YANCIN KI Page 11 to 20

ahankali take daga kafafunta har zuwa office din alhj Ibrahim wanda yake shugaba ga maikatan kuma aminin mahaifinta, bayan sun gaisa ya tambayeta lafiyar mutanen gidansu, tace “duk lfy atakaice sannan akabata aiki wanda zata dinga daukar albashi me tsoka batare da wani interview ..kusan minti biyar tana zaune alhj ibrahim ya d’ago yana dubanta sannan yace “ko akwai wani abu ne, shiru tayi na minti biyu kana tace akwai “ina sauraronki ya fad’a tare da meida idanunsa kan tarin takardu dake gabansa “akwai wani danake son ka taimakawa kabashi aiki a ma’aikatar nan.
“yana ina?
” shine kika tsaya jan maganar abinda zaki fad’a da confidence ai ba mutun daya ba diyata ko mutun goma kike son a d’auka za’a d’auka masengen sa ta aika yaje ya shigo da fu’ad, wanda shigowarsa yayi daidai da tashin da alhj ibrahim yayi, yakaraso shigowa sanye da suit da bakin glass frada a idanunsa take office din ya gauraya da kamshin turarensa kafafunsa rufe cikin cover shoe baki ,taja masa kujera tana nuna masa gurin zama amman yaki zama “ka zauna zaka samu aiki karkashin jagorancina matukar shi kazo neman ,idan kuma kaki zaka karad’e garin nan batare da kasamu aiki ba saboda mu ‘yan alfarma gama maganarta keda wuya ya juya kawai batare yace mata ko uffan ba, ta mike da sauri tabi bayansa tana kiran sunansa “fu’ad ka tsaya zan saka abaka aiki me mahimmaci .
amman ina ko juyowa baiyi ba har ya isa inda sudais ke tsaye yana jiransa ya rike hannunsa “zo mu wuce kawai ya iya furtawa “ka tsaya mana bakaji tana kiranka bane ?
kana ji fa taimakonmu zatayi “banason duk wani taimako daga gareta kazo muje kawai idan km baxaka ba na wuce…. ya fixge hannunsa cikin nasa “to bazani ba shekara nawa ina neman aikin bansamu ba yau zamu samu amman kake girman kan banza …
fu’ad ba tsaya ba ballanatana ya juyo gareta yacigaba da tafiyarsa shi kuma sudais yakarasa gareta “ranki ya dad’e kiyi hakuri hk halinsa yake, shegen girman kan tsiya shi ba… “dakata karka soma furta kalmar ‘batanci garesa, daya tsaya har kAi zaka iya cin albarkansa tana karasa fad’ar hk ta juya fuuuuuu zuwa inda tayi parking din motarta ta figa aguje, mutane kuwa sai zagin fu’ad suke akan wasa da damarsa da yayi.
tana barin oil and gas kai coffter coffe ta zarce inda suka saba had’uwa da sajida ,dukkaninsu shiru sukayi suna kallon junansu bayan labarin da me’ad tabata akan abinda ya faru atsakaninta da fu’ad. “me zai hana ki hakura dashi, tunda yaki saurararki.
“i can’t sajida ina son shi bansan ina son shi ba sai yau dana yi masa kallon gani ga shi, ni dai ki tayani adduar samun shi kawai dan matsawar ban auresa ba sai dai na mutu babu aure ..
“all the same inji cewar sajida “what?
“no babu komai suka cigaba da zance fu’ad batare da sun kai coffen da’aka kawo musu bakinsu ba tsawon lokaci suna zantawa sannan suka mike atare daga nan gidansu sajida suka nufa ,trafic ya kamasu suka tsaya inda malik shima yana d’ayan gefen hagu bai lura dasu ba sai danja tabasu damar wucewa sannan ya gansu, nan fa yashiga binsu akan lefan dinsa .
kmr ance sajida ta kalli mudubin gefenta ta hangosa yana daga musu hannu, leko da kanta tayi domim tabbatar dashi din ne “me ad duba madubin gefenki kiga wannan d’an jagaliyar fa mu yake bi inji cewar sajida “kai dan Allah tayi mgnr tana dubawa ,”tabbas mu yake bi amman nasan yadda zanyi maganinsa k’ararsa zan kai gurin uncle ya jefa min shi cikin magark’ama ayi masa dukan tsiya haba dai ke kuwa kamar shi yace kar fu’ad yasoki takarasa mgnr tana dry a daidai lokacin da suka iso kofar gidansu sajida shims yaja ya tsaya tare da parking din mashin dinsa suna fitowa daga cikin motar ya iso garesu yana cewa jimana me’ad. nasan kinsani amman kike pretending kamar bakisani ba …dau dau ta d’auke shi da mari “how dare you calling my name? yayi saurin dafe kuncinsa yana kallonta.
