YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 11 to 20

 cikin hk ruwan saman ya tsaya cak sai kuma harbi takoina a harabar gurin, harbi fa sosai ban san yadda akayi ba sai dai ganin nayi fu’ad ya kamo hannuta sai ga yarinyar manne da kirjinsa nan take suka tsurawa junansu ido suna kallon junansu, wanin harbin yasa tayi saurin shigewa jikinsa gabadaya domin neman mafaka.

cikin minti biyu kacal duk ilahirin gurin ya har gitse, jamar dake wucewa a gurin bubu wanda ya damu da halin da kowa yake ciki, kowa gudun ceton ransa kawai yake saboda gabadaya gurin ya hargitse da k’arar harbi, police na harbi ,y’anta’ada na meida musu .

“ai in gaya muku na rud’e tare da gigicewa amman fu’ad da yarinyar nan ko ajikinsu kallon junansu suke karasowa garesu nayi ina girgiza fu’ad domin shi nake da yancin tabawa, nayi sa’ar ya dawo cikin haiyacinsa amman ita yarinyar ruhinta yayi nisa akansa ,girgizata fu’ad yasoma yi amman ina bata ma san yanayi ba, cikin rud’u ya rike hannunta ya kwasa aguje yasoma gudu daita, ganin harbin na sake yawa, sannan yana kiran sunana ,ni kuwa daman tuni na boye bayan inji din cire kudi ina kirma..

“kusan awa daya ana batakashin tsakanin ‘yanata’ada da police har zuwa sanda acp aliyu rano yayi nasarar harbe wannan mutumin a kirji sannan komai ya lafa gurin gbdy ya turnuke da hayaki daya bayan daya mutane suka soma bayyana fuskarsu cike da matsanancin firgici daga mubuyarsu, ni kuwa sai ware ido nake naga ta inda fu’ad zasu fito, ahankali sai ga fu’ad da yarinyar nan makale da juna sun fito daga mabuyarsu aiko gama bayanarsu ke da wuya sai agaban acp wanda naji yace”a’a me’ad me km kike yi anan ?

hankalinta kwance tace “uncle nazo cire kudi ne ina fatan babu abinda yasameka? ta fadi hkn ne saboda ganinsa rike da hannunsa ga jini na tsiyaya alamun an harbeshi .

” ina jin dai lafiya kalau nike me’ad, waye wannan da kuke tare dashi ? 

da sauri ta juyo gefenta fu’ad tagani tsaye agefenta hannunwansu malake cikin juna ,jin Abind acp yace yasa fu’ad yin sauri zare hannunsa cikin nata yana shafa sumar kanshi .

 d’an runtse idanunta tayi kana tace “amm bansashi ba ucnle ,yanzu muka had’u dashi ta juya tana kallon fu’ad kmr zata cinyeshi muryata a sanyaye “tace sunana me’ad nagode da taimakona dakayi. 

“muryarsa a dake yace ni kuma fu’ad karki damu ya juya ,naga yasoma waige waige ala’mun yana nemana, ita kuma tabishi da kallo yayinda acp aliyu yakira daya daga cikin yaransa “md .

“na’am yallabai . 

” taimaka ka’ajiye min wannan yar tawa a gida. 

“ok yallabai kasa daga kafafunta tayi agurin, tacigaba da kallon bayan fu’ad . 

ina kallonta, jiki a sanyaye tashiga bayan wata hadadiyar mota kiran toyata camry .

 Ina kawowa karshen labarin nace ni dai dan Allah ku gaya masa idan bai sonta ni dai ta min, ina sonta kuma aurenta zanyi, aikuwa suka ce me zasuyi ba dariya…. “kai wallahi bazan ne a gbdy labarinka fu’ad take so bakai ba ,koda yace baya sonta kana tunanin zata soka ne? 

take na marairaice murya da fuska “ni dai ku taimaka ku tambayar min shi idan bai sonta ya tsaya min na aureta, wallahi dagani yar babban gida ce kunga motar da za’a kaita gida dashi kuwa , kuma dagani akwai halaka me karfi atsakaninta da acp Aliyu rano.. 

“kai dan Allah malam rabudamu da wannan shirmen banza suka soma kokarin watsewa su barni ,nayi saurin kamo hannun sudais, kai ma tafiya zakayi kabarni?

“Kai rabu dani, idan kana son yarinyar da gaske kawai ka nemi gidansu Dan gsky nasan fu’ad ba sauraranta zaiyi ba ,dan shi bashi da lokacin mace ,mata nawa suka nuna suna son shi Amman yaki? 

