WATA RANA Romantic hausa novels complete

“Da sauri ta kalli screen din wyar sae kuma ta cije lebenta na kasa’ xan dae aiko da driver ya daukeku mumin ina busy ,Husna kenake so kixo ki daukemu nabaki nan da minti Ashirin banason ,musu da haka ya datse kiran” haushi ya kamata tabi wyar da kallo ..kafafunta ta fara bugawa a kasa tamkar Wata baby gal” me mumin din nan ke nufi ??.taji xata je daukarsa amma shi daya xata dauka sae dae Aliya ta hau motar haya bazata shiga motarta taba.”da wannan tunanin ta nufi dakinta gamida kashe cooker ga’s din.
_”Fatan Alkhairi Asma’u Abdul Jabbar_..❤
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu.
©Haske Writer’s Association..
55
“A hnkali tayi parking motar ta A gurin na mussaman da aka tana da Dan parking din motoci Acikin air port, din.
Cikin takunta na kasaita ta fito daga motar.
Tana cikin shigar Doguwar rigar Arabian gown ,dark blue a gaban rigar a masa ,ado da stones work masu kya’kyalin gaske,sae Dan karamin veil baki da tayi rolling kanta dashi glass din frada ne manne a idonta.
Ta fito rike da wayr ta ,ta shiga Neman layin mumin haka ta cigaba da Neman layin batareda ya shiga ba .” juyawa tayi a hnkali ta fara tafia.”
“Acikin Air port din duk inda ta taka ka’fa sae anbita da ,kallo abunda ta tsana kenan.
” A hnkali taja tsuka cigaba da tafia tayi tana Neman layin mumin,
Jin tayi anyi hugging back nata.
A tsorace ta juya cikin wani irin salon ya riko waist dinta ya juyo daita tana fuskantar sa ,ya ka’ra manne ta a kirjinsa.
,har tana jin bugun zuciyarsa saurin kwa’tar kanta tayi gamida Dan ja da baya.
“Tana maida numfashi hnnun sa ya sa’ka gamida zare gilashin idanunta,suna hada ido ya kashe mata ido daya.
Sae taga ya ka’ra yi mata wani irin kyau,
Yana cikin farar shadda dinki (Hilton)” bbu hula akansa ,sumar nan tashi ta kwanta luff”as usually ,tamkar
Ta larabawa harde hannayenta tayi akan kirjinta ta Dan hararesa gamida ,hararar sa.
Baka tsoron matar ka tagan ka,nan take taga ynayinsa ya canja juyawa yyi yabi wata hanya ,da sassarfa tabi bayansa tana kiran sunan sa ,
Banza yyi mata gurin Aliya taga ya isa ya dauki ka’ramar trolley dinsa ganin hka itama Aliya ta mike jiki sanyayye itama ta dauki jakar kayanta.
,suna hada ido da Asmy tayi saurin dauke idonta.”
Tayi gaba abunta yyinda AJ .yake binta da ,mugun kallo Allah Allah yake su isa gida ,Dan sunyi wya da Aunty sadiya itama tana hnyar zuwa gdan.
“Tana tuki tana kallon yanayin sa gaba daya, yabi ya hade rae a hka suka isa gda.
Aliya ce farkon fita shima xae bude ,marfin motar tayi saurin riko hnnun sa,na dama nan tayi tozali da bandejin dake manne ,A hnnun sa.
Cike da tuhuma ta kallesa,Alamr tambaya kwa’nce akan fuskar ta ,cikin sanyin murya take fadin mumin wae meke faruwa ne??
” Rabuwar mu da Aliya yazo husna kiyimin Addu’a Allah yasa haka shiyafi Alkahiri ,bana son ta ka’ra awa daya a gdana.”
“Gabanta taji ya fadi me mumin ke nufi ? Badae ya ruguza masu plant ba.,baijira mai zata fadaba ya ba’lle marfin motar yyi gaba abunsa,yyin da security’s guard ,din suka kwashi kayan su suka nufi cikin gdan.”
,Da sassarfa ta cimmasa falo tasha gaban sa .”cike da tashin hnkali take fadin wae meke damunka??
“Tayi mganar gamida bude masa, manyan idonta ,mekikaji na fada maki. Shima yyi mganar a tsawace I don’t need her in my life any more…,saboda hka I want to divorce her.!.
” A fusace ya ra’ba ta gefenta ya nufi up stair’s.
Cike da tashin hnkali ta zube gwiwowin ta ,kasa.[Truncated by WhatsApp]
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu.
©Haske Writer’s Association.
