Romantic Hausa Novels

WATA RANA Romantic hausa novels complete

” Rahama bansan Mae ke shirin faruwa dani ba ina yima sa wani irin sone wandda Allah kadae yasan yawan sa Anan ta shiga labartawa kawarta ta mai ya faru ,haka Rahama ta dinga hango tashin hankali acikin idanunta.”

Batayi Aune ba hawaye suka ziraro akan kuncinta haka taji xuciyar ta ma wani irin kuna hnnunta ta hade gamida xubewa agaban Rahama hawayenta kuma tamkar ruwan fanfo.”

Plzzz ????Rahama ki tayani shawo kan Em.tun jia nake Neman wyarsa yaki ya daga ki kiramin shi a wyarki ki tambayesa laipin me nayi masa??” Idan ya fada maki nayi alkawari xan basa hkuri plzzzz Rahama ki taimakeni ,baki wangalu Rahama ta saki tana kallon kawarta ta hka taji ranta yyi balain baci wannan wane irin balai ne wani irin sone take ma Emran din nan da take Neman xaucewa akansa.”..

“Shaye da toka Rahama ta kalli kawarta ta Dama kin daina rokona kin San bana son wannan Emran din tun farko baiyimin ba .” Asma’u  idan mafarki kikeyi ya kamata ki farka.

Emran ba son tsakani da Allah yake maki ba.” Cikin daga murya da xafin rai Asmy ta katse kawar tata idan baxaki yimin wannan Alfarmar ba ki kyaleni da surutunki Mae haifar min da ciwon kai plzzz …na Rokeki zanje na samu yah Al’ameen xan fada masa damuwa ta nasan xai fuskance ni hawayen idonta tayi saurin gogewa gamida daukar hijab dinta tayi hnyar fita dga dakin.”

Cike da tashin hnkali Rahama tasha gaban kawar tata.”

“Tabbas da tasan irin yarda yah Al’ameen ke sonta da baxata tunkaresa da xancen Nan ba.”

“Am sorry dawo kiji xan kira mki shi Anan ta daga wya tana Neman layin Emran ” Ta fiso ta kirasa A wyarta da dae ta Fama ma yayan nata ciwon dake addabarsa shekara da shekaru.”..

WATA RANA !

N@ Asmy b Aliyu.

©Haske Writer’s Association….

27

Zubama kawarta ta ido tayi wadda ke famar Neman layin Em. Kusan kira biyu bae daga ba.Rahama ta kalleta “A sanyayye kinga bae daga ba wata kila baya kusa ne!!.

” Ta fada tana kallonta Asmy bata ce komae ba ta jawo wyarta ta kunna ,Anan kuma ta dinga cin karo da test message’s din Em.dinta na ban hkuri ne da kuma kalaman soyayya masu sanyaya zuciya.”

Fara’a sosae ta hauyi washe da baki ta kalli Rahama cikin wani irin farin ciki marar misiltuwa ta mika ma Rahama wyar anan ta shiga ,karanta sakon nasa, Wanda ta basa suna Kalaman yaudara.”

A zuciya ta mika mata wyar gamida Dan Jan guntun tsuka.”

“Rahama nayi farin ciki sosae ynxu ma na nemi ciwona na rasa ,muje naga yah Al’ameen Rahama ta tabe baki ynxu kuma mexaki fadama su mama?? kina  nufin fada  masu zakiyi kin tashi dga ciwon wahalalliyr soyayyar da kike yiwa wannan yaron ko kuwa??”..

Wlhil azeem Asma’u watarana kunya kike bani yarda kk haukace akan wannan yaron dama ko kadan ,ba sa’an auren ki bane!!

” Yah isheki Rahama!!

Asmy ta katseta cikin tsawa ke baki isa ki hanani son abunda xuciyata ke soba.” Idan baxaki tayani son abunda na keso ba sae kija bakin ki kiyi shuru.”

“Dan shine kike min tsawa da ihu akae sae kace wata uwata??” Rahama ta fada cike da bacin rae ohkey ! Asmy na daina shiga sabgar ki keda wannan yaron Kekika sani Amma karki manta “A WATA RANA !! Sae kin tuna dani Mae fada maki gaskiya ce a koda yaushe anan tabar mata dakin a zuciya Allah yasa bbu wandda ya ganta da haka ta fice dga gidan rae a bace.”

“Tana sawo kae kofar gidan su taci karo da yayan nata ganinta hka ya daga masa hnkali karasowa gurinta yyi Dan ba karamin ji yakeyi daita ba.”..

Rahama meya sameki hka??”

A sanyayye ta kalli yayan nata tana tausaya masa ,tana tausayawa yanayin da zai shiga muddin yaji Asma’u na soyayya da wani .”.

Bbu komae yaya ina zuwa haka ??” Ynxu har akwae damuwar da xaki iya boyemin plzzz fada min meye matsalar??”

