YANCIN KI Page 11 to 20

“NASREEN …ya kira sunanta a sanyaye “na’am unlce “kwalkwaluwarki bazata iya d’aukar sauran labarin ba.. “zan iya uncle am getting to 10yrs now babu abinda zaka fad’a da bazan fahimta ba.. ina jin tausayin dad dina dayawa, ina son nasani wani abu akansa takarasa maganar tana meida kanta bisa cinyarsa..
naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa “daga bangaren fu’ad da me’ad babu wanda bansan halin dayake ciki ba, akoda yaushe muna tare da fu’ad, haka me’ad duk inda tasanya kafa ina biye daita sai dai a iya nan zan tsaya … ya d’auke kanta akan cinyarsa ya meida kan karamin kushin din dake jingine da kujera, sannan ya mike tsaye yana duba agogon bangon parlour’n karfe tara ta wuce da wasu ‘yan mintunoni, wayarsa ya ciro daga gaban aljihun gaban rigarsa yana kokarin neman layin fu’ad, sai gashi ya fito “yauwa zo kaji da wannan yar rigimar taka, ta matsa,lallai sai taji haduwarku da me’ad, ni dai nayi kok’arin sanar daita kad’an daga cikin had’uwarku sauran kuwa na barta da bagudo takarasa mata yakarasa fadar hk yana murmushi, murmushi fu’ad yayi shima sannan yakaraso inda take kwance kmr ruwa , ya komata ya zaunar daita tare da yi mata makari da pillow ta bayanta “kinji abinda uncle malik yace ?
“ni ..ni naji amman babu ruwana dashi tunda yaki yacigaba dabani labarin, takarasa mgnr muryarta a shagwabe kmr zatayi kuka,kissing din goshinta yayi “don’t cry my bby rabu dashi kinji bby nah ni da kaina ma sai nabaki, ai zaki fi son nawa ko?
ta gyda masa kai kawai batare da tace komai ba fu’ad ya fuskanci malik “yanaga kana kok’arin tafiya batare da kaci komai ba?
“kai rabani da cin abincin nan, yanzu ina ci idan naje gida sai nayi bayani daya bayan daya, an dinga yi min qausetion’s kenan ,gara kawai idan na koma gidan naci gbdy, ok muje na taka maka “baby nan ina zuwa just give me w minti .
har waje fu’ad ya rako malik suna sake tautaunawa akan sha’anin rayuwa, da hakuri da rayuwar ita karon kanta …
koda fu’ad ya koma parlour’n bai iske NASREEN ba ,dan hk kai tsaye ya nufi d’akinta ,inda ya isketa kwance cikin blanket dinta, ya yaye blanket din tare da d’aura hannunsa kanta “my bby kin sha maganinki? “yes dady .
“ok kiyi bacci abinki Allah ya baki lfy me d’aurewa .
“ameen babana, shiyasa nake sonka…..
“i love you more yacigaba da zama yana dubanta tana matukar bashi tausayi yana jin kmr ya ajiye komai ya bata kulawar data dace, ita kad’ai garesa kmr yadda ya kasance, a zahirin gasky baya son yarasata duk da kasancewarta mai karancin lfy yana sonta hk… tsawon lokaci yana zaune yana tunani har sanda bacci ya d’auketa sannan ya yunkura ya tashi ya nufi d’akinsa ya kwanta lamo akan gadon yana tunani ya saka wancan ya kwance wancan, runtse idanunsa yayi sosai yana kiran sunan Allah, ahankali ya bude idanunsa wanda suka kad’a sukayi jawur saboda tuno abinda yake yi masa cikin rayuwarsa, a filli yace “nayi dana sanin aurenki me’ad dana san hk zaki zamomin arayuwata da ban yi kuskuren aureki ba…hawaye ne yaji suna sauka masa akan kuncinsa ,cikin sauri ya sharesu, lokacin ne wayarsa ta d’auki kara, ya kai hannunsa ya d’auka akan bed side ya manna a kunnesa batare daya duba ba.
sautin muryarta yaji ta doki dodon kunneshi ,yayi Shiru tare da janyo pillow ya manna akirjinsa ya rungume tsam sbd d’and’anon dadin muryar “hello hello fu’ad kana jina !! ta sake maimaitawa akaro na biyu.
“uhmm ya’akayi kira adaidai wannan lokacin ko kin manta ina iyali ne ?
