YANCIN KI Page 11 to 20

Sam bai kalli inda take ba hasalima cigaba da danna wayarsa dake rike a hannunsa yayi, tayi kusan minti uku sannan tayi kokari kai hannunta da zumar Kwace wayar hannunsa ya kallota a fusace tana dakatar daita da manya idanunsa domin bayason kusancinsu a yadda yake Dan shi kadai yasan abinda tafiya acikin jikinsa tsawon minti 2 yana tsare daita da manya idanunsa kafin daga baya yasoma mgn kasa kasa “karki wahalar da kanki da wata banzar kalmarki ko gaya min uzirin abinda ya kawoki,domin ina tabbatar miki sam banyi murna ganinki kusa da innata ba ,ni a bangarena bai zama lallai dole sai na soki ba ko yin wata muamula dake ba, dan haka ki daina wani rawar kafa dan sam ba birgeni zakiyi ba, dani bakowace mace ce zata iya yaudareni ba ..
me’ad datayi masa kuri da idanunta tana kallonsa ta saukar da numfashi tace” na jinka fu’ad sai dai abinda nake son kasani tunda nice naganka kuma na aminta da kai, zan iya d’aukar komai tare da shanye duk wasu kalamanka gareni sannan zanyi komai dan ganin na mallakeka amatsayin uban ya’yana koda dukiyata zatakare da numfashina..
wani irin kallon banza fu’ad yayi mata irin na sama da kasan din nan sannan yace “iska na wahalar da mai kayan kara .
“Ina tabbatar maka wannan iskar bazata wahalar da mai kayan kara ba ,domin zamu kasance cikin inuwa daya koma nace bargo daya . tana gama wannan mgn ta juya cikin fushi tayi ficewarta shi kuwa fuad daya bita da kallo ya saukar da numfashi cikin sanyin jiki ya mike daga inda yake zuciyarsa cike da tunaninta tabbas tana matukar burgeshi muttaka, har yana jin idan bai sameta ba komai zai iya faruwa dashi .
bayan tafiyarta tashi yayi ya sake yin wanka yasanya kananan kaya marasa nauyi ya tsaya fesa turare inna tashigo hannunta rike da bakar leda mai dauke da ruwan roba da Malta Amman taga wayam babu yarinyar dazu babu alamunta cikin sauri tace ” kai fu’ad ina yarinyar da malik?
Kafadunsa ya daga mata alamun bai sani ba sannan yasanya kai yayi waje inda machin dinsa ke parke.
tuki take cikin ‘bacin rai tana ciza yatsan hannuta gbdy ta kagara taje gida domin ta samawar kanta mafuta akan lamarinta da fuad wani irin taka birki tayi dan karfi gudun kada ta buge abinda tagani a gabanta.
a matukar fusace ta fito daga cikin motarta tayo waje inda tsohuwar take tattakawa ahankali saboda tsufa datayi Dan har ta d’an rankwafa “haba matar nan wannan, wani irin mugunta ce hk wato ke kin gama cin kuruciyarki A cikin tsiya shine zaki ja min masifa wato idan na bugeki kika mutu a kamani ko? to in har hk kike nufi ki sani idan na bugeki na kad’e banza dan dake da kuda daya ne agurina dan hk ki matsa kafin nabi ta kanki da mota..
tsohuwar ta d’ago da kyar ta kyalleta tace yarinya kiyi ahankali ahankali domin an yi wasu kafin ke kuma basu ta’ba cin riba ba kinga kema baxaki ciki riba.
me’ad taji wani irin ‘bacin rai ya turnukota sai dai lokaci daya shawarar da malik yabata ya fad’o mata “fu’ad na matukar son kyautatawa da kyautatawa marashi kenan irin wannan kyautatawa yake nufi?
“bugu da kari mgnr tsohuwar ta kashe mata jiki murus,Dan HK tasoma nadamar abinda ta aikata da farko ta matso sosai kusa tsohuwar tare da rage sautin murya kasa sosai”inna dan girman Allah kiyi hkr nayi nadamar abinda na aika miki, ni kaina bansa abinda yasa wani lokacin nake reacting hk ba, amman kiyi hkr idan magana ta ‘bata miki ,muje na tsalakar dake ta kai hannu zata ta’ba tsohuwar tace “dama kin bar shi yar nan zan iya tsallakawa, sai dai naji dadi da kikayi saurin gane kuskuren abinda kikayi ,ita duniyar ma guda nawa take?” ku dunga d’auka da mai kudi da talaka duk abu daya, saboda Allah da yayi mai kudi shi yayi talaka ba kuma dan baya son shi ba.
