WATA RANA Romantic hausa novels complete

Ya fada cikin muryarsa tamarasa lpia ..”kema kin yarda da abunda Nura ya fada kan wani dalili nasa na banza zae Dan ganta matar da nakeso fiye da komae “A dunia da karuwa !!! kitashi ki fita bana son ganin ki A kusa dani ya fada cikin tsawa tsawa ” A tsorace take kallonsa ….
Bakiji mai na fada ba kinenan ? ” Hannunta tasa ta rufe masa baki haka hawaye na zuba a idonta girgixa masa kai tayi alamr yyi shuru Dan Allah plZz na rokeka karka dagama kanka hankali “A fusace ya fisge hnnunta kan Bakinsa ..
” I said get out of my Room!!
Kosae na nuna maki ta ido gamida jinyatar dake sa’annan Auchhhhhh!! Dafe kansa yyi jin wani irin wani a zababben ciwon kai na gefe daya ,dae dae nan su hajja suka turo kofar dakin Rukaiyya bata tsaya ba tafice a dakin Da gudu tana kuka yyin da Hajja suka karasa gurinsa A tsorace …..
“Ya daga Jajjayen idonsa Yana kallon hajja Yana son yyi magana ya kasa Aunty Salma ta fita kiran likita da sauri…
*****
Nura ka taimakeni ka kaini gidan su Asma’u! Wae meke damun ki ne Rukaiyya??” kinsan kuwa wannan shaidaniyar?. na tabbata ko kallon ariziki baxaki samu” A wurinta ba .naji na dauka in dae xata saurareni indai xataji halin da Yah AJ. Yake nasan in dae Ita mai tausayi ce xata duba mgana ta Nura bana son ya rasata wllhi na Hakura da son Da nakeyi wa Yah AJ.” Indae har zan samo masa farin cikin sa Aza kanta tayi a jikin motar tana shesshekar Kuka.”
*TEAM AJ.” OR TEAM Al’Ameen*??”…..????
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu.
©Haske Writer’s Association…
36
“Gaba dae Ahalin Alh.umar omra suna a katafaren falon sa da misalin karfe Tara da rabi na dare.yyi gyaran murya sa’annan ya kalli Mama ” ya fara da fadin ke Khadija kinji Abunda ya’yanki suka yimin ko ??”
Mama da mmki take kallon Sa kamar ya ya’yana daddy.”??
“Ni dae na rokeka ka daina sanyoni cikin sha’ani Asma’u sabida ta Riga da tafi karfina ,shikuma Hameed din tunda bayajin mgana ta ya biye mata sae yaje yyi tayi .”
“Rai bace mama ta mike tsaye zatabar falon yyi saurin da katar daita ya gano fushi tayi.” Dawo kiji Khadija ,ae bamu gama mgana ba.”
“Bbu musu ta dawo ta zauna amma ran nan nata a hade Yah Anas ya gallama yah Hameed harara ina kallon yah Hameed din yyi murmushi gamida dauke kansa.”
Naji Abunda kace Abdul Hameed xan sassauta ma Asma’u da hukunci da na yanke Akanta amma fa Aure ne bbu fashi!
“Da sauri Asmy ta kalli yayan nata gamida yin ” rau rau da idonta. ”
“Ina Son ta kawomin wandda takeso din Xuwa gobe jibi xan hade Aurenta da na ya’n uwanta shi kuma Al’ameen sae ya auri zulfa ,Dan ni Asma’u ta gama zaman gidana .” cikin Tashin hnkali Asma’u ta bude baki da niyar tayiwa daddy magana Yah hameed yyi saurin,dakatar daita .” Hankali tashe take kallon yayan nata ..nan Yah Hameed yyiwa daddy godia yyinda hukuncin Da daddy ya yanke baiwa mama ddiba dasu .”Yah Anas …”
Cikin fushi yah Aliyu ke fadin Daddy Dan meye zaka biyema shirmen way’annan yaran ?? Kafiso ka faran tamasu kaji kunya a idon dunia??” Shin ya zakayi da Yaron nan Al’ameen da mahaifinsa??.. wannan ba matsala bane Babana! Nasan mahaifinsa xai fahimceni dashi kansa Al’ameen din ,zulfa’au kuwa nasan zatayi min biyayya!!
“Da haka taro ya watse mama taja tsaki bayan fitar yaran .” Daddy ka daina biyema wannan yarinyar wlhi to yanxu ina xata samo miji nan da kwana daya??” Ina fa jin hirar da sukeyi da Rahama aranar shi saurayin ma wandda takeso yaudarar ta yyi Dan tuni ya samu wata!
