WATA RANA Romantic hausa novels complete

Kallona suka tsayayi tamkar masu kallon talabijin ,Aunty shema taja tsaki gamida gallamin harara Ciwon haukan nata ya motsa kenan??”
“Cewar Aunty shema aunty zulfa ta amshe xancen da fadin Da alamr na kara sakin ihu nace ina ruwanku munafukkai nikam anriga an gama dani Ancuce ni tunda aka hadani Aure da yah Al’ameen.”
“Uban waye ya cuceki??Cewar yah Anas Wanda ya ratso cikin dakin nawa ,da duk wandda ya hadani Aure da yah Al’ameen ido bude yah Anas ke kallonta.” Wato uban namu ne ya cuceki kenan??…
“Belt ya cire ya shiga jibagata dashi yana dukana wandda xankira da dukan mutuwa Wanda tunda Allah ya halicce ni ba’a taba yimin makamancin saba.”
Bbu mai kwatata a hnnun yah Anas Sae jin nayi an rike yah Anas gagam.” Ana fadin yah Anas gani ka dakeni kadaina dukarmin kanwa karka kashemin ita tunda Ku bakwa sonta ni ina sonta !
“Muryar (ABDUL HAMEED OMAR OMRA”) naji tana yimin yawo a kwakwalwa ta Anan wurin kuma na fadi A some…
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu.
©Haske Writer’s Association..
33
“Hameed Omra ne yyi saurin tarota a jikinsa ya kalli Yah Anas hankali a tashe yace shikenan ka kasheta yah Anas!
” Idan wani Abu ya sami kanwata bazan taba yafema kuba.” Yah Anas yyi tsaki kanku akeji dama ae kalan haukan Ku daya indaan akuyan gaba tasha ruwa tana baya kesha.
“A fusace Yan Anas yabar dakin gamida bugo masu kofar A hnkali ya kwantar daita kan gado da gudu ya sauka kasa yana kwalama shema’u kira cikin hargagi da kunar rae.”
“A tsorace ta fito lpia yah Hameed irin wannan kira haka ??” ya galla mata hara Dan Allah bani ruwa masu sanyi a fridge .” munafukan banza munafukkan wofi wlhi idan wani Abu ya sami kanwata baxan barku ba.”
“Ya fisgi gorar ruwan hnnunta ya koma sama da gudu mama bin Dan nata tayi da kallo.
Tallabo fuskarta yyi ya bude gorar ruwa gamida Dan xubasu a hnnunta yana Shafa mata a fuskar haka yana tofa mata ayautul kursiyu Ajiyar zuciya ta fara saukewa da karfi tafi minti biyar a haka kafin tayi nasarar bude idonta wandda suka kumbura gamida fuskarta da tayi sukutum!!
Asma’u sannu kinji.” Ya fada cikin so da kulawa kokarin mikewa take ya hanata zubama ta ido yyi gaba dae ta canja ,tafita hayacinta sae kace ba Asmy ba ya’r gayu “yanxu ba wannan gayun…
” Yayah Hameed!!
Ta fada hawaye suka gangaro daga idonta .Ina ka shiga??” tsawon wannan lokacin kabar rayuwata cikin wahala gaba dae gidan nan nasan ba’a kaunata kai kawae ke sona!
“Plzzz karka bari Daddy ya auramin yah Al’ameen yi shuru haka Asmy taimakeni ynxu kiyi wnka yanxu xanje na hada maki break fast kinji karki damu bbu maiyi maki Auren dole muddin ina Raye.”
“Taimaka mata yyi ta Mike tsaye Yabar dakin itakuma ta rage kayan jikinta ta fada ban daki danbin umurnin yayan nata..”
Haka Hameed ya tube ya dawo daga shi sae Tree quarter da farar singlet ya fada kiching su Aunty shema sae gulmarsa sukeyi kasa-kasa suna daria mama ta dubesa me xakayi haka kiching Abdul Hameed ??”
Idan wani Abu kakeso baxakayi ma su zulfa magana ba su hada maka meye “Amfanin su??…kibarsu kawae mama xan hada mata da kaina tunda bbu Wanda ya damu daita ni Ae na damu daita gani na dawo zan cigaba da kula da Abuta.”
“Daria Abun yabawa mama tabbas kaunar Hameed da Asm’au daga rabbil izzati ne badan sun fito ciki daya ba da sae tace Hameed din son Aure yakewa kanwar tasa.”
“Da haka Mama taja bakin ta tayi shuru hakama ,aunty taxo ta sami Hameed din A kiching tambaya dayace haka Amsa daya Dan haka suka xubama sa ido ….
Kusan kawae Shidda ya soyama kanwar tasa sa’anan ya soyamata Dan kalin turawa sa’annan ya hada mata Tea.