“am sorry for disturbing you , but ina son ka saurareni fu’ad kaji abinda za….
saurin katseta yayi ta hanyar cewa “sauraran me zanyi miki, karki meidani wani shasha mana ,ta yaya kike kokarin manta dangantakarki da me’ad mana ,karki manta har yanzu me’ad matsayin matata take, dan me kike kokarin sanyo damuwa acikin wace nake ciki….?
” fu’ad ka saurareni mana, haba fu’ad ya dace ace nasamu kar’buwa a wajenka a daidai wannan lokacin, na d’auki sama da shekaru goma ina dakon soyayyarka batare dana fayace maka ba .
” wannan damace tazo mana, kabari mu dama mana dan Allah … karka ki amsar soyyayata saboda dan adam daraja garesa, idan ka amince zaka aureni zan ajiye komai har aikina domin na baka farinciki dakarasa.
“dakata dakata malama enough is enough don’t talk any rubbish.. “kinsa yadda zaki bani faricikin any not ki fahimtar da me’ad tabi abinda nake so domin a zauna lafiya?
” ni dai ka ajiye mgnr wata me’ad kawai ka amince da au..
“ok baxaki iya bata wannan shawarar ba amman zaki iya shigowa gidanta amatsayin kishiyarta ko…?
“ka fahimceni fu’ad ba …
“babu wata fahimtarki da zanyi idan ma aure nake da bukata ,bake zan aura ba…. bake ya dace na aura ba, ina da ido nasan inda mata suke okay, dan haka ki shafa min lfy if not zan gayawa me’ad da kaina tasan yadda zatayi dake ya katse kiran yana fitar da numfashi sama sama.
“meyasa kayi haka?
zuciyarsa ta kismamashi hkn, “m e yasa baka amshi tayin soyayyarta ba?
take yabawa zuciyarsa amsa da, bazan k’ara wannan kuskuren ba bazan sake kuskuren auren ya’yan masu arziki ba…….
a ranar fu’ad baiyi ishashen bacci ba, juyi kawai yake ga tunanin ciwon NASREEN ga kewar iyayensa dake addabarsa uwa uba matsalar me’ad da sabuwar matsalar dake shirin kunno kai, har karfe daya ta buga fu’ad bai san yadda zai yi da al’amura dake kokarin kusowa rayuwarsa ba. ahankali tunanin haduwarsa da me’ad ya dinga zuwa masa daki har zuwa lokacin da sajida ta bar gidansu me’ad agigice zuwa gidansu taga lafiyar mahaifinta .
“koda sajida ta koma gida hankalinta yayi matukar tashi saboda ganin raunin harbin da d’anta’ada yayi masa, kuka take sosai tana “furta sannu dady ..shi kuma yana rarashinta da kyar dai yasamu tayi shiru.
ita kuwa me’ad bayan ta tagama kimtsa kanta tattare da tunanin sabon fuskar data tsaya mata arai ta nufo hanyar parlour tana kwallawa me aikinsu kira ” ummi ummi!! har takaraso parlour’n shiru babu kowa hatta misna da suhailat basu gurin, nan ranta ya soma baci tashiga kai kawo ta sake dawowa cikin parlour’n tattare da matsancin damuwa tasamu guri ta zauna tare da d’aura kafar daya kan daya tana girgizawa tare da cizon yatsanta ummi dake d’akin suhailat tana mata guga tayi saurin ajiye Iron ta fito da gudu tana haki, cikin rawar murya tace “aunty gani me’ad ta d’auke kanta cikin isa tace, “ummi ina son tambayarki…
ummi ta d’aga kanta da sauri cikin tsoro jikinta yana rawa tace “kiyi duk irin tambarki da kike so.
me’ad ta sake d’aure fuska kana tace “wai shin nan gidan ubanki, ko kuwa da gadonki acikin wannan gida..?
da sauri ummi ta sake d’ago fuskarta ta kalli me’ad lokaci guda, kuma tayi saurin d’aukewa dan wani irin kallon da me’ad ta watso mata, sannan cikin rawar muryar tace babu ko daya sai dai kawai cin arziki danake yi acikinsa.
“okay a she kinsan cin arziki kike yi amman kike neman kifi ya’yan gida sakewa, ki km fisu iko ko?
ita dai ummi tayi shiru kawai tana kallon kasa dan daman hk halin me’ad din yake duk wanda yake kasanta ,sai yayi hakuri, in kuwa ba hk ba zai rasa aikinsa acikin kankanin lokaci. me’ad ta girgiza kafarta cikin isa da iko “daga yau duk sanda na sake kiranki, kikayi banza dani wallahi kinji na rantse in har baki rasa aikinki ba, zaki had’u fushina jahila kawai dabba mummuna…….