“A hnkali daddy ya kamo hnnun mama Yana murzawa a hnkali bansan Ki da fushi ba .” Nana Khadija ,Addu’a zakiyi mata su kuma ki zuba masu ido naga yarda zata samu miji nan da kwana daya .” tunda samun mijin wasa ne ba.”daita da yayan nata ba hankali ne dasu ba daga waya ki kiramin zulfa’u bbu musu mama ta nemi layin Aunty zulfa anan ta sanar mata kiran daddy din nasu.”
******
“A can kuma dakin Asmy hnkali tashe take kallon yayan nata!
” Idonta yyi Rau rau yah Hameed kaji daddy da wani sabon zance kuma??”
Ta fada cikin muryar son tayi kuka.”ni ina ruwana da wani namiji tunda nasamu ‘ya janye zancen hadani da yah Al’ameen. ”
“Baza’ayi haka ba husna! Kin dae San halin Daddy ,ki lallaba cikin samarin ki kisamo wani din wandda kin kasan zae rikemin ke Amana!!
” Hawaye suka silalo daga kan fuskarta Jin tayi mganar wani iri nabarki lpia kiyi tunani da kyau kanwata .” da haka yaja mata dakin fadawa tayi kan gado gamida Rushewa da kuka.” Itakam ta shiga ukku!! Ynxu ya zatayi da daddy ??….”
**************
Da misalin karfe goma sha daya na safe tafito falon cikin shigar “dinki Riga da skirt na Le’ss brown da Ratsin Milk a jikinsa ….sae Dan karamin veil milk Wanda ta yafa saman kanta handbag nata da hills shoes nata brown ne taci uban gayu sosae sae kace mai shirin xuwa Party ” Sae uban kamshi take zubawa ,cikin takunta na yanga da Jan hnkali ta iso falon gaba dan su suke xaune “A falon yyinda AJ. Ke shan Ruwan Lipton hka hajja na gefensa” Kamshin da sukaji yasa sukayi saurin Dagowa Akanta.”
“Anan ta gaishesu batareda Ta kalli AJ ba shima ko kallo bata ishesa ba.”..
Baxaki gaisheda Yayan naki da jiki ba??” Cewar hajja.”
”A hnkali ta turo Dan karamin bakinta ta gaishe sa bai ko kalleta ba ,Kai kanaji bazaka amsa Gaisuwar kanwar taka bane??” ………Shaye da toka yake fadin bana Amsa gaisuwar marar kunya tabe baki ,tayi gamida dauke kae.”
“Aunty Salma ke fadin yau kaida Rak! Din naka angan Ku A Rana! Sae ina ya’rlelen Yah AJ??” Cewar Aunty Salma.” Shaye da toka Rukaiyya ke fadin Fita zanyi zanje gidan wata friend dina .”
“Waye zai kaiki?”. Cewar hajja ga yayan naki baya jin ddi..” Tareda yah Nura zamu fita jin tace Nura AJ.ya zuba mata manyan idonsa daganin yanayin kallon tasan na tuhuma ne .”
Hajja Aunty sae na dawo anan tafice da sauri Lokaci daya ,AJ.ya bita da kallo Yana mmkin ina xasu fita da Nura Dan shi yasan karya tayi bata da wata kawa a Kano.”
“Dai dai kofar gidan su Asmy Nura ya faka motarsa .” yah kalli Rukaiyya da murmushi tom.kanwata Allah ya bada sa’a idan zaki fito ki kirani ta wya.” Zan shiga gida.
“Jiki sanyayye Rak ! Ta balle marfin motar kai tsaye ta nufi get din gidan su Asmy cikin takunta na kasaita ” bata sha wahalar shiga gidan ba..”bbu laipi Aranta take fadin suma Ashe suna da kudi ,Amma duk da haka ko kafar Mr.meera family basu takaba.”
Kai tsaye mai gadin gidan yyi mata iso xuwa shiga falon babban gidan sae da ya sadata da kofar sa’annan ya dawo bakin Aikinsa.” Masu aikine ke kai da kawo sae Wata Hamshakiyar macce matar manyan wadda ke zube dae daga cikin kujerun dake zagaye da Falon tana Amsa wya.”…
“Da sallama Rukaiyya ta shiga dae dae lokacin da mama ta gama Amsa wyar,ta Amsa sallamr tata.” Dauke da fara’a A fuskarta zubewa kasa Rukaiyya tayi tana kwasar gaisuwa.” Mama ta Amsa cike da fara’a sun zauna Jim na ya’n mintuna mama tayi karfin halin fadin Ya’mmata sae dae ban shaidaki ba daga ina??”
“Murmushi Rukaiyya tayi haka ne momy ni kawar Asma’uce cike da fara’a mama ke fadin Ayya yi hkuri bara akaiki wajenta” Amma kafin nan bara nasa akawo maki Abun motsa baki.”
“Murmushi Rukaiyya tayi da kin. barsa momy wlhi na koshi kedae kisha koda ruwane bara nasa akaiki dakin Asma’u din sae a biyoki da Abun motsa bakin daga baya.” Godia tayiwa mom.