YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 11 to 20

 Ganin ta kasa d’auke idanu akansa yasashi yi mata wani irin kallon wanda yasa kirjinta bugawa da karfi, sannan ya d’auke kansa dan shi duniya babu wanda yake jin yana matukar so kmr ita,amman ji da kanta gadara takama da kudin mahaifinta tare da wulakacin abinda tayi malik yasa yake jin kaunarta na neman riked’ewa ,a lokacin ji yake kmr ya tashi ya bar gurin sai dai kafin yayi hk sai ya wulakantata, sun jima tare da yin shiru kowanensu zuciyarsa na saka da warwara, fuad yaji shirun yayi yawa har sanda maikacin gurin ya ajiye tire me d’auke da cups guda biyu ya juya siririn tsaki yaja batare daya kalleta ba ” yana da kyau kiyi abinda ya kawoki domin duk lokutana atsare suke babu wata dakika da take a wajena dazata zo face tana cikin tsari don haka kiyi gaggawa sannan ki takaita wajen maganarki dan banason mutun mai surutu ko dogon magana dan hk ina sauraranki .

Me’ad tayi mugun tsaresa da idanunta tare da gyara zamanta tana saukar da numfashi” hakika so wani shu’umin abu ne wanda yake sarrafa duk wanda ya shigesa ,fu’ad da fari dai sunana me’ad kmr yadda na sanar maka a ranar farko da muka had’u muna zaune agarin nan tare da mahaifana ,ba sai na tsaya gaya maka waye mahaifina ba, kana ganinmu kasan muna da milloyoyin Kudi da bazasu lisafu ba sannan….”dakata dan Allah malama kafin ki cigaba da wad’an banzayen kalaman naki “jikeke ke wata jaruma ce ko me dakike zubo dogon bayanai hakan kmr agidan radio ? 

kanta ta girgiza tare da cewa “aa. 

“ok Kamata yayi ki yi magana me ma’ana da takaitawa kmr yadda na fad’a miki tun farko, 

“Ko kin d’auka da hkn da kika soma zaki birgeni ne ? 

“dan kin wani zo kina zancen dukiya, kin d’auka soyayya ce a ganin farko bari kiji ba wata soyayya irin haka kin siyo furi kin kawowa saurayi abu ko tsari babu sannan saurayin dasani minti kwanaki kalilan kika yi masa, ki kashe kudinki a wasu abu na kirki wata killa zaki iya samun lada.. 

Me’ad batayi musu ba tabishi da shu’umin kallo wanda ke bugar masa da zuciya sannan tayi wani irin murmushi duk abinda take bukatar nmj dashi, fu’ad ya tattara, aji kyau kamewa tare da sanin Ciwon kai shima ya juya ya kalleta wani irin shaukin sonta na dibarsa.

” a zahirin gsky maganar dakayi tasa ilahirin jikina yayi sanyi …

” go straight to your point dan Allah malam.. tsura masa ido tayi gbdy ya d’aureta duk ta inda tayi tunaninsa ya zarta hkn cikin sanyi murya tace “.tun ranar farko dana d’aura idanuna akanka naji kamin, na dad’e ina tunani kmr bamu dace ba amman zaune da nake agabanka na tabbatar da babu nmj daya dace dani kmrka ,ka cancanta kazamo uban ya’yana shiyasa zanyi kok’arin domin naga na fayyace maka na kamo da matsanancin sonka, duk da nasan kaima hk ne dan na cika budurwar da dole nmj ya kalleni ya soni ,ba dan komai kodan kyawuna kudina da kuma tarin ilimi na, da iya kalamai duk da nasan a yanzu hk ka gama amincewa, amman zanso ka furta kanasona kmr yadda na furta maka, sannan ga sakon zuciyata danazo maka dashi takarasa mgnr cikin murya me sanyi ta mika masa wata karamar akwati , amman sam yaki amsa illa idanunsa daya tsura mata”ka amsa dan Allah ni fa sonka nake tsakani da Allah kuma a shirye nake dana aureka.. zan iya sadaukar da komai nawa akanka ciki kuwa har da rayuwata.

Fu’ad yaji gbdy dry ta kufce

Masa yayita dry abinda bai taba yi ba kenan dryr data bayyana hakorarnsa “ni kike so…?

” yes ofcourse dole nasan zakayi mamakin kamata na furta ina sonka, amman kayi la’akari da so ba karya bane ,kuma kagaggen abu ne tunda kan Annabi adamu (a.s) kaga kuwa babu mamaki dan nace ina sonka. 