“me ma yasa kake bina? “kasan ko ni wacece?
“dan jagaliya irinka kake bibiyata “waye ubanka a duk fad’in garin nan ?
jiki a sanyaye yace” daman bawani abu bane amman idan baki tunani ba, ni ne malik wanda muka had’u agurin ciro kudi ..
“and so what?
“jibeka kawai wani wawa dashi ,ko iya fitar da maganar bai iya ba,da muka had’u sai akayi yaya?
“daman kin yar da diary dinki ne shine fa na amsa gurin abokina fu’ad dan nasan shi ba bazai ta’ba biyoki domin yabaki ba ,shi nake ta ajiyarsa kullun ina son nabaki amman bakya saurarata..
“inna ilaihi wa inna ilaihi rajiun ta furta acikin zuciyarta ………..idanunta a kansa
mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 49 to 50
….kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu duka uku sajida me’ad malik, shiru me’ad tayi tana kallonsa batare da ta sake yunkurin cewa dashi komai ba ,sai dai gabadaya nadama tattare da kunyar abinda tayi masa a yanzu ya kamata tare da raunata wani shashi na gangar jikinta,” ta wulakanta mafi kusanci ga zuciyarta bisa ga mummunar d’abi’arta….”me yasa tayi saurin marinsa?
“why why why!!! me’ad?
“why did you slap him..?
tana nan tsaye jikinta na rawa har malik yakaraso zuwa inda take tsaye jikinta nacigaba da kyarma ya miko mata diary dinta ……nadama ce fal dankare da zuciyarta “hakika ta cuci kanta ta cuci rayuwarta ba zata ta’ba yafewa kanta abinda ta aikata masa ba matsawar yayi silar rasa fu’ad dinta…..”ki amsa ko nabawa kawarki ne?
jin sautin mgnrsa yasa tayi saurin dawowa cikin haiyacinta domin natsuwar tasoma barin gangar jikinta, kallo daya zaka mata kagane kalar damuwar datake ciki.
sai daya sake mgn sannan jiki a sanyaye tasanya hannuta ta amshi diary dinta, shi kuma ya juya tamkar wanda kwai ya fashewa aciki yasoma tafiya , har ya kai gurin mashin dinsa yana shirin hawa yaji sautin muryarta ahankali “tsaya dan Allah sannan tasoma kok’arin takowa zuwa inda yake, jikinta a matukar sanyaye .
muryarta na rawa tace “dan…dan girman Allah kayi hakuri ta furta hkn tana mai runtse idanunta kasancewar wannan shine Karo na farko data bai wa wani mutun hakuri ,bayan iyayenta da suka kawota duniya “kayi hakuri ta sake maimaita kalmar muryata a raunane tare da bud’e idanunta fess akansa tana kallon yanayinsa da gbdy ya sauya, a yanzu dayake gabanta ganin take tamkar fu’ad dinta ne tsaye a gabanta cikin matsanancin damuwa , “hakika nayi abinda bai dace ba ,da rashin kamata gareka,
tun ranar farko dana soma ganinka a gidanmu nayi tunanin kmr nasan fuskarka amman alokacin na kasa tuna inda nasanka, sannan lokacin dana ganka tare da fu’ad a boutiq shima ban tantance alakarku dashi ba amman dai kayi hkr dan Allah.
” babu komai ,komai ya wuce Allah ya kiyaye na gaba, hk daman rayuwar take ,da nabi shawarar fu’ad da ban jawo wa kaina wulakanci ba, domin babu abinda ya kai wulakanci kmr a tsinkaka ta hanyar mari….. …amman babu komai “me’ad yakira sunanta ,nasan kina mutuwar son abokina fu’ad duba ga yanayin nadamarki bayan kinsa alakata dashi, amman shi mutun ne me matukar kamewa ,kai tsaye hk bazai ta’ba fuskantarki ba ….
“nasani ….nasan da haka amman ko zaka iya taimaka min plz takarasa mgnr muryarta na craking ?