56
Sae da ta murzawa ko’far bedroom din nata key sannan ta dauki wyar mamin ta,
Cike da tashin hnkali take fadin mami !! Ta fada cikin,rawar muryar ki kwantar da hnkalin ki Aliya na fada maki bazaki bar gdan AJ. ba kixuba eye’s naki ,kisha kallo an turawa kakarsa baka’r aljanah.”
Kwa’llar da ta taru a idonta ,tayi saurin gogewa da Dan yatsan ta,gamida sakin kya’taccen murmushi mami ,yaushe zaki kawomin ziyara?? Tayi mganar a shagwaban ce, zuwa jibi insha allahu .ajiar heart ta sauke anan tayiwa mamin nata sallama ,rage kayan jikinta tayi ta nufi bathroom.
*****
Gaba daya family member’s din nasa ana a babban falo ,dama idan ana wani muhimmin taro anan sukeyin sa ,mom tunda ta shigo falon taji zuciyarta ta tsinke ” cikin takun sa na kasaita ya shigo falon yana cikin shigar ka’nanun kaya ,
Farar T.shirt ce mai guntun hnnu ,da bakin wandon Jean’s ” fuskar nan tasa ko kadan bbu walwala ,itakam Hajja binsa kurum take da kallo Sallama yyi masu ga badaya suka amsa sa ,itakam Asmy gaba daya jikinta yyi sanyi.”
“Aunty sadiya ce ta bude taro da Addu’a cikin sanyin muryarsa AJ.ya fara kora bayani tun daga ranar da yaji Mom da Aliya na ko’karin zuba masa magani a Lipton,har kawowa ranar da yaji ya tsara plant akansu akan yasha ,da zuwan sa kano da Aurensa da Asma’u har plant din da suka hada dasu hajja dasu Aunty Sadiya Abu daya yasan ,ya boye contract marriage dinsa da Asmy.”
“Wandda wannan sirrin sane ,acewar sa.
” Cikin fushi ya fara mganar ganin likita da sukaje ,shida Aliya akan abunda yace akan ta ,Dan haka mom na baki nan da minti talatin ki kwashe komae naki kisan inda dare yyi maki ” Idan ba haka ba hukuma ce zata rabani dake, dukiar daddy an baki kason ki so ,bama bukatar ki acikin zuria’r mu ,sa’annan ya maida kallonsa kan Aliya wadda hawaye ya gama wanke mata ,fuska wani irin kishine ke cinta dama da kishiyarta take zaune bata sani ba.” Dama kishiyar ta ce ta wulakanta ta haka.”
“Aliya na sake ki !
Saki daya ,Allah ya haramta saki ,lokaci daya da wlhil azeem ukku zan baki ,amma kije I hate yhu Aliya ! I so much hate yhu!……saukar mari yaji akan kyakkyawar fuskarsa ,A tsorace ya daga manyan idanunsa yana kallon wadda ya masa, wannan aika aikar ,Ga mmkin sa grannyn sa yake gani tsaye a gabansa tana wani irin huci ” karo na farko a rayuwarsa da kakar tasa ,takai hnnun ta jikinsa,Da sauri Asmy taxo tasha gaban hajja “Sae taga hajja nayi mata wani mugun kallo wandda takasa ,fassara sa.”
“Cikin fushi take fadin muddin Aliya tabar gdan nan to na Rantse maka da Allah ka’fata ka’farta ,hka kuma bbu ni bbu kai har abada .” haba Abdul yaushe zakayi hnkali ne?” Kodan irin son da yarinyar nan take yimaka ,yaci ace kayi mata afuwa “A tsorace ya fara jada baya ,rike da fuskarsa hka hawaye ke tsiyayowa acikin ,kwayar idonsa Aunty sadiya tayi saurin kallon Hajja a tsorace.”
Cikin rawar murya ta fara mgana hajja meye haka?” Daga mata hnnu tayi sadiya bana son doguwar magana ,nariga nagama mgana in kuma kuna ganin ban isa daku ba bissimillah ga fili ga mai doki ,tana fadin hka taja hnnun Aliya sukabar falon ,A hnkali yaji duniar na juya masa wani irin tsoro ya dirar masa a zuciya ,wandda bai taba jinsa ba tsawon rayuwar sa ,A hnkali aunty sadiya ta fara tunkaro sa.”
Yyi saurin dakatar daita ,plzzxzz aunty sadiya karki nufoni “shin menayi wa hajja a rayuwa ,da zatayi min wannan hukuncin ??” Ya fada yana ya’rfe hnnunsa ,da gudu Asmy taxo ta rungumesa ga gam” ga mmkin ta Sae taga ya turata da karfi baya -baya tayi zata fadi da Sauri Aunty sadiya tayi saurin tarota a tsorace,
“Da gudu yabar falon hawayen Idonta suka kasa tsayawa ,aunty plzzz ki tsaida sa kar yaje yyi ma.