YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 11 to 20

Momy ta maso kusa daita tare da dafata “haba me’ad yanzu arayuwa babu wanda baya son cigaba ,idan kika aure safwan zaki samu cigaba arayuwarki da wata daraja ta Musamman..

“Kai momy meyasa zaki dinga yin irin wanna bayanan , ada kinsa duk duniya babu mutumin Dana fi muradin kasance dashi kmr sa, amman yanzu an wayi gari bana bukatar hk, momy kudi fa da kike ganinsu a yanzu nasan basa siyan kima daraja mutunci kwarjini soyayya ,dan hk momy ki daina irin wanna tunanin kiyi fatan na auri wanda zai bani farinciki ina son fuad …..

Duk da nasan takala ne tulis……kuma zan auresa duk da talau…

Subuhallahi karki sake ki karasa wannan kalmar domin fiyayen halita ma yanemi tsari da ita dole ina son kiyi aure wanda duniya take damawa dashi wanda shi da mahaifinsa, suka maza masu abin hannunsu kuma bazan so ki auri Wanda bai kai ubanki kudi ba, sai wanda yafi shi dan haka a kullun adduar da nake miki kenan, ki janye batun yaron nan tun mahaifinki bai ji ba, idan dad dinki zai amince da aurenki dashi ni meye nawa aciki ?duk yadda nake son kiji dadi a gidan safwan hk zan hakura amman da zaki yarda ki amince kwarya tabi kwarya atsakaninku dana ji dadi sannan ki shiry tarban safwan yana kan hanyar dawowa .

Me’ad ta ta’be baki aranta tana jin zata iya yaki da kowa akan fu’ad , ahankali ta mike ta nufi bangarenta inda ta iske ummi tana faman goge goge tayis din dake barandar .

Ummi tana ganinta ta mike da sauri tana cewa “aunty sannu da zuwa, tsaki me’ad taja a maimakon ta amsa mata tayi shigewarta ummi tacigaba da abinda take yi aranta tana mamaki yanda me’ad ta d’auki duniya da zafi hk, duk da tun kafin tazo duniya anyi wad’an da suka fita wulakanta mutane amman babu wanda aka taba nunawa aka ce yayi nasara, balle itama tasanya ran wata rana zatayi nasara wannan girman kan nata ta sake ajiye numfashi tacigaba da aikinta.  

mmn sudais ce

????????????????????????

       ‘YAN CINKI

      ????????????????

????????????????????????

             ~NA~

 *AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

      MRS ADAM

( YAR MUTAN KAGARA)

Page 51 to 52

…….kwance take akan makeken gadonta kiran italy tana kallon saman d’akinta ,sosai tayi zurfi cikin tunanin lamarinta da fu’ad tare da neman mafutar yadda zatayi, ahankali ta mike zaune ta koma gefen gadonta ta zauna tare da lullu’be kanta da hannuwanta duka sakamakon bugawar da zuciyarta keyi akansa ,tamabayoyi tashiga jerewa kanta d’aya byn d’aya “me yasa fu’ad yaki amincewa da tarin soyayyata garesa?”me yasa ya mareni akan nace ina sonshi? “Kodai Malik ya gaya masa abinda ya faru ne da hkn yazamo silar d’aukar fansa gareni ta hanyar disgani cikin bayanar nasi…”ga shan mari har uku ga rashin amincewa da soyayyata da bai yi ba… “yanzu ya zanyi da rayuwata ? Ta sake jehowa kanta tmby. 

” ina bukatar fu’ad arayuwata kuma zanyi komai akansa domin naga na mallakesa. wani abu ne data samu yazo wa zuciyata shine sake jin fu’ad datayi ajikinta yana yawo cikin jinin jikinta, tayi saurin goge hawayen da suka cicciko a kwarnin idanunta ya kawowa kuncinta ziyara, tasa hannunta ta dango d’igan hawayen tana kallo “yau itace ke kuka akan nmj?”nmj ma d’an talakawa wanda ba kowa bane…mikewa tayi ta isa gaban dress mirror dinta ta tsaya tana karewa kanta kallo daga samanta har k’asa “meye tarasa ajikinta kyau ne ko me da har fu’ad yake mata kallon ita bakowa bace? 

