WATA RANA Romantic hausa novels complete

” kana ganin nayiwa mahaifana Adalci a rayuwar su sakamakon jin mganar su da banayi sabida kawae son zuciya na da soyayya yau na tabbata yau so bala,i ne bana tunanin xan kara son wani A rayuwata na tsani maza na tsanesu ta rushe da kuka mai taba xuciya haka ta saka kanta ajikin cinyoyinta yana jinta bai hanata kukan ba.”
“Amma yarasa fahimtr Mae kalaman ta ke nufi??”
Saurin taka burki yyi kiyiwa allah ki daina wannan kukan Na rokeki bakisan yarda kukan ki ke tabamin xuciya ba Ynxu fada min ina kikeson zuwa??
“Dago idonta tayi tana kallonsa na ya’n mintuna ganin yarda yake kallonta tayi saurin dauke kanta cikin muryar kuka take fadin bansan mexan fadawa daddy ba da yah Anas ba nasan mumin baxaka cutar dani ba ko gidan ku ne ka kaini xuwa gobe sae na tafi gida ta fada hawaye masu xafi suka gangaro akan kuncinta.”
Girgixa mata kai yyi alamr ta daina kuka wani irin sonta yakeji xuciya da ruhi ji yake tamkar ya jayota jikinsa ya lallasheta ko xaiji saukin abunda yakeji to “Amma ina bbu halin yin hka.
” Jiki sanyayye ya tada motar bata kara kallonsa ba ta dauke kanta gamida xubama titi ido.”
Nan gidan Auntyna ne komae xakiji na fada mata kawae kiyi shuru kina jina ??”
“Daga kanta tayi alamr to..
Kusan tare suka fito dga motar ita dai binshi kurum take aranta tana Addu’ar allah yasa ba mugu bane!
” Falon yyi tsit sae karar T.V. yana gaba tana binsa a baya dae- dae kuma lokacin Aunty salma ta karaso daga falon ganinsu tare yasa ta tsaya cak !
“Tana bin AJ da ido daga ina haka??” Na ta kiran wyarka bata shiga ,murmushi ya kwa’kwalo na Dan fita ne Aunty ga bakuwa nan na kawo xuwa gobe da safe kanwar Abokina ce biki taxo a garin nan kasancewar bata da kowa shiyasa ya kirani ya damka min Amanar ta cike da Fara’a Aunty salma ta mata sannu da xuwa .”
Nixan tafi na watsa Ruwa karki damu Asma’u Aunty salma na da kirki kisaki jikinki nan ma gidane washe da baki Aunty ta kalleta kice sunan ya’ta gareki Da kuma sunan hajiar mu ….kauda kai kurum Asmy tayi haka ta kwa’kwalo murmushin dole.
“Anan AJ. Yabarsu ya karasa masaukin sa.
Kusan karfe goma sha daya na dare ya dawo falon cikin farar jallabiya bae tarar da kowa a falon ba wya ya fiddo ya kira Aunty salma yah akayi ne Abdul jabbar??”
“Cewar Aunty salma ina dakin Abban su Nana Bakuwar ka kuma tana dakina.”
Ohkey tom.”
Saurin datse kiran yyi kai tsaye dakin ya nufa murda kofar dakin yyi da sallama hangota yyi kan Sallaya da alamr sallah ta idar Kan bedside drower ya xauna gamida Dan xuba mata ido .”
Kana son wani Abune??”Ta fada tana kallonsa girgixa kai yyi alamr A’ah kinki cin Abincin da Aunty ta kawo maki ko. Baiyi maki bane??”
Ya fada cikin sanyayyar muryarsa bana jin yinwa ne ta basa amsa batareda ta kallesa ba.”
Baxai yuyuba.!!
“Tana mmkin karfin halinsa ,murmushi ta danyi kadan mexai hana ya yuyu mumin tunda ni ba y’arka bace da zakayimin dure.”
“Ta fada gamida dan turo baki girgixa kai yyi gamida sakin guntun murmushi baxata ta bata canjawa ba.” Duk da kuwa tana cikin damuwa.”
“Nifa ki daina cemin *MUMIN*”…
Ba shine suna na ba koma dae meye sunan naka ni ina ruwana da na sansa kawae dae nasan kana da kirki ba irin Mln Nura muguba !!
” Dan haka dole ka karbi sunan ka mumin tom.naji na karba kici abinci plzzz karki xauna da yinwa aciki tayi ma lpiar ki illah..
Karka wahalar da kanka plzzzz idan dae xan samu coffee xan iya sha shi kike son sha ne??”
Saurin daga kanta tayi batareda ta kallesa ba “Angama my drama queen!!
Ya mike tsaye gamida yin hanyar fita daga dakin ” A sanyaye tabisa da kallo ….
*TEAM DRAMA QUEEN*..????