“Haka ne inna na gode sosai amman kiyi hkr kibarni na taimaka miki tayi saurin komawa cikin motarta ta kirgo kudi wanda zasu kai kimanin dubu goma ta dawo inda tsohuwar take ta riko hannuta tasanya mata kudin “inna ki amshi wannan dan Allah karki aa”kai yar nan har da wata hidima to nagode kwarai da gaske Allah yayi albarka, Allah yayi miki abinda kike so Inshaallahu zaki gama da duniya lafiya. “Ameen inna na gode.
fu’ad da fitowarsa kensn abun ya faru akan idanunsa duk da bai ji tautaunawarsu ba ,Amman ya ji dadin taimakon datayiwa matar har sanda ta tsallakar daita dayan bangaren tsohuwar na dariya tare da d’aga mata hannu ta koma tashiga cikin motar ta figa a guje yana kallon sannan ya taka mashin dinsa yacigaba da binta abaya batare da tasani ba ,har inda ta sake tsayawa saboda hango wata makauniya rike da yar jagoranta wace bazata wuce kamin shekara takwas ba ta mika musu sadakar dubu daya bayan ta tsaya sun tsallaka abu kmr wasa hk ta dinga taimako mutane wanda abin yacikasa da mamski “daman tana da zuciya irin hk me kyau ?”gsky idan har tana da irin wannan halin na taimakawa marasa karfi ta cancanta tazamo abokiyar rayuwarsa, adaidai jection din bankole suka rabu shi yayi titi dopemu road ita kuma kai tsaye gida ta nufa inda ta iske sunyi bakin da suka dade suna expecting zuwansa, wato safwan almustapha maitama daga kasar hollond, mahaifin safwan baban mutun ne a kashen duniya gbdy ,sannan me gidan mahaifin me’ad ne a can baya kafin yayi rites . Safwan ya dawo daga kasar Holland ne da niyyar abubuwa guda biyu, na farko cima burin auren mead daya kwalafawa ransa tun shekarun baya, sai abu na biyu cigaba aikinsa amatsayin shugaban shashi na kasuwancin Nigeria.
jin ana jera mata sannu ne yasa mom dinta yin saurin fitowa dan tayiwa yar tata gargadi kada ta kawo musu wargi .
me’ad ta kalli uwar cike da mamaki “ni wai momy meyasa kike min hk ne?” narigada na gaya miki na canza mind dina akansa yaje gaba ya auri matarsa ni matar fu’ … momy tayi saurin rufe mata baki “karki sake me’ad kiyi ganganci, karkiyi wasa da damarki,domin damar mutun sau daya take zuwa masa arayuwa, ina shawartaki karki bari taki ta subuce miki.
me’ad tayi wani irin murmushin sannan tace, karki damu momy da subucewar wannan damar ni dai fu’ad nake so simple as that tana gama fad’ar hk tashiga cikin parlour’n mahaifinta wanda sai bakinsa masu mahimmanci yake tara acikinsa ,ta samu gefe daya ta zauna “dad sannu da zuwa ya hanya ?
mahaifin safwan ya amsa da kulawa sannan ta waiga inda safwan wanda tun shigowarta idanunsa ke kanta yana kallonta saboda wani irin azababben kyau dayaga takarayi masa sai dai ta rame kad’an Wanda bai San dalilin faruwar hkn ba ,sautin muryarta ce ta dawo dashi “yaya ina yini?
ya lumshe idanunsa na second biyu sannan ya bud’esu fess akanta kanwata kin yini lfy?
tayi masa wani irin kallo mai bugar da zuciya sannan tace lfy atakaice.
sun jima a parlour’n dad dinta ya dubeta yace ki kai yayan naki lambu ya huta mana , babu mutsu me’ad ta mike shima yabi bayanta cikin matsananci farinciki yayinda ita kuma ba’a son ranta ba Dan dai babu yadda zatayi ne.
wani parlour’n ta kai shi al wanda duk gidansu babu irinsa an maserfar zuba abun duniya agurin ,an zuva komai wanda me rai yake burin mallaka.
bayan ya zauna tasa aka gabatar masa da abubuwa sha kmr yadda tasaba sannan ta sake tashigowa batare da wani abu ba ta zauna shiru batace masa komai ba gbdy sai yaji baya bukatar cin komai dake gabansa illa matsowa da yaayi ya saita bakinsa daidai kunneta “ina sonki mead dayawa amman banji dadin yanayin dana ganki ba at least kinsa ina bukatar kulawa daga gareki. .tace har da gaske kana sona har yanzu ka mayar da akalar soyayyata ga wata in har kana son farincikina .