WATA RANA Romantic hausa novels complete

“Ina har Abada!! na dai yie xaman hkuri ni na tabbata (WATA RANA !) Zuciyata xata samu wadda take so ina mafarkin hkan mom wadda Sae kinyi Alfahari daita nina fada maki mom ….
A xuciya Aliya ta mike wani irin bakin ciki ya ziyarci zuciyar ta ,haka hawaye suka dinga malala akan fuskar ta haka ta dinga ciccika tana karawa ” idan Akwae abunda Aliya tafi tsana a dunia shine….AJ. Ya rabi wata macce da ayi mata kishiya gara kowa ya mutu wlhi a xuciya tabar dakin da gudu tana goge hawayen idonta.
Jikin mom qlau yyi sanyi ta maida hnkalin ta kan AJ.wanda yabi bayan Aliya da mugun kallo gami da yin Dan karamin tsaki…
My son!
Rinan nun idonsa ya dago yana kallon ta bacin rae ne tsantsa acikin su ka dinga hkuri da Aliya Dan Allah har ynxu yarinya ce ,baece komae ba ya bar dakin baijima ba sai gaya tareda salame..
Anan yyi mata umurnin ta ta taimakawa mom din tasa taci Abinci ya kalli mom ,ni xan wuce office plzzz idan da matsala ki kirani mom ya fada yana kallon ta .”
Murmushi tayi masa tana yimasa Allah ya kiyaye daga hka ya fice daga dakin ….
“A office ma kasa zama yyi Sae waya kan waya yake yi akan ya jikin mom din nasa yna cikin wannan yanayin kiran Angel nasa ya shigo ” A sanyaye ya daga wyar ..
Cikin kasalalliyar murya yake fadin ..
“Angel!
Yayana baka nema na ko??
Takarasa mganar A shagwaban ce bbu alamar ma kayi missing dina ni kawae ke haukata !
Nop!
Angel waye ya fada maki?”
Nayi kewar ki sosae Anan suka cigaba da hirar su..
Bayan dawowar sa office gaba dae gurin mom din nasa ya tare shike jinya duk da ta samu sauqi haka ma hajja taxo ta dubata ,Aliya kuma tun safe bata kara leko mom ba.
Sae kusan karfe goma AJ.ya dawo gidan sa koda ya dawo bai nemi Aliya ba Dan har lokacin fushi yake yi daita…jin yayie xuwa wannan lokacin tamkar ya fasa tafiyar daita.
Dan an riga an yanki ticket ne kurum.” Haka kuma an gama komae , kwanciyar sa yyi batare da ya leka part dinta ba.
Itama bangaren Aliya fushi ta hauyi dashi….
(Washe gari……..)
WATA RANA !
N@ Asmy b Aliyu.
©Haske Writer’s Association..
11
Karfe 8:00@m na safe ya tura kofar dakin nata wanda tsaye take ajikin mirror dressing tana shirya kanta karar bude kofar da taji shi ya dawo da hnkalin ta jikin kofar ido biyu sukayi dashi yana cikin manyan kaya na captani ruwan kasa haka ya kafa hula kalan kayan ,ba karamin kyau yyi ba.
Saurin dauke kanta tayi akansa bata reda ta kara kallon inda yake ba.” Ki shirya da wuri jirgin karfe 9;00am. Xamu bi bai jira mai xata fada ba yyi ficewaer sa xuwa estate din grannyn sa.
“Sallama yyi a babban falon karar T.V. yaji bbu kowa a falon sae tashar sunan t.v. dake aiki kai tsaye bedroom dinta ya nufa nan ma bata nan mmki ya cikasa to ina ta shiga ne??
Karar bude kofa yaji da sauri ya maida hnkalin sa jikin kofa granny ce murmushi tama sa harka shirya kenan?”
“Ajiyar heart ya sauke oh my world!
Daga ina hka granny ” ina kiching muna ta kokarin hada Karin kumallo nida laraba.
Meya faru kuma?
Yana shagwabe fuska to ba keki ka tsorata ni ba!
Gyara xaman gilashin idonta tayi wanda ke karama idon nata lafia oya muje kayi break fast nasan shiya kawo ka ban San yaushe wannan matar taka xata canja ba anan kuma granny ta shiga banbamin fada shidae biye daita yake kurum.
Allah ya kawo maka wata matar kirkin wadda xata cikamin gida da ya’yanka!
” murmushi mai kyau yyi amin my sweetheart mekika tana darmin ne?”
Yyi mganar gamida xaunawa akan kujerar denning table ,koko ne da kosae!
“Ya tsine fuska yyi kai gaskiya ni baxan ci ba ya fada gamida harde hannayen sa akan kirjinsa ya wani bata rae.
” A mallan gari da yawa !
Kuma da kake xuciya akan baxaka Ciba.” Yau shi nake sha’awar ci ga ruwan lipton nan kasha sae ka hada da wainar kwae.
