YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 11 to 20

Washegari tun 7:00 malik ya tashi yayi shirinsa ya iso oil and gas, sai dai bai iske me’ad ba dan bata karaso ba tukun, yasamu guri ya zauna zaman jiranta, sai gurin takwas tashigo cikin hadaddiyar motarta kiran toyota Camry ta gabansa ta wuce amman bai ganta ba saboda ba’a cikin irin motocin daya saba ganinta ciki bane, bayan ta isa office dinta da kmr minti 2 tasa ayi kiransa,cikin wasu ‘yan mintuna malik ya bayyana a office dinta cike da girmama ya gaisheta, ta amsa da kulawa sannan ta nuna masa gurin zama da hannunta kana ta bukaci takardunsa ,batare da ‘bata lokaci ba ya mika mata, bayan ta duba ta mike tsaye “kabani minti 20 “ok badamuwa ranki ya dade. Kai tsaye office manager ta nufa domin neman alfarma. 

Acikin awa daya kacal malik yasamu aiki a ibadan karkashin kulawar me’ad amtsayin wanda zai dinga kula da ficen da shigen kud’ad’en kasancewar accounting ya karanta

 Lokacin da wannan labarin yasameshi a zaunen dayake a office dinta, yayi matukar murna da farinciki, godiya ya dinga yi mata kmr zai mata sujada, aikin daya d’auki sama da shekaru biyar yana nema sai gashi yasamu acikin awa daya nigeria kenan kayi karatun kagama sai kana da hanyar zaka samu aikiyi..

“Kabar min godiya hk nan ,ka godewa Allah daya nufeka dasamu, sai dai shawarar da zan baka ,ba wuce ka rike aikinka da mahimmanci ba ,domin mutane dayawa irinka na can suna nema kasa danaka basu samu ba , sai abu nagaba ka taimaka min nasamu fu’ad…..

“Angama ranki ya dad’e InshaAllahu zanyi iyakacin kok’arina akan lamari, “ok ranar Monday zaka soma aikinka yanzu zakayi dropping account number dinka, akwai wasu kudin daza’a tura maka domin siyan sutura.

 “Nagode nagode!!! ranki dad’e wallahi har bansan irin godiyar da zan miki ba ,hk suka rabu malik na farinciki samun aiki ita km tana murnar zata samu fu’ad cikin sauki tasan idan yaji itace tasammansa aiki zaiyi farinciki wata killa adalilin hk burinta ya cika. 

Koda malik ya jewa fu’ad da labarin samun aikinsa ta hanyar me’ad, yace “tayi kokari sosai, sai dai kajira ranar zuwan wulakanci daga gareta, domin wannan aikin daka amsa daga hannunta daidai yake da ka amsarwa kanka wulakanci ne da damuwa, ni dai babu ruwa duk abinda yaje ya dawo sai dai ya kare akanka. 

“Wace irin magana ce hk fu’ad?

” gskyar lamarin nagaya maka sai kayi taka tsantsan “Naji ni dai ka min addu’a shi nafi bukata daga gareka bawani dogon sharhi ba ,sai agame da zance me’ad , yarinyar nan ta damu da lamarinka dayawa , ka duba kagani kyau ilimi nasaba duk tana da, uwa uba gata da zuciyar taimako “ai ta taimaka maka dole ka fad’I hk mana , ni dai ina umartarka ka takaita maganarta anan dan kadameni da zance ina da abubuwan yi.

Malik yayi dry sannan yace “ni da zakabi shawarata da ka amince ka aureta komai cikin sauki zaka samu aikin ma dake bulayin nema ba sai kaje ba, kana daga kwance za’a yi maka komai.”to baza’a d’auki shawarar taka ba ,idan ka damu da lamarinta har hk ka aureta mana ,ai daman kana sonta. 

“Ina sonta bata sona kai take so, da kace ni ta nuna tana sona wallahi ina tabbatar maka babu abinda zai hanani aurenta,”yanzu ma zaka iya gwada sa’arka yana karasa fad’ar hk ya wuce ya bar malik tsaye yana kallon bayansa. 

 

*********

Duk abinda me’ad zatayi domin shawo kan fu’ad tayi, tabi abokansa da duk wani wanda tasan suna muamula, duk inda tasan zata ganshi kafafunta na gurin amman ko kallo arziki bata isheshi ba ,asalima yana ganinta zai bar gurin yakama gabansa, acikin tsakankanin wannan lokacin ne labarin rashin lfyrsa ta risketa, bata tsaya sanya a gwiwa ba ta nemi malik da yayi mata rakiya, shine yayi mata jagora har gidansu inda ta tsaya kallon ruba’b’ben gidan dake shirin zubowa “kace na ne gidansu malik?

