YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 11 to 20

A matukar firgice ya tsura mata ido yana kallonta Kafin daga baya yace “no no hkn ba zai yuwuba “saboda me ?”saboda bana sonka yanzu sannan karka kazamanto me yawan wahalar da kanka wajen sake tadda zance aurenmu domin ahalin yanzu zuciyata bata gareka , ta kamu da soyayyar waninka ,da sauri safwan ya kalleta cike da matsanancin mamaki abinda take fad’a masa yayi shiru ya kasa cewa komai illa jikinsa dake rawa.. 

“kaji abinda nace amman har yanzu ka kasa Cewa komai, ko magnata ta kurmanta da kai ne?

. “ko daya kawai mamaki kikabani shin kin manta matsayina a gidan nan dama duniya gbdy?

“sam maganganunki a yau babu girmamawa balle nuna tarbiya, “dan Allah ki gyara maganarki sam banji dadin yadda kika min ba saboda har yanzu ina sonki me’ad kuma banga abinda zai hanani aurenki ba matukar ina raye.

 da sauri me’ad ta kalleshi cikin mamaki tayi wata dry na rainin hnkl ” amman baka kyautawa xuciyarka ba sannan bakayi tunani me kyau ba, karkayi takamar dan mahaifinka me gidan mahaifina ne bazai sa nagaya maka abinda ke cikin zuciyata ba, idan kuma kayi kuskuren aurena girmamawa zai yi wahala ka samu romon da maxa dayawa in sunyi aure suke samu ba sai nagaya maka ba dan nasan kaima agidanku akwai irina safwan kake ko wa kake ;? ina son nagaya maka wallahi ban ta’bawa yiwa kowani mahaluki karya ba ko shi waye to kaima bazan ma karya ba, safwan har ka aureni bazan maka biyyaya aure ba sannan bazakayi min kulle ba, duk abinda nake so shi zanyi agidanka,kuma ba lallai ne na dinga maka girki ba idan taka ma har Wanda nake so sai na kawoshi gidanka kuma nayi duk abinda nake so dashi ,idan har kaga zaka iya to kana iya turo a karasa mgnr aurenmu da kai ,idan km ka janye niyyar aurenka akaina sai mucigaba da muntuncinmu , tayi shiru tare da mikewa tayi hanyar kofa, har ta zira kafarta daya a kofar parlou’n sannan ta tsaya batare data jiyo ba tace zaka iya fitowa ka tafi tunda na sallameka ..

tana gama fadar hk ta juya shi kum safwan da bita da kallo sannan ya saukar da numfashi ckin sanyi jiki ya tashi ya nufin parlour’n zuciyarsa cike da tunaninta tabbas yasan yana son me’ad so kuwa me tsanani har yana ji aransa matukar bai aureta ba tabbas akwai Matsala dan wannan abun datayi masa mugun burgeshi tayi shifa bai ga dalilin da zai bar wani me’ad dinsa ba alhalin yana raye bai mutu ba ,babu wannan nmj a duniya kuma kowaye sai ya nemoshi da karfinsa da dukiyarsa .

 ita kuwa me’ad byn tafiyarsu ta shige part dinta ta sake wanka tasanya kaya marsa nauyi sannan ta fito paloun mom dake zaune ita kadai tana kallon labarai a CNN jin takun me’ad tana saukowa daga step ” momy kallon kike ke kad’ai a parlour’n ina suhailat ? 

momy tayi dry ai daman yanzu zan kiraki dan ina son naji yadda kuka yi da safwan. 

me’ad tayi saurin kallon momy tace “waye km hk an?

da sauri momy tayi saurin kallo me’ad cikin mamaki da tsoro, cike da in ina momy tace ” me’ad me ye nufinki? 

batare da ta kalli momy ba tace “nufina bawai wuce ya nemi wata ya aura ba danni har abada ta fu’..

“yi min shr me’ad kada ki meidamu kanana mutane tare da meida hannun agogo baya dan wallahi tallahi baki isa ba a wannan karon mune muka haifeki dole muyi duk yadda muke so dake wallahi baki isa kiyi mana mugunta ba dan hk ki meida hankalinki cikin jikinki tun kafin mahaifinki yaji .

“momy kingama ?

me’ad ta fad’a batare data kalleta ba, bata jira abinda momy zata ce tacigaba “mom ni babu ruwana da dady yasani dan nafi son hk, kowa fa takasan yake yi yanzu dan hk baxaku matsamin ba, dan kawai kun kawoni duniya, ku dai yi hkr zanyi shawara da zuciyata idan na rarrashita akan fu’ad taji zata iya rabuwa dashi fine then zan iya auren safwan ,amman idan taki hakura sai dai kuyi hakuri, duk yadda nayi da zuciyata zan gaya muku tana gama fadar hk ta mike zata fita momy itama ta mike cikin bacin rai da fushi ta riko hannunta har sai datayi kara. 

