Estate ,dake unguwar namadi Azikwe .
Wandda shine suke ciki aurensa arxikinsa ya Dada habaka “yana rayuwa ne acikin gidan shida matarsa mahaifitarsa kanninsa ,shekara daya da auren sa aka samu cikin Abdul jabbar xo kuga tsananin son da Hajia Asma’u ke nuna ma Lailah bayan wata Tara ,ta haifi Dan ta namiji mai kama da mahaifiyar sa sak!!
Dan a zahirin gaskiyya sameer meera bakin mutum ne sae dai yana da kyau ,Anyi shagalin suna anyi bidiri tamkar ba’a san xafin naira ba.”
Shekarar Abdul jabbar biyar A dunia lokaci daya aka yima Sadiya aure da wani ma’akacin banki abokin Sameer meera ne ,lokacin hidimar kula da Abdul jabbar ya dawo gurin salma wankan sa Abincinsa shirin makarantar sa gabadae salma keyinsa Dan yarda suke nuna ma Dan Dan uwan nasu So!
Shekarar Abdul jabbar goma cif ! A dunia lokacin laila na da tsohon ciki a jikinta cikin bakaramin wahala yake bata ba ,bayan haihuwar ta da kwana biyu rai yyi halinsa bmutuwar ta girgixa sameer meera inda ta haifi kyakkyawar ya’rta mai kama da uban hka aka radawa ya’r sunan lailah Abdul jabbar shima mutuwar ta girgixa sa inda ya dauki son dunia ya daurawa Ya’r kanwar tasa …
Tun tana karama yake kiranta da Mimi..hka sunan ya cigaba da binta shekarar ta biyu a dunia ,ana shayar da ita madarar yara lokacin kuma Mr.sameer meera ya dauke Abdul jabbar ya kaisa UK. Karatu..
*****************
Bayan shekara goma sha biyar. A hka Abdul jabbar ya cigaba da karatun sa a UK …acan ya gama secondary skull inda ya fada jamia ,yna da shekara Ashirin A dunia yaxo Nigeria ya samu mahaifinsa ya aure wata ya’r kasar nupawa amma a Bauchi ,take rayuwar ta Hajia jummai Hka kuma lokacin mahaifinsa ya tsun duma cikin siyasa ,yarda yaga Hajia jummai na tsananin kulawa da Mimi ysa ya saki jiki daita wandda a zahirin gaskiyya a xuciyar Hajia jummai ba hka bane ” tana son duka ta saye xuciyar ya’n gidan ne kafin ta fito masu da ainahin kalan ta na gaskiyya .”
Sameer meera yana matukar son Hajia jummai musamman irin kyautatawar da take yiwa ,mima Dan a lokacin Aunty salma tariga tayi aure inda take auren Wani professor wandda Dan kano ne hka yana aiki a nan jami’ar Ahmad bello …
Jinin kanin mijin nata ko kadan bai hadu ba.” Basa kaunarta hka ma mahaifiyar su Hajia Asma’u kawae dae kullum. Tana ma Dan ta Addu’a Allah ya karesa da sharrin mutum.”
Da na Aljan haka kuma a lokacin yana cikin tsakiyar siyasa , wannan xuwan da yyi Abdul jabbar yaga gata sosae gurin matar uban nasa .” da yake shi ba mutunen ne mai son hayaniya ba da kuma son fada komae nasa cikin sanyi yake yin sa haka yake tun yana karamin sa ..
Da hajja tamasa complain din matar ubansa murmusawa kurum.yyi inda yake cemata hajja mom bata da matsala bakiga yarda takeson mima bane ,kawae dae keda su Aunty ne Baku fahimce taba.
Baki so mom ta kawo maki jikoki ??
A wasance xata jefesa da filo tace Allah ya raba Sameer dinta .”bata ma so mom ta haihu da Sameer ….ya kanyi daria yace hajja rigimar ki yawaaa garesa.”
Cikin hka Mimi ta shiga Aji daya na secondary skull..da hka shikuma Abdul jabbar ya koma UK.
***********
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu.
©Haske writer’s Association.????
4
Abdul jabbar yana shekarar karshe A jami’r ta UK.inda shima yyi karatu a fannin kasuwan ci ne kwatsam yaji rasuwar mutuwar mahaifinsa “mutuwar da ta girgixa tunanin sa ta haifar masa da ciwon zuciya wandda sae da ya kwanta gadon Asibiti shekara biyu ya kamu da tsananin ciwon zuciya.”
Da kyar da Addu’a da sadaka Hajja tasamu jikanta ya dawo lpia wandda a shekarar da ya tashi ,sae da hajja tasa sukaje umra duka har mima lokacin tana aji 6 na secondary ”
Da yake shima Abdul jabbar ba banxa bane gurin Addinin Islam ya samesa sosae ,haka yyi ma mahaifinsa Addu’a da mahaifiyar sa sosae.
Shekara ukku da mutuwar mahaifinsa ,ya koma UK. Ya cigaba da karatunsa Dan da yanxu ya gama shekarar sa hudu acan ya samu ya hada masters dinsa ,ya tattaro ya dawo Nigeria.