Hnnunsa taja zo muje yah Al’ameen kaji hka tajasa tamkar karamin yaro har xuwa side dinsa .”

“A falonsa sukayi masauki zuba masa ido tayi na Dan wani lokaci yah Al’ameen !!

‘Ta kira sunan sa cikin wata irin murya .”

Na’am Rahama!.” Ya amsata gamida zuba mata ido.”

“Mexai hana ka fadawa Asma’u irin dumbin kaunar da kake yimata ??” Ganin nayi boye-boye baya da Amfani ina tsoron karka rasa ta yayah!

“Ta fada idonta cike da kwallah.’

Meya kawo wannan mganar Rahama?? Ya fada cike da tashin hnkali anan ta labarta masa soyayyar da Asma’u keyi da yayan kawar su …

Nan take ta hango tashin hnkali acikin idanunsa ,sae dae yyi saurin kawar da damuwar sa karki damu Sistr xamuyi mgana daita xuwa anjima.”

“Da fara’a ta kallesa da gaske kakeyi yah Al’ameen??

Daga mata kai yyi alamr Ehhh.” Yawwa yayana Allah yabaka sa’a bana son karasa Asma’u baxan ma rasata ba Rahama “yah fada cikin wani irin yanayi .

★★★

” An kawo lefe aunty shema saiti goma sha biyu kaya masha allahu ,sunyi kyau da yake shima Faisal iyayensa suna da kudi.”

“Da karfe shidda na fito daga gidan mu xuwa gidan su Rahama nasan tunda banganta ba tayi fushi ne .”

Dae-dae kuma lokacin na hango ya Al’ameen cikin mota da alamr fita xaya yi ,ganina yasa ya fito daga motar cike da farin ciki na karasa garesa da nupi na rungumesa ,Dan na jima  ban gansa ba kasancewar bai fiye xuwa ba Dan “A sokoto yake aiki.”

Sae yyi saurin kaucewa yana daria kae kae my Ma’u ynxu kin girma sunan da yake kirana dashi kenan .”

Sae nayi folding din hnnuna akan kirjina na bata rae gamida turo baki cike da shagawaba ,sae yyi daria wadda tasa naga yyimin kyau.”

“Dan yah Al’ameen karshe ne gurin kyau cikakken bafulatanin Asalin dogone sanbal haka yana da kaurin jiki sae kasumbar da ya Tara baka wuluk wadda takara yimasa kyau.”

Ko Rahama baxata Nuna ma yah Al’ameen kyau ba.”

Haba ke kuwa my Fulani gal!!

In banda ke da abunki wake fushi da babban yayansa ,to bakai bane ka hanani na nuna maka murnar ganinka “kin girma Ma’u na wannan sae su Afra ,yah Al’ameen meye sirrin ne wae??

Naga ka aza tumbi gaskiyya yakamata ace xuwa wannan tym.” Din kuxo Ku aje iyali kaida yah hameed ,Dan na tabbata bbu maccen da xata kiku…

Daria Al’ameen yyi ya langabar da kansa yana kallonta shikam yana son komae nata yana son life style dinta .”baka taba ganinta cikin damuwa ,nikam tuni nayi mata! Amma ban sani ba ko xata soni ina tsoron tunkarar tane.

Zaro ido tayi gamida dafe kirji wacece wannan ka fada min ita bata isa taki son yayana ba! Tayi kadan plzz fadamin ita naje na sameta komae take ji dashi dole ta saukesa ta kularmin dakai.”

“Zuba mata ido yyi ganin yarda take murna a ransa yake fadin kece Asmy amma bansan taya xan fahimtar dake hakan ba.”

Hy!!

“Hohoho!!

Wallahi da alama yah Al’ameen kana tsoron budurwar nan taka , ji yarda ka rude lokaci daya plzzz muko ma cikin gida dole yau sae ka fada min damuwar ka !!

Ta Amshi car key dinsa ” ta shige motar ta gyara masa parking sannan taja hnnunsa suka nupi gidan su.[truncated by WhatsApp “].

WATA RANA !

N@ Asmy b Aliyu.

©Haske Writer’s Association…

28

“A cikin barandar gidan su sukayi masauqi bisa wasu fararen kujorun roba da aka kawata da wurin dama kuma anyi sune Dan zama.

Tana xaune kan kujera mai fuskantar sa ta xuba masa ido ta kagu taji wannan wace macce ce Mae sa’a har yah Al’ameen ya kamu da tsananin sonta haka??”.. Plzzz yah Al’ameen kayi shuru mana ka fada min ko so kake Abba ya dawo ya gammu anan??”..

” Ai nafison ya dawo ya samemu anan   nafiso ya ganmu atare dalili kuma na gaji da Jan ran da kike yimin plzzz Asma’u ki tsaida hnkalin ki guri daya.” Cikin rashin fahimta take kallon yayan nata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Leave a Reply

Back to top button