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu.
©Haske Writer’s Association..
_thank yhu for my beautiful birthday wishes! I fell grateful and Lucky to have so many amazing by my side ,I love yhu so much my biggest fan’s bohoot -bahoot shukriyah!!_*One love*#.
31
Hawaye masu xafin gaske suka sauko akan fuskarta tana jin ciwon abunda emran yyi mata har aranta haka tana jin zuciyar ta na yimata wani irin zafi.
“Ya dde tsaye akanta wandda yakai minti biyu a kanta bata ma San ya dawo ba.”
Cup coffee ne rike a hnnunsa samun kansa yyi da durkusawa a gabanta kamshin turaren da taji shiya sa ta dago jajjayen idanunta da sauri sukayi ido hudu dashi,saurin goge idonta tayi tareda dauke kanta .”A kansa Drama Queen!!
“Ya kira sunan ta cikin wata rikitacciyar murya bata kallesa ba .” bata kuma amsa masa ba baxaki amsa niba??”
“Yah fada A raunane niba drama queen ne sunana ba kanme zan amsa ka??”.. Saurin katseta yyi bana bukatar naji sunan ki da mmki take kallonsa yarda ya masa a daxu shine ya mata hakanan.”
“Am sorry da wannan sunan na sanki tun ranar da na fara Daura idanuna akanki.” Ganin zae canja xancen zuwa wata manufa wadda itakuma ko kadan bata son wata alaka Mae karfi ta hadasu shiyasa taja bakinta tayi shuri ta mika masa right nata ,gamida karbar cup din hnnunsa.”
Godia tamasa batareda ta kallesa ba tsam “ya mike tsaye yyi mata sae da safe Dan yaga da alamr batason mgana.”
_washe gari_”..
Tafia suke a mota shuru ya ratsa a tsakanin su sae kira’ar Mln shureem dake tashi a motar kowane da tunanin da yake sakawa a ransa.
“Gabda shiga layin gidan su tayi saurin tsaeda shi ganin motar yah Aliyu!!
Sae da zuciyarta ta kusan tsinkewa hka yasa tayi saurin dakatar da AJ.
” Ta kallesa hankalinta a tashe da kyar ta iya fada masa nagode . da haka ta balle marfin motar ta fito sauri sauri gudu -gudu ta tunkari gidan su zuba mata ido yyi yana zaune a mota yana kallon ikon Allah!
“Har ta bace daganin sa doguwar ajiar xuciya ya sauke yana ayyanawa a ((WATA RANA !)) Xasu xauna a karkashin innuwa daya a matsayin ma’aurata masu tsananin son junan su.”
Samun kansa yyi da Daura kansa akan sitari haka ya tsinci kansa acikin wani irin yanayi da kyar ya saita kansa ya Ciro waya ya dannawa Nura kira .”yana dagawa Tambayar sa ya somayi yana ina??”
Jin muryarsa wani iri yasa Nura yace lpian ka kuwa??”..
“Da sauqi dae ina gida amma xuwa 11 xan fita office ohkey gani nan karasowa .”
Yana aje wyar ya nufi gidan su Nura.
“Dai dai lokacin da ta karaso kofar gidan su Taga yah Aliyu tsaye shida Yah ” Al’amin lokaci daya kuma suka zuba mata ido ganin mugun kallon da yah Aliyu ke jifan ta dashi yasa ta fada cikin gida .
Hango motar daddy tayi a parking space’s da Alamr bai fita kasuwa ba sallama tayi a babban falo taci sa’a kowa na xaune a falon duka sunyi jugum !!
“Ganinta yasa duka suka mike tsaye zubewa nayi a tsakiyar falo haka hawayen idona suka kasa tsayawa ,gabadae kunyar iyayen nawa ta gama lullubeni “…
Shaye da toka daddy ya kalleni cikin daka min tsawa daga ina??”
Har kingama yawon karuwan cin naki!!
“Gabana naji ya fadi na kalli daddy na girgixa kai baki na rawa na bude baki da kyar nace Dan Allah daddy kayimin rai kaji kaina !!
” wallahi sharrin shaitan ne da kuma zuciya Daddy abunda kake nufi bashi ya faru dani ba!
“Ta karasa zancen cikin rawar murya Asma’u kin bani mmki sa’annan kin tozarta ni A idon dunia nayi tir da halinki wae yau ace ni da girmana da mutunci na ya’ta ta dauki kafa tabi wani da namiji A hotel !!
” kanki kika cuta Asma’u bamu ba mgana na ,”Na karshe dake na cireki daga makaranta idan itace tasa idonki ya bude haka bbu ke bbu zuwa jami’a nan da Sati biyu zan hada Aurenki keda Shema’u keda Al’ameen kafin nan xansa Aliyu yakaiki a bincika ki ko bakida cutar H.I.V.