YANCIN KI Page 11 to 20

biyota malik yayi” dan Allah ki tsaya abunki zan baki. da sauri taja hannun sajida ,haba me’ad ki tsaya mana wulakanci bashi da amfani balle d’an adam daraja garesa “bawani abun fad’a anan kawata , wancan banza nema yake na kulashi ,ni km ina i can’t suka shiga motarsu cikin sauri suka bar gurin kafin malik yakaraso.
“okay mubar zancesa cigaba da gaya min labarin kyawawa nan , ko shima kmr sauran samari gari yake ?
birki taja sakamakon gitawar da wani me okada yayi ta gabanta.
ta Leko da kanta cikin bacin “kai ina zakaje kake sauri hk?
” jiki da wata banzar mgn kisawa motarki alamar koya tuki Dan da alamun baki kware ba .
” kai koya min tuki zakayi ko me ?
“Kina bukatar hkn ai.
“kutumar uban can… “kinga malama duk abinda za’a yi ayi ammam ban da zagin iyaye yar rainin hankali kawai, ko dan kinganki cikin wannan kememiyar motar kike tunanin zaki zageni na kyaleki?
sajida ce tayi masa alamun ya wuce kawai tare da cewa “kinga manta da wannan ” kibani labarin kyakyawan saurayin nan da kuka had’u last week wallahi ina jin dadin yadda kike fassalta shi, me’ad tayi shiru ta kasa cewa komai ,kafin daga baya ta furta sunansa “fu’ad kenan ….
“suna me dadi tunda kike furta min sunasa naji sunan har cikin raina inji cewar sajida “Allah ko ai sai ma kinganshi kawata hadadden gaye aji farko zance fu’ad suke har suka shigo harabar gidansu sajida inda suka iske motar gidansu me’ad”kai kinga da ala’mun dady Dina ya sauka? Cikin sauri suka fito hannunwasu rike da farar laylon.
Da dariya suka shigo parlour ,n inda suka iske mahaifin sajida da nata zaune suna tautaunawa akan abinda ya faru ” ai ina gaya maka Aliyu tabbas zakasamu k’arin girma nan ba da jimawa ba akan wannan kokarin naka,mead takarasa kusa da mahaifinta ta rungumeshi “dady sannu da zuwa.
“yauwa yar baba fatan kina lfy?
“ina lfy amman ba lau ba takarasa mgnr tana nufar mahaifin sajida “gashi uncle “ka gwada wannan kaji yana da dadi sosai .
” yar baba aliyu ya gaya min cewa tsalake rijiya kikeyi a wajen harbe harben da’akayi? batare data juyo ba tace “eh baba amman babu abinda yasameni ,uncle ka fa zama jarumi a gari “kalli can kagani ta nuna masa tv da yatsan hannuta, kowani gidan talbijan kai suke nunawa tun daga last Week har yau din nan sajida ta zauna kusa da mahaifinta tana gyara masa zaman bandage dake d’aure da hannunsa.
Mahaifin me’ad ya gyara zamansa tare da cewa ” yar baba kawo min coffee mara madara “okay dad.
“uhm yar baba nima ki kawo min, me’ad ta nufi hanyar kitchen tana karasa shiga ta ja ta tsaya tana kiran “sajida ……..
“na’am.
“a ina kika ajiye sugar?
takarasa mgnr tana kallon wasu jerin robobi dake ajiye a kitchen cabinet ,acp ya bata amsa daga zaune dayake ” ai in dai wannan yar zaki tambaya ,to kuwa kin saba lamba.
sajida ta kaiwa babanta naushi a dayan hannunsa mara ciwo tana dry “kai baba “kai baba ko gsky na fada? ” ko sau daya bata ta’ba shiga kitchen din nan da sunan d’aura wani abu ba, bari nazo na d’auko miki yakarasa mgnr yana me mikewa tsaye “me’ad….. sajida takirata tana murmushi nima kizo min da coffee da k’arin sugar kinji kawata.
” hmmm yarinyar idan zaki koyi had’a shayi Da kanki , ki tsaya ki koya ko Dan aure da zakiyi watan gobe “ni imran din ma nake tausayi inji cewar acp “in tambayeki yar baba, waye wancen yaron dana samun labarin yana xuwa gurinki kullun bayan ga maganar safwan da’aka ajiye “uhmmmm wannan Shashan , ai kwana hudu data wuce na fara ganinsa ban san inda yasan ni ba amman har sunana ya sani abun tsoro .
“uhmmm?