“momy cire min hannuna zakiyi dan kawai banason safwan ?  

momy dataga ala’mun fa yarinyarta tayi zurfi sai ta kwantar da murya “kiyi hkr me’ad ki zauna muyi mgn nasan zaki fahimci mamanki. 

me’ad ta kurawa momy ido tana saukar da numfashi momy “kema kiyi hkr ki barni da zabin raina sannan mgnr da zamuyi ,mayi idan na tashi daga bacci tana karasa fadar hk ta mke ta koma samanta momy tabita da kallo cikin takaicin domin ita kad’ai tasan bala’in daza’a yi idan mahaifinta yasan tana soyayya da talaka abunda shi ya tsana kenan had’a hanya da talaka arayuwarsa .

me’ad kuwa gadonta ta haye tayi kwancinyarta tare da rufe idanunta fu’ad fess take gani acikin idanunta har ga Allah wani irin so take masa me tsuma zuciya da wuyar bari ..hk tayita tunaninsa har bacci ya dauketa bayan ta tashi momy tashigo d’akin tayita rarrashita amman furrr taki yarda da zabin iyayenta “momy tun farko banason safwan ke dady kuka matsa min ,ta yaya yanzu nasamu wanda nake ku nemi hanani aurensa. 

“Ba hanaki aurensa mukayi ba ki tuna alkwarin dake tsakani Dan allah yarinyata ki duba lamarin nan “momy kema uwa ce nasan kinsa abinda ake kira da soyayya tunda nasan ba hadaku akayi da dady ba, ku kuka ga junanku ,ina rokonkanki momy ku barni da fu’ad wallahi akansa zaku iya rasa takarasa mgnr tana kuka . ..tsakanin uwa da ‘ya tuni itama ta sauko taji zabin diyarta yayi mata, zata bata damar ta auri zabin zuciyarta..

Ranar da kyar safwan ya runtsa kwana yayi yana zubawa cikinsa giya da tunanin abun yi, “tabbas yakamata ya d’auki mataki nemo kowaye ke kokari kawo rayuwarsa nakaso ,tun da sanyi safiyya ya baza yaransa domin bincike akan wanda mead take so .

Tashin farko bincike ya zo masa akan yadda bai so ji ba ,domin duk wani abinda ya danganta da fuad da rayuwarsa sai daya zo masa daki daki ya sha mamakin” wai Dan talakawa me’ad take kokarin neman gujewa aurensa ,aransa yace” idan kinsa wata ai baki San wata ba ,nasan dai babu ta yadda za’a mahaifinki ya yarda ki aureshi, balle shi karan kanshi yaron bai sonki ,gbdy safwan yazaba yaransa a gari domin cigaba da kawo masa rahoton komai akan fu’ad. 

******

 ranar monday da misalin karfe 1:00 na Rana kabir yazo gidansu fu’ad domin zuwa office din Alhaji Abubakar aminin mahaifinsa Wanda zai samarwa fu’ad aikin da kaninsa ,a shiryensa yake zaune a kofar gida yana zaman jiran karasowar kabir yana hangosa yashiga cikin gidan inda yakewa inna sallama “inna mu za fita akan zance neman aikin kiyi min adduar samun nasara kansa ta dafa “InshaAllahu zaayi nasara zaka samu wannan aikin ina jin hk ajikina sai dai Wani tsananin rabo”allah yasa ni na wuce, “a dawo lfy Allah ya tsare, “ameen ya fice daga dakin .

kai tsaye company da alhj Abubakar ke tafiyar da aiki suka nufa akan lefan din fu’ad suna isa suka iske jama’a wanda dayawansu neman abunyi ya kawosu, batare da bata lokaci ba suka nufi office Alhaji Abubakar inda suka iske shi yana sallah sai mataimakinsa sukagani suka gaisa ya nuna musu gurin zama “ku zauna ga guri nan ,suka zauna har zuwa sanda ya idar yakaraso garesu inda kabir yayi saurin cewa dady barka da Warhk “a’a kabir har kun iso?ya fad’i hk tare nufar hanyar office dinsa dake cikin wanda suke zaune da sauri kabir da fu’ad suka mike sukabi bayansa atare suka shiga kabir yasamu guri ya zauna akan daya daga cikin kujerun gurin tare da jawa fu’ad shima ya zauna “ai kuna da sa’a duka takardun mutun biyu din da ka kawo sun samu aiki,Amman D’an bani minti 2 ya fadi hk sakamakon wayarsa dayaji ta d’auki kara ya zagayo ya zauna mazauninsa tare da d’aukar wayar ya manna kunnesa abinda yaji ne ya kusan bugar masa da zuciya “safwan almustapha maitama ne ke mgn da kai daga nan office din jakandancin na kasuwancin Nigeria, naji ance wani mai suna fu’ad yazo neman aiki gurinka ko ba hk ba ?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button