“Tabbas kin burgeni dan naga ala’mun kema jaruma ce da har kika iya kallon wad’an idanuwana kikace wai kina sona duk da kinsa ko acikin mafarki baxakiyi tunanin ni fu’ad zan amince da uzirinki ba, yayi shiru tare mikewa a fusace yasoma kok’arin barin gurin batare da ya amshi abinda ta miko masa ba da sauri tabiyo bayansa tana share gumin daya jikata mata fuska “ka tsaya dan Allah ko coffee din fa baka sha ba , tafiya yake tana biye dashi tare da kokarin son magana ” yayi saurin daga mata hannu “karki dameni da banzayen kalamanki, I thought tun farko nace banso mgn dayawa ko? “Ummmm amman Dan girman allah ka tsaya ka saurareni bakasan yadda nake jin zuciyata .

” yi min shiru tare da d’auketa da wasu maruka har guda uku ajere sannan yace “wawiya kawai kinyi zaton a banza zaki samu soyayyarta ko? Har da zuwa da shukun fure da akwatin zoben masoya, kina zaton zan amince da soyayarki ne saboda kina da kudi, iyayenki ma hk kisani wannan talakan daban yake da sauran talakoki koda nake talaka ina tabbar miki wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa dan kije ki samu daidai dake mai kudi da duk abinda kike takama dashi .

“fu’ad ka mareni a bayyanar jama’a dan nace ina sonka? 

“yes na mareki ko zaki rama ne? 

girgiza masa kai tayi kawsi ala’mun a’a, “ok na d’auka tak’amarki zai sai ki rama dakikiya kawai yana gama karasa wannan mgnr ya juya kai tsaye bakin titi yaje yana tsaida me adaidaita “kai zaka capitol road? 

ta biyosa da sauri “kabari na rage maka hanya nima hanyar zanbi “kai me adaidai wuce abunka tare muke dashi batare da bata lokaci ba me adaidaita ya wuce ya sake saida wani nan ma ta hana tare da fito da id card din acp aliyu ta nuna masa kana kuskuren d’aukarsa sai dai ka iske kanka amagark’ama nan take ya wuce yana cewa “kan wani dalili aiko bazam jawowa kaina ba.

 tafiya fu’ad yke tana binshi a baya tana rokonsa yazo ta rage masa hanya amman yaki saurarata har sukayi nisa da inda tayi parking din motarta 

tsaida me okada yayi kawai kafin tasoma dogon bayaninta tuni me okada ya wuce hk jiki a sanyaye ta koma tashiga motarta cikin tsananin damuwa da bakin cikin abinda fuad yayi mata ta figa motar aguje ta nufi estate dinsu kai tsaye tana wani irin mahaukacin gudu Wanda zai kayi mamaki matuka in idan akace macece take tuka wannan motar ta miliyoyin kudi ,wani irin sautin kidan soyaya ne ke tashi acikin motar tamkar zai tarwatsa motar. 

Yayinda samarin dake zaune a layi masu ji da kansu kuma yayan masu kudi irinta sai binta suke da wani irin kallo cikin bakinciki domin duk isarka duk iyawarka da iya wankanka baka isa tayi ma koda kallon arziki bane ballanatana kasanyawa ranka zata saurareka, hk ta ratsa har ta iso makeken gate din daya lullube ilahirin gidan hon daya ,tayi duka mutun ukun dake kula da get din suka taso suna kokarin bud’e mata get tare da jero mata sannu da zuwa amman babu wanda ya isheta kallo balle har ta amsa gabadaya idanunta a rufe suke .

bayan tayi parking a inda aka tanada domin ajiye motocin ta fito jikinta a sabule still zuciyarta na mamaki tareda alajabin abinda fu’ad yayi mata wanda ko a mafarki bata taba expecting wani bil adama zaiyi mata ba da wannan tunani ta taka zuwa parlour mahaifiyarta, inda ta cusa kai tare da yin sallama aciki .

Momy ta d’ago tana dubanta kallo daya tayi mata tasan tana cikin damuwa amman sai ta ajiye hkn akan aikin data fara ne, yasanya yanayinta ya sauya cikin sakin fuska momy tace ” duk gajiyar hk?

Naunayen ajiyar zuciya ta sauke batare datace komai ba illa kwanciya datayi akan kujera tace “.ganin nan dai momy kwata kwata bansa abinda ke damuna ba “allah ya kyauta momy tace kawai tare yin shiru kana ta sauke ajiyar zuciya momy tayi “ni kuwa me’ad ina son nayi wata tambaya . ” kai momy zaki fara ko, kwana biyu kin barni nayi kiba amman yanzu zaki soma yi min zance safwan abinda kika san banason jin a halin yanzu….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button