” Daga kiching ya dinga kwalawa Zulfa’u kira sae gata da sauri ta shigo kiching din gani yaya!
“Daukar min ki kai Dakin Asma’u bbu musu ta dauki kulan Dankalin da plat shin kuma ya dauki flask da cups nashan tea haka yaxo ya wuce mama .”
Sau mazurai yakeyi yana hawa kan stairs Shema takasa rike daria cikinta …tako kyalkyale da daria wayyo ! Cikina yau ga likita da shiga kiching !
“Hahhhhhhhh !
Kasa- kasa take dariar tata Dan tana tsoron yajita yaci kaniyar ta ,tana cikin shadda galila doguwar Riga tana parking din gashin kanta sae gaya sun shigo .”
“Anan zulfa ta galla mata harara bata kulata ba ta maida hankalinta kan yayan nata sannu da aiki Yayana! Yawwa kanwata kinga yarda kikayi kyau ko kefa ,ynxu kika fito Ainahin Nana Asma’ul husna sak!???????? ” murmushi tayiwa yayan nata zulfa anan ta wuce tabar su bara naje nayi wanka naxo muyi break fast “..ni na hada mana break fast bama cin na gidan nan .” tunda basa sonmu ya karashe maganar yana kallonta.” Murmushi mai kyau tayi Dan haka nakeson ka yah Hameed dina kuma abokina ina sonka yayah Hameed!
“Yhu Are d best lovely brother in d World ” murmushin sa Mae kyau yyi mata nima haka kanwata bara naje na watsa ruwa anan ya fice daga dakin tabi yayan nata da kallon so Tabbas tasan baxa’ayi mata wannan Auren ba tunda yah Hameed nata yana Raye.”
********
“Tare sukayi break fast da yayan nata anan dakin ta.” bayan sun kammala ta kawalama mai aikin nasu kira taxo tattare gurin ,haka yah Hameed ya umurceta da taso suje Dayan falon daddy suyi magana mai’aiki ta Dan gyara mata dakin Dan yaga duk ya wani hargitse.”
Murmushi tayi gamida bin umurnin yayan nata .”..
“Duk cikin yayunta tafi jin mganarsa.
Suna xaune ” A falon daddy karami ya fuskanci Kanwar tasa Dan yana son yaji gaskiyyar lamari kafin ya dauki mataki bata boyemasa komae ba akan soyayyar sa da Emran ..”
“Yah Hameed nayi da nasanin Em ” A rayuwata nasan nayima su daddy laipi amma meyasa baxasu karbi uzurina bane??” Tunda a rayuwa bbu wandda baya kuskure kuma yaxo ya tuba.”A kayiwa mahaliccin mu laifi ya yafe balanta na Dan Adam.”
“Yah Hameed wannan hukuncin na daddy baiyi min dadi ba ko kadan bana bukatar wani da namiji acikin Rayuwata a halin yanxu burina baifi na koma makaranta ba .” Dama can Al’ameen ya taba fadin yana sonki??”
“Tambayar da yayan nata yyi mata kenan,a kwanakkin baya nasan muyi mganar Amma.ban boye masa komae ba bana jin soyayyar sa yah Hameed A raina lokacin ma muna tare da Em.” Ina ga yanxu da abubuwa suka rikice …..”
“Hawaye suka gangaro akan Kuncinta na tabbata koda baka goyon bayana yah Hameed baxanyi wannan auren ba sae dae kuyi gunduwa gunduwa dani ,ta sharbe majinar hancinta sassauta murya yyi Haba Nana ta bansan Asmy da kafiya hakaba.” Kinga shi Al’ameen din yana sonki fa kuma xakiyi farin ciki a gidan sa na tabbata kodan Amintar mu dashi xai rikemin kanwata da Amana ! Kiyi hkuri Da auren nan.ki Rungumi kaddarar ki Nana Asma’u na tabbata “(WATA RANA!)) Zakiyi Alfahari da Auren Al’amin kinji Ma’u na!!
Kuka na fashema da yah Hameed dashi lokaci daya na birkice masa ,ganin da gaske yakeyi ….
” Na rantse maka da Alllah Mr.Hameed Omra koda “Gunduwa -Gunduwa xakuyi dani baxanyi Auren nan ba nafiso Ku babbaka ni A gidan nan ta fada tana sharbar hawaye baki wangalau ya saki yana kallon Kanwar tasa baitaba ganin fitinanniya irinta ba …ta Fiye rigima da yawa Sam mai sunan ta ba haka takeba.”
Bbu musu Hameed ya langabar dakai yana kallon kanwar tasa murya kasa kasa yake fadin,Abun baikai can ba Mrs.Omra bbu wandda ya isa yyi miki dole.”
*”TEAM ASMA’U OMAR OMAR*….????