“Kwarai kuwa nan ne gidansu “kina mamaki ne?

Shiru tayi batare datace masa komai ba illa tsurawa gidan idanu datayi “yanzu anan fu’ad dinta ke rayuwa tun tasowarsa? A she fili tayi zance batasani ba ,

“Ki daina mamaki ranki ya dad’e nan ne gidansu kuma inda yayi rayuwa acikinsa idan kin mutsu ne mushiga Kigani d’aki na d’aya na biyu nan ne d’akin kakarsa.

Tana gama sauraransa ta juya ahankali Jikinta matukar a sanyaye tashiga cikin parlour gidan me cike da duhun tsiya ,hannunta rike da karamar jakarta da kyar take ganin inda take sanya kafafunta duk rana ce ba dare ba ,yayinda malik ke biye daita da manya manya fararen lododi guda biyu ,taja ta tsaya abakin kofar shi km malik yayi sallama tare da kutsa kanshi cikin d’akin sannan itama tayi sallama tashiga “a’a Malik kai ne hk da rana tsaka ?”to marhabun lale ku karaso ciki mana inna ta fad’i hk tana mai mikewa ta shimfid’awa me’ad dadduma ,Dan shi Malik tuni ya ajiye lododin hannunsa yakarasa inda fu’ad yake.

Duk wanda yasan d’aki marasa shi hk d’akin yake bawani shararrun kaya ne acikinsa ba illa wani D’an madaidaicin gadon, sai kayan miyar dake ajiye gefe guda mai nuna alamun na siyarwa ne, gefe daya km wata katuwar akwati ce ajiye kallo daya tayi wa d’akin tasan d’akin marasa shi ne kmr yadda gidan yake sai da ga dukkanin Alamu yana samun kulawa ta hanyar gyara da tsaftaceceshi . 

 cikin ladabi tamkar ba ita ba, ta durkusa har kasa kanta a sunkuye cikin sanyi murya”inna barkanmu da warhk ya gida da me jiki.. inna ta amsa cikin sakin fuska da kulawa batare datayi tunanin inda tasanta ba saboda ganinta tare da Malik .

 ahankali me’ad ta juya inda fu’ad ke zaune Wanda ke aikawa malik da uwar harara sanye cikin gajeren wando da T shirt fara sol gashin jikinsa kwance luf Luf tmkr na jarirai ,ta gaida uban gayyan da ko kallon inda take bai yi ba ” ina yini ya jikin ? abunda me’ad ta fad’a Kenan taja bakinta tayi shiru. 

ya d’an d’ago kad’an yace lfy atakaice shima dan inna tayi masa ala’mun da kafarta ne ,me’ad ta sake yin wani kayataccen murmushi sannan tayi shr.

Malik yayi gyaran murya sannan yace “inna ga surakarki budurwar fu’ad tazo duba lfyrsa ..inna tayi dry “kace kishiya ce shine har da bata gurin zama ,shi kuma jairin sai wani cika yake yana batsewa kmr ba yanzu nagama fama dashi gurin shan magani. Me’ad ta sunkuyar da kanta alamun kunya .malik yace ” har yanzu fu’ad bai bar gudun magani? ” ina fa har tsoron rashin lafiyarsa nake saboda hkn.

Mead ta dago da niyyar ta saci kallonsa ,karaf suka had’a idanu atake kirjinsu ya buga, tayi saurin d’auke idanunta Dan bazata iya cigaba da kallon surar jikinsa inna na gurin, sai dai muryarta a sanyaye tace “inna me yasa aka barshi a gida ba’a kai shi hospital ?

“Wannan za’a kai hospital inna ta nuna fu’ad daya yatsina fuska alamun damuwa inna tacigaba “mutumin dake gudun magani balle allura idan kika ganshi kuzarin jiki kawai garesa amman laulauyi garesa sai ki kishirya, murmushin jin dadi mead tayi ganin tasamu karbuwa agurin inna .

sun jima shr sannan inna ta mike tayi waje ,shima malik yace “bari nabawa masoya guri, tsaki fu’ad yayi batare daya tanka masa ba .

Yana fita fu’ad ya gyara zamansa cikin rashin jin dadi fitar da inna da Malik sukayi dan ba’a son ransa ba, dan babu yadda zaiyi ne.

 me’ad ta matso zuwa inda yake ta tsuguna tare da cewa “fu’ad…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button