YANCIN KI Page 11 to 20

mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 45 to 46
………”Wallahi Ba kiga yadda na tsanaki ba, ji nake kmr na kasheki ta had’e hannunwanta duka biyu al’amun da gaske zata iya aikatawa abinda ta furta .
da sauri ummi taja baya tare da furta ” Dan Allah aunty kiyi hakuri Insha’allahu bazan sake ba,zan kiyaye ….
“Kar ma ki kiyayye kiga yadda zanyi dake .
“Kiyi hakuri ta sake furtawa jikinta a sanyaye “Dan Allah malama banason long talk tashi ki bani guri kazama kawai.
Ummi ta mike jiki a sanyaye babu laka ta fito, idan da sabo tarigada ta saba da wulakancin me’ad.
Me’ad taja dagon tsaki lokaci daya taji gabanta yayi wani irin mahaukacin bugu da karfi , tayi shiru tana tunanin abinda ya sata jin hk, take fuskar fu’ad tasoma yi mata gizo acikin ‘kwal’kwaluwarta ,runtse idanunta tayi kawai ta d’auki wayarta tare da mikewa tsaye ta haye sama inda mahaifiyarta take zaune da system agabanta tana tura sakonni, shigowarta d’akin yasa mom dinta d’agowa tare da cewa ” yauwa gara da kika shigo, yanzu nake son aikawa akira min ke, me’ad takaraso jiki a sanyaye ta zauna kusa daita “gani sweet momy dina,ina matukar alfahari da kasancewarki mamana “uhmmmmm dan kinga abbanki baya kasar ba,?
“kai momy wai meyasa kike kishi da dad ne?
“nifa gbdyanku ina sonku domin banida abin so fiyye daku a duniya ku ne komai na.
“kinga bason zance karya ina file din da hjy maryam tace ta tura dazu da safe?
tsam tayi da ranta sannan tace” yana cikin jakata “okay je ki zo min dashi yanzu akan aikinsa nake.
cikin mintina kad’an me’ad ta fito daga d’akin mom dinta , ta nufi d’akinta tasoma duba jakarta amman abun mamaki babu diary dinta ballanatana file din dake ciki, gabanta ne ya sake fad’awa , lokacin da ‘kwal’kwaluwarta ta hasko mata ko dai ta yarda dashi agurin batakashin da ya rutsa daita gurin cirar kudi.. “tabbas in har bata ganshi ba definitely acan ta yar, ta furta hkn a fili tana cigaba da bincike gefe da gefen jakarta sannan cikin sauri ta fito da niyyar komawa gurin, har zata fita sai taga kmr shigarta batayi ba, basani ba, ko zata sake had’uwa da wannan kyakkyawan fu’ad , Dan haka takoma cikin d’akinta .
ta fito cikin wani koren voyal dinki doguwar riga har kasa ba D’an kwali a kanta ,sai koren mayafin data yane kanta dashi, takalman kafarta suma duk kore ne, ta cigaba da tafiya cikin yanga, ta isa inda aka tanada domin ajiye motocin gidan, ta tsaya tana karewa motocin kallo ,4mart itace wace zuciyarta tabata umarnin shiga .
Tun kafin ta kunna motar me gadi ya zabura ya mike tsaye, yasoma kok’arin bud’e mata get, ahankali tasanyo hancin motarta wajen gidan..a natse take tukin m .
kai tsaye ta d’auki hanyar isa inda suka had’u da fuad ,cikin kankanin lokaci ta iso ,tasamu guri tayi parking din motarta ,tana bin gurin da kallo abubuwan da suka faru a d’azu da safe ne suka shiga dawo mata, tun daga kan sanda ta d’aura idanunta akansa ,har zuwa lokacin data nutse a tsakiyar faffad’an kirjinsa…fuskarsa , ajinsa, jin k’ansa da komai nashi sunyi mata ,ta dad’e bata ga halitar da kai tsaye aganin farko ya mamaye zuciyarta ba .
fitowa tayi daga cikin motar ahankali tana dube dube, duk da zuciyarta na tabbatar mata bazata gansa ba adaidai wannan lokacin ,dan haka tasoma duba inda suka had’u, bata jin ATM dinta domin tasan cikin kankanin lokaci zata mallaki wani ,tafi bukatar diary din dake d’auke da manya sirrinkan rayuwarta tare da file din momy dinta, da shi kanshi fu’ad ,Saboda idanunta na matukar kwad’ayin sake ganinsa .