********

bangare me’ad kuwa zuciyarta ce ke mugun buguwa a tun sanda tashiga bayan motar tare da hasko mata kyakkwar fuskarsa “tun datake bata ta’ba had’uwa da saurayin daya tsaya mata arai ba kmr shi, sai dai daganin zai yi jin kai da girman kai tattare da isa. 

zaune suke su uku sajida misna hailat , sun mugun tsurawa TV plazma ido dake manne da bango suna kallon batakashin da’aka tafka tsakanin ‘yanta’ada da ma’aikan sack a dapemu express way dake jahar lagos “barkanmu ,a yau anyi musayar wuta tsakanin ‘yansanda ,da ‘yanta’ada an samu nasarar harbe wani dan ta’ada me hatsari, acp aliyu rano da jamiansa su sukayi nasarar harbe nabel wanda ya kasance babban dan ta’adar da jamian tsoro suka dade suna nemansa a fadin jahar nan.

“yeeeeee babana yazamo zakaran gwaji….. sajida tasoma murna har da tsallenta “nasan kwanan nan za’ayi wa babana k’arin girma…murna take sosai tare da rungume misna dake kusa daita “gsky na taya dad dinki murna sosai inji cewar misna , hayaniya ce ta kaure atsakaninsu kowanensu na fad’ar albarkacin bakinsu. 

 me’ad tashigo hadadden parlour’n gidan wanda ya k’awatu tamkar da tayis akayi ginin ,gashi an zagaye shi da manya furanin. 

hannuta rike da karamar jaka wace bata wuce a sakalata a tsintsiyar hannuta ba tana juyi sanye cikin doguwar rigar ” kawayena yau na had’u da wani saurayi kuma ko wallahi kyakkyawa gaske ne kalar launi danafi so.. takaraso garesu tana murmushin jin dadi “kunji aunty dan allah da wata magana ana labari da d’umi d’uminsa ke kuma kina labarin wani saurayi , “dan Allah malama kiyiwa mutane shiru had’ad’d’e ne fa sosai, Allah ina gaya muku duk fadin garin nan babu me kyawumsa ta karasa fad’ar hk tana sake juya jikinta .

“haka zakice tunda zuciyarki ta yaba dashi ba ,da baki yaba dashi ba duk kyawunsa sai kin nemo makusansa” kmr kinsani kuwa inji cewar misna . 

“wai ina miki wasa ne suhailat, ko dake nake maganata? ta fad’i hkn tana tsaki sannan ta fuskanci sajida da misna. 

“ku kuma daku fa nake mgn amman kuka min shr , ba ma zaku saurareni ba ,kuna can kallon kwazon da acp yayi “ke dai bari me’ad Allah ina cikin jin dadi yau ,ina ma mama tana raye ta dinganin irin cigaban da baba yake samu, wannan furunci da sajida tayi yasa me’ad kasa cigaba da tsayuwa a gurin ta nufi hanyar d’akinta tana magana “Allah ya jikanta sai dai ki shiyawa jinyar dad dinki bayan kingama tayasa murna k’arin girman da zai samun saboda ‘yanta’ada sun harbeshi .

da sauri sajida ta mike jikinta na rawa tabiyo bayanta atare suka shiga dakin “da gaske an harbi dady? 

“ke baki lura ba, bakiga ya dafe hannunsa na dama ba? 

“ina tunanin anan aka harbe…….

ai sajida bata jira jin karashen zance ba, tayi waje aguje tana kiran layin dad dinta, tayi sa’a ya d’auka “hello dady.. 

“sajida kina lfy?

” ina lafiya dady kana ina?” yanxu me’ad ke gaya min wata mgn da gaske ne ‘yan ta’ada sun harbeka? 

“gaky ne sajida ,duk boyewar dana yi ashe ta lura, to dai ki kwantar min da hankalinki, yanzu haka an cire min harsashi , mu had’u a gida, kashe wayarta tayi tare da bud’e murfin motata tashiga ta bar gidansu mead a guje. 

mmn sudais ce

????????????????????????

       ‘YAN CINKI

      ????????????????

????????????????????????

             ~NA~

 *AYSHA A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

      MRS ADAM

( YAR MUTAN KAGARA)

page 42 to 44

……Ahankali malik ya sauke kwayar idanunsa akan NASREEN dake kwance ajikinsa ,wacce bacci yasoma kok’arin d’aukarta amman son jin labarin had’uwar iyayenta ya hanata runtsawa .

shiru malik yayi yana dubanta batare da yacigaba ba, ya d’auki sama da minti goma a zaune kawao yana kallon NASREEN cike da tausauawa, yarinyar tana bukatar kulawa takowani bangare, amman tarasa shirun da NASREEN taji yayi yawa ne yasa ta, bud’e idanunta dake runtse taki sunansa “Uncle malik continue now…. kacigaba ina son jin komai, domin kai kad’ai ne zaka iya ‘bata lokacinka ka gaya min. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button