” uhmmm uncle nifa abun ya fara damuna yau ma sai da muka had’u dashi a shopping, acp ya juya zai bar kitchen din fuskarsa da ala’mun rashin yarda “uncle kar ka fahimceni ba daidai ba “ai shikenan yar baba na fahimceki ….
********
tsaye suke su duka acikin had’ad’d’en boutique dake depomu wanda yakasance mallakin mahaifin kabeer ne .wasu yammata ne su biyu suka shigo cikin harabar gurin, kowace sanye da riga iya cinyarta wanda ke nuni da yare ne, makale da yar karamar jaka suna tautaunawa, kabeer dake tsaye kusa da malik yana dan kurban fiver alive “yace kumeless tare da binsu da wani shu’umin kallo malik yayi saurin juyawa shima ya bisu da kallo ,sannan ya juyo ya kalli fu’ad yana dage masa gira kana ya sake juyowa ga kabeer “idan kabiyi wad’an yammanta kai ka zasuyi su baro ,duk bugi ne wallahi ina gaya maka. “kai dan Allah banason shirme ka juya ka kalleshi da kyau gsky sun hadu inji cewar kabeer.
Malik ya sake juyowa ahankali yana kare musu kallon tsab sannan yace “uhmmmmm wad’an yammanta lagos din suna da tsabagen wayo tsiya ,su sha kwaliya su dinga maganganu irin na birgewa, amman duk fanko suke,ya dan sake kallon inda fu’ad yake sannan yacigaba “daya nagani acikinsu me nagarta da kamalar madarar kyau …… sudais yayi saurin cewa “da gaske ?
“yace uhm.
“kallesu da kyau kagani duk kwaliya ce kawai “yanzu kayi kok’arin kallonsu batare da kwaliya ba kagani .
“kamar yaya kenan? inji cewar kabeer .
“ka aiyana da tunaninka mana ..
“kai dan Allah banason shashanci da ala’mun fa kwal’kwaluwarka tasoma samun matsala inji cewer kabee .
“kai ne dai mahaukaci amman ni nasan abinda nake duk da cewar akwai yammata dayawa amman me’ad dina ta zarce kowa yakarasa maganar yana ware hannunwansa duka..
“kaji mahaukaci suka kwashe da dry “matar da jiya jiyan nan tagama shuka maka rashin mutunci, wai har da wani cewa me’ad dinsa suka sake kwashe da dry suna nunashi .
fu’ad dake tsaye rungume da hannuwansa duka a kirji bai kulasu ba illa fuskantar kofar shigowar dayayi tare da takaicin malik, aiko tamkar a mafarki yaga shigowarta sanyi cikin doguwar rigar abaya har kasa ta nad’e kanta da mayafin abayar hannunta rike da karamar jaka saurin runtse idanunsa yayi yana cigaba da kallonta ahankali ya mutsutsuka idanunsa” itace ko kuwa wata ce me kama daita ,tabbatar da itace yasashi saurin waskewa alokacin da suka had’a ido daita itama kallonsa ta tsaya yi cike da matsanancin mamaki ta mutsumutsuke idanunta tagani ko shaukin sonshi ne yasata ganin hk oho.
muryarta a sanyaye tace “sajida ga fu’ad dina tare da nuna mashi, tsura masa ido sajida tayi, lokaci daya numfashinta ya nemi d’aukewa ganin halitar da bata ta’ba ganin irinta ba, tana ganin kyawun imran wanda zata aura amman na fu’ad ya zarta nashi,kad’an kad’an taoma jin tsigar jikinta na tashi abinda ta kasa fassalta ma’anarsa, wani irin sanyi soyayyarsa ne ya tsarga mata ya fara bin ilahirin jikinta, take ta lumshe idanunta zuciyarta na wani irin harbawa da sauri sauri, gbdy ta kasa d’auke idanunta akanshi har sanda ya juya musu baya.
shi kuwa malik na ganinta yasoma murmushin tamkar wanda akayiwa bushara da gidan aljanna sannan yace “kai kabeer sudais itace fa gata can yarinyar nan wallahi itace ..me’ad najin hk tayi saurin riko hannun sajida “kinga wanda na nuna miki?
“uhmm sajida ta iya cewa still idanunta na kan fu’ad “wance dake sanye da kaya shine fu’ad dina amman zo mubar nan yanzu yanzu saboda banason wancan mahaukacin ya dagula min lisafi ,sai yanzu na tina shi, ranar da muka hadu da fu’ad suna tare sai dai bansani ba taren suke ko kuwa anan suka had’u, wanda nake so daban shi kuma yana kokarin hanani rawar gaban hantsi .