YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 11 to 20

“Dan Allah abokina, da gaske ,da gaske addu’ar samun nasara kamin? yakarasa mgnr yana me karasowa zuwa inda fu’ad ke kwance ya rike hannuwansa duka cikin nasa “na…gode abokina amman tare zamuje gidansu tunda ga addresse dinta acikin diary..?

“a’a kaje kai kad’ai ,hallo dai ina maka fatan samun nasara akanta sannan ya meida idanunsa ya runtse ya cire hannunwasa cikin na malik yana dafe goshinsa da hannunsa daya.

malik yayi saurin boye dryrsa sannan ya mike tamkar wanda akayiwa wanka da ruwan tsanyi ya isa makwancinsa “wannan shine karo na farko daya ganshi cikin damuwa hk, yammata dayawa suna kawo masa farmaki amman babu wace yaga tsan tsan damuwarsa akanta kmr me’ad, ayau suka soma ganinta amman da dukkanin alamu ta tafi da zuciyar abokinsa, ya kwanta yana dryr mugunta, domin a zahirin gsky shi ba son me’ad yake ba, amman ganin fu’ad yana neman waskewa akan sonta, yasa shi son shiga rayuwarsa tunda daman sukanyiwa junansu hk shi dasu kabeer , daga baya komai ya daidaita, Amman banda fu’ad da duk macen data kawo masa hari baya yarda ya amincewa soyayyarta ,acewarsa ba soyayya ce agabansa ba, yadda zai samu aikin da zai kula da kakarsa yake .

“itama bangaren me’ad kasa runtsawa tayi duk ta inda ta juya fu’ad take gani acikin kwayar idanunta,wani irin canji take ji a gabadaya ilahirin jikinta, ahankali take jin feeling’s na bijirowa gangar jikinta wanda wannan shine lokacin na farko dataji hk ajikinta, domin duk yadda sajida ke bata labari akan yanayi makamancin hk, bata ta’ba yarda ba, ta d’auki lamarin amatsayin shirme, ashe ba shirme bane da gaske ne?” mutun kanji wannan yanayi ajikinsa idan ya had’u da abinda yake so…

    kudundune jikinta guri daya tayi acikin bargonta, tana kok’arin basar da abinda take ji yana tafiya da bugun zuciyarta ,wanda a zahirin gasky mamaki faruwar hkn ya soma kamata, a kallo daya komai ba neman birkice mata……. da kyar da taimakon bacci barawo tasamu tayi bacci. 

Abu fa kmr wasa kullun me’ad sai fita zaga gari ko Allah zai sa ta had’u da fu’ad amman shiru ka keji ,har kusan sati daya , tana garari agari. yadda take zariyar neman fu’ad, haka malik ke zariyar nemanta domin bata diary dinta dake d’auke dakatin ATM dinta ,da kyar ya samu shigowa cikin estate dinsu ya isa bakin tafkeken get din gidansu da’aka nuna masa, yasamu daya daga cikin masu gadi gidan bayan ya gaishesa ,me gadi ya amsa yana masa wani irin kallo sannan yace” wa kake nema? 

“dan Allah ina neman me’ad.

Me gadin yayi shiru kawai yana duban malik daga samansa har kasa, ba dan yana da wata makusa ba ajikinsa, sai na talauci da babu daya nuna ajikinsa, me gadi ya sake maimaita tmbyr da malik yayi “kace kana neman me’ad ko me?

malik ya d’aga masa kai ala’mun eh. 

“Ita me’ad din tasan da zuwanka ?   

“Aa amman idan kashiga kace mata wanda suka had’u agurin injin din ci…

“Dakata anan da shirmenka, sannan ka juya ka ‘bace daga gurin nan , daganika irin yan yunwan nan ne, jobless marasa aikin yi,” kaga yarinya yar babban gida shine ka lallabo ko? “oya maza ka ‘bace tun kafin ita kanta tasan da zuwanka kasha dukan banza.

Batare da mutsu ba jiki a sabule malik ya bar unguwar tamkar wanda kwai ya fashewa acikin yana mamakin girman al’amarin, sai dai kullun zai zo amman baya samun ganinta hk zai juya ya koma da diary dinta , inda fu’ad ya d’auki zafi sosai dashi “kana wahalar da kanka abanza daga karshe ka had’u da wulakaci . 

“ka fahimceni fu’ad Allah ba wai ..”dakata malam kaje kacigaba da bibiyarta rayuwarka ce, abinda zai min ciwo bai wuce naga ko naji kace an wulak’anta ka ba, yana karasa mgnr ya fice daga d’akin yana huci. Malik ya girgiza kansa ,tabbas ya fahimci irin son da abokinsa kewa me’ad amman ya dakewa zuciyarsa, shi zai yi iya kokarinsa yaga ya had’a ruhinsu guri daya….