Suna break fast yana mita granny dae sae shan kokon ta take tana gamawa da kosae ..
8:30@m.
Yama granny sallama akan idan sun isa xaikira ta anan ta masa fatar Allah ya kiyaye ,hka ma mom yau bbu laipi taji sauqi tare suka shiga da Aliya ta hade cikin wata doguwar rigar material marron sae Dan yololon mayafi da ta aza wanda dashi da bbu duka daya.”
Sae wasu uban hill dake a kafarta kalar handbag ” nata bbu laipi tayi kyau ,nan tayiwa mom ya jiki anan AJ.ya kara jaddama ya’n aiki akan su kula da mom nasa da kuma granny dinsa.”
Idan akwae matsala su neme sa da hka yayiwa mom sallama drivern sa ya jasu xuwa air port da sauran tawagar body guard nasa.
“A mota sai kiran sageer yake baya shiga ,har lokacin da jirgin su ya daga xuwa kano .”
**********
Sosae Aunty salma tayi farin ciki dasu sae nan nan take dasu itakam Aliya duk a takure take ,Suna xaune gaba dae a Falon na aunty salma wanda baifi awa daya ba jirgin su Angel nasa ya sauka.
Wae aunty ina Nana ne?
Murmushi Aunty salma tayi ,tadan harare sa a wasan ce sae yanxu kasan daita sowiee aunty na sha’afa ne aikin San ya’r gidana ce.
Tana gidan kanwar Abban su kwanan ta biyu yau acan saleem kuma yana Abuja. Kasan mahaifin nasu da tsastauran ra’ayi akan boko mussaman A boarding skull.”
Hka yana da kyau Aunty uncle jafar yyi tunani mai kyau.
Uffan dae Aliya bata cema su ba sae hirar su sukeyi a tsakanin su ana saura minti talatin jirgin su ya sauka gabadai suka nufi air port din.
“A wannan lokacin AJ.sae duba agogon hannun sa yake ,ya kagara yaga ya’r tilon kanwar tasa rabonsa daita shekara daya kenan har karfe biyu dai dai na rana ya buge bbu alamr saukar jirgin su abun da ya saka AJ.cikin matsanaciyar damuwa da wasi-wasi kenan 2:10pm…jirgin su ya sauka.
Murna kamar meye a wajen AJ. Gaba dae ya rasa na tsuwar sa burinsa kawae yyi tozali da ya’r kanwar sa Aliya na lura dashi sae dae ta kallesa ta tabe baki gamida dauke kae.”
“Matashiyar budurwar ce ke saukowa daga matattakalar jirgin ” A tamfar sharaton ce ajikin ta kalar xubin brown da ratsin light pink ajikin ta dinki Riga da zani ne xanin single sae rigar wadda ta iso har gwiwarta an yimata dinki da wasu irin stones work.” Wanda ba karamin dacewa sukayi da Zubin atamfar ba.
“Medical glass ne A idonta haka din kyakkyawa ce ajin farko tana da manyan idanu masu ,daukar hnkali kallo daya xakayi mata kaga tsantsar kamar da sukeyi da AJ. Ta koina kanwar tasa shi ta debo.”
Sae Dan karamin veil brown wanda ta sakalo sa tun daga bisa kai ta sakalo sa a wuyan ta babbar trolley ce take jaye daita …
Matashiyar budurwa .mai kimanin shekara goma sha Takwas A dunia.” Masu karatu ba kowa bace wannan illah (LAILAH SAMEER MEERA”))..
Tafia kurum take taga inda xata hango ya’n gidan su nan take yanayin fuskar ta ya sauya tamkar tayi kuka wato ma .Yah Abdul din baixo ba. Bbu granny bbu mom bbu Aunty’s dinta.
Tunanin ta ya katse dai dai lokacin da taji saukar hnnunsa akan Fuskar ta.” Hka taji kamshin jikinsa wanda tasan wannan tabbas yayan tane.
Ihun murna tayi ya janye hnnunsa akan fuskar ta tayi arfa dashi ihu tasa keyi A karo na biyu tayie hugging dinsa sosae tamkar xata koma ajikin sa.
Wayyo ddi yayana!
“Ashe xaka xo?
Oh my Allah ! Gaskiyya” Am very very happy kasan cewar ka anan.
“Murmushi dauke A fuskarta ta subbaci goshin sa ,tareda fadin ” by d way I miss yhu yayana!
Murmushi ya sakar mata ,tareda fadin by d way I love yhu my “Angel muryar Aunty salma ce ta daki dodon kunnen ta sae lokacin ta kula daita tsabar murnar ganin yayanki kin manta dani oh sorry my Aunt nan tayi hugging dinta tana murna ,Anan ta maida hnkalin ta kan Aliya wadda bata Santa ba gaba dae dan bbu wanda ya fada mata Yayan nata yyi aure.”