ta kasa hakuri tsayuwa guri daya, tayi tafiya me nisa dan har ta kusan shiga alimoshi local government, amman bata ga ko mai kama da fu’ad ba da diary dinta , sannan ta dawo gida cikin wani irin ‘bacin rai ,cikin sarsarrafa ta shiga parlour’n, yau kam gabadaya a sama take jin kanta, kuma duk wanda yayi kok’arin shiga track dinta zai had’u da ‘bacin rainta.
a daidai tsakiyar parlour’n suka ci karo da mahaifiyarta “ke kuma daga ina haka kika yi wani wujiga wujiga dake?
me’ad ta dan tsosa tsakiyar kanta batare da tace komai ba, “dake fa nake magana kina jina?, kinsa banason wannan fitar ta babu gaira babu dalili ko.
takarasa mgnr tana jan tsaki sannan tace “ina file din danace kin kawo min?
“uhmm ammmmm daman shi naje nema ,daxu da safe ko da direbanta ya kawo na shirya zanje injin ciro kudi sai na kar’ba na saka acikin diary dina ,amman narasa komai nawa ina tunani agurin bata kashin nan ya subuce acikin jakata ,”yanzu hk gurin na koma ko zangani amman …..sai tayi shiru ta kasa k’arasa maganarta sakamakon wani irin kallo da uwar ta jiho mata ….
“abinda kike kok’arin cewa baki gani ba, ko ba abinda zaki ce min kenan ba?
me’ad tayi saurin d’aga kanta “kinsan ko file menene kika yarda shi? ”
file ne dake tattare da mahimman bayane akan kudad’en marayun ya’yanta, amman kalli yadda sakacinki yasa aka rasashi , keda zaki ajiye abu a gida amman kika fita dashi, nan fa suhailat tafiki kaifin baseera “am really sorry momy zanyi kokari na nemo.. ” a ina zakigani?
” zan sake komawa gurin ko Allah zai sa nagani takarasa mgnr tana narke fuska alamun shagwaba.
“ke bar shi kawai zan sake tuntubarta ko tana da wani copy “thank you my mom …. hjy khadeeja ta shige d’akin mai gidan . Ranta babu dadi ta shiga d’akinta tana shiga ta fad’a saman gadonta ta kwanta flat tare da runtse idanunta
*******
Misalin karfe tara na dare ranar a kwance da fu’ad yake ya ciro D’an karamin diary dinta brown me d’igon ruwan zinari, daya tsinta bayan rabuwarsu da me’ad ,yana kallonsa dagani kasan me tsada ne ,ahankali ya kai diary din daidai saitin hancinsa yana shinshina, ni’imtaccen kamshin, Dior addict daya kama jikin diary sosai ,sai kawai yasamu kanshi da lumshe idanunsa tare da bud’esu duka atare cikin wani sabon alamari da ba zai iya kwatantawa ba, a lokacin fu’ad matashi ne Dan kimanin shekaru talati cif da haihuwa ,duk inda ake neman kyau ga d’a nmj fu’ad ya mallakeshi ,fari ne tass me dagon hanci da yawon suma me kyawawan idanu farare kal kuma manya masu cike da nagarta .
Cikin sand’a malik ya iso inda yake kwance ya fixge diary din yana dubawa yaga wasu mahimman file da ATM atsakiyarsa, fu’ad ya d’ago idanunsa ya kalleshi a matukar tsorace.
” uhmmmmm daman nasan ka fad’a tarkon son yarinyar nan ,amman kake wani son waskewa, shiyasa fa nace idan kana sonta ni na hakura nabar maka , kaje ka nemi soyayyarta, amman ka tsaya wani jin kai …”kana sonta ko ba hk ba abokina?
“Tsaki fuad yaja a d’an hassale sannan ya juya masa baya “kai dai ayi D’an matsala wallahi, kaje man kayi introducing kanka agurinta Dan ni bata gabana …..
” shiyasa naga ka tsurawa diary dinta ido ba ,tare shakar kamshin turarenta? inji cewar malik yana me tuntsurewa da wata uwar dry.
Wani tsakin fu’ad yaja “kanka ake ji, ga diary din nan a hannunka kayi duk abinda zakayi dashi ,sannan kayi kok’arin ya isa gareta a duk sanda kaje gabatar mata da kanka ,ina maka fatan alkhairi tare da samun soyayyarta …