*******

Yau takama litinin wanda kowa yake sauri ya shirya ya samu halatar makaranta da wuri ,ko neman aiki da sauransu , ita kuwa me’ad tana gado tana juyin da tunanin fu’ad dinta ,har kafe tara sannan ta tashi tasa aka had’a mata ruwan,tayi wanka ,nan ma sai da ta’ba lokacin gurin tunaninsa ganin take kmr yana tare daita, duk inda ta juya shi take gani har mafarkinsa take, suna rayuwar aure tare.

ahankali ta fito daga bathoorom gurin shiryawa ma sai data bata tsawon lokaci ta fito ta karya sannan takama hanya dan zuwa bank domin amsar sabon ATM. 

 tun da ta cusa hancin motarta cikin harabar zenieth bank ta sauya yanayin tukinta tayi parking sai dai tajima acikin motar saboda ganin kmr mutane sun yi yawa kafin daga baya ta fito, tana taku ahankali da rangwad’a tashiga .

kai tsaye gurin costume’s care ta nufa , somi itace wace jinisu ya had’u daita sosai, somi na ganin me’ad ta sakar mata murmushi tare da cewa”me’ad you are welcome hade da tmbayarta abinda ke tafe daita, cikin harshen tsadadden turancinta tasoma mata bayanin abinda tazo yi, hannunta ta zura karkashin table ta zaro wani file ta mika mata tare da nuna mata wani madaidaicin office da hannunta “ki shiga can ki cike sai kawo min.

“okay me’ad ta furta sannan ta amshi file din ,cikin mintuna kad’an ta cike ta fito “ta mika mata batare da ‘bata lokaci ba akayi mata komai akace taje ATM ta canza pin dinta tare da mika mata envelop ,cike da rausaya ta nufi injin cire kudi bata wani canza pin dinta ba, ainhin pin dinta na da 5996 ta sake sakawa sannan ta kama gabanta wanda dayawa mutanen dake tsaye agurin hankalisu na kanta. 

Yau ma kmr kullun tana fita malik yazo gidan sai dai me gadin bai bi ta kansa ba ,saboda kallon wani mahaukaci dayake masa har sanda ta sanyo hancin motarta, ana kok’arin bud’e mata get shi kuma yana kok’arin isa inda motarta take, sauran security suka dakatar dashi, dan wani har ya kai masa mari ya goce da sauri. 

Me’ad ta bishi da wani irin kallon sani ,sannan ta kusa hancin motarta cikin gida tayi parking , ta fito tana gyara zaman glass din dake manne da idanunta ,ta kira daya daga cikin masu kula da bakin get “waye wancan mutumin da kuke dambe dashi kan sai ya iso gareni? 

sai da obi yayi jim..

 sannan yace “wai gurinki yazo yau akalla ya kai sati kenan yana zuwa ” what? ta furta arazane sannan tace. 

“how dare him yazo gurina akan wani dalili ?

“hk dai yace ranki ya dade. 

“Karku sake ku bashi damar sake shigowa estate din nan ballanata har ya iso bakin get din gidan”yes ma .

ta juya zuwa cikin gida tana tunanin inda tasan fuska amman sam ta kasa tunawa.

obi ya juya cikin sauri ya isa ga malik yasoma tura keyarsa “dan Allah ka saura ni abunta nazo kawo mata data yar bawani abu nazo nemana gurinta ba, amman ina sam obi yaki sauraransa har sai da kai ga fitar dashi gbdy daga estate din. 

*******

tafe suke ita da sajida a Shopprit domin siyaya wa mahafinta dake jinyar hannunsa agida,kuma a yau din nan suke expecting dawowar abbansu me’ad daga kasar America wanda yaje cheek up , ahankali suke takawa kmr basu san taka k’asa me’ad na sake bawa sajida labarin fu’ad sannan suna daukar duk wani abun amfanin daya kai su bayan sun gama sukaje inda ake biyan kudi me’ad ta bada ATM dinta, suna daf da fitowa suka had’u da Malik cikin saurin yake binsu yana kiran sunanta” me’ad me’ad!! me’ad ta juyo tana ganinsa tayi saurin kawar da fuskarta tacigaba da tafiya “kai kawata wannan mutumin fa ke yake kira.. ki tsaya mana da ala’mun yasanki “baki da hankali aganni na tsaya da wannan ai sai mutane su raina da ajina . 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button