Ahankali take karewa cikar halitar da Allah yayi mata, tayi imani ko ita ta isa tasa fu’ad ya fuskanci lamarinta yasota fiyye da yadda take masa, sai alokacin ta lura da irin yadda gashin kanta data d’aure duk ya wargaje a saman kafad’unta adalilin tunaninsa ,hannuta ta kai kan wayarta tasoma neman layinsa, Amman yaki d’auka, kasa hakuri tayi tacigaba da kiransa har sai data yi masa kira yafi sau goma bai d’auka ba sannan ta nemi layin malik kira daya biyu malik ya d’auka, bayan sun gaisa tace “malik kuna tare da fu’ad ne ka had’ani dashi?

” a,a ina gurin kallon ball, na dai barshi tare dasu kabeer a gida.

“Okay idan bazaka damu ba zanyi maka wasu ‘yan tambayoyi, amman ina bukatar jin gsky daga bakinka .”uhmmm ina sauraranki?

“Ka ta’ba gayawa fu’ad abubuwa da suka dinga faruwa atsakaninmu da kai har zuwa kan marin danayi maka?

sai daya ja naunayen ajiyar zuciya ya sauke da kyar sannan yace”alahakikanin gsky wasu Abubuwan yasani sai dai batu na mari bai sani ba, dan ban gaya masa ba, wani abu ne ya faru da har kikayi tmby?

“Nothing ,Amman yanzu wani irin taimako zaka min malik akan abokinka?”na maseefar kwadaituwa da aurensa, ina son shi sosai kuma zan iya yin komai akansa matsawar zan sameshi, ka taimakawa rayuwata malik nasamu fu’ad, nayi maka alk’awarin zan maka komai ciki kuwa har da samammaka aiki a karkashin ikona tunda shi yaki amsa daga gareni ..?

Numfashi da ajiyar zuciya ya sauke atare kana yace “zaki iya mallakar zuciyar fu’ad cikin sauki dashi kansa gbdy, bisa dalilin abu daya da sauri ta katse Shi ta hanyar cewa”meye shi malik ka fad’a meye shi zan iya yin komai akansa “meye zanyi fu’ad yasoni?

“Bawani abu bane daya wuce kyautatawa, fu’ad na matukar son kyautatawa ,da km kyautatawa wanda ya cancanta most especial mara shi,ina tabbatar miki matukar kika kasance daya daga cikin masu kula da kyautatawa zaki mallaki zuciyar fu’ad cikin sauki batare wata matsala ba, ni kaina ina miki sha,awar aurensa domin idan kika sameshi amatsayin miji ina me tabbatar miki zaki yi alfahari samun miji kmrsa “shikenan malik nagode sosai da shawararka, km InshaAllahu zanyi kok’arin naga na kasance cikin masu kyatatawa mutane, gobe karka manta kasameni a oil and gas. 

” InshaAllahu bazan manta ba Na gode sosai Allah ya mallaka miki zuciyar fu’ad “ameen nima nagode da wannan adduar taka sai mun had’u goben ta katse kiran ta koma gadonta ta zauna inda zuciyarta take bata umarnin me zai hana ta tura masa ko da sakon text message ne tunda yaki d’aukar wayarta hannuwanta duka tasa ta rike wayar tasoma rubutu sako kmr hk.

_Assalamu alaikum ina fatan kana cikin koshin lfy, daman na turo maka wannan sakon ne domin na k’ara baka hakuri bisa ga kalamaina na d’azu danayi amfani dashi ,wanda sukayi silar ‘bacin ranka har ka mari kyakyawar fuskar matarka, azahirin gsky naji babu dadin abinda kayi min ,sai dai tarin soyayyar danake maka ta hana rashin jin dadin nawa tasiri ,ina sonka fu’ad har bansan yadda zan misalta maka ba, ka daure ko ba yawa nima kasoni kwatankwacin yadda nake sonka I really sorry for what I did ..sai da safe daga mai sonka Me’ad Ediris Takai_

Tana tura masa ta koma kan ganta, ta kwanta lamo tare da runtse idanunta bawai dan tana jin bacci ba, sai Dan shaukinsa dake dibarta ,gudundune jikinta tayi, lokacin da tunaninsa ya yawaita ajikinta dan har ta fara hango sunyi aure dashi da yadda yake sarrafata akan bed gurin aika mata da zafafan romancing dinsa masu birkita ‘kwal’kwaluwa.

A kwancen dayake a d’akinsu sanye cikin jallabiya fara sol hannunsa rike da wayarsa yana brownsin sakonta yashigo ,amman bai bi ta kai ba yacigaba da abinda yake, km ko bayan daya gama bai duba ba yayi kwanciyarsa, ranar dai me’ad bata samu ta runtsa ba duk inda ta juya fu’ad take ganin da hannunsa dake yawo a ilahirin jikinta . 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button