YANCIN KI Page 11 to 20

domin zan iya yin komai akansa ,”da fari dai ka taimaka min da number wayarsa tare da sake bashi hakuri.
“sajida plz ki matso kusa mana ki bashi hakuri kema bawai ki wani ja kin tsaya kina kallonmu ba.
“me zance masa me’ad?
“me kike son nace masa after kingama aikata son ranki ?
“i think kin bashi hakurin kuma yace ya hakura.
“eh amman ni dai kice masa wani abu dan Allah har yanzu akwai damuwa a tattare da shi.
“dole kuwa kiga damuwa atare dashi me’ad , bashi ba koni kika karewa kallo zakiga ala’mun hk atare dani “ta yaya daga ambatar sunanki zaki maresa?
” tun ranar farko daya kira sunanki na gaya miki definitely wannan mutumin yasanki wani guri amman kika nuna min sam ba hk bane yanzu wa gari ya waya?
” komai sai kin saka zafin rai aciki, sosai sajida tayi mata fad’a ta inda take shiga bata nan take fita ba har sai da malik ya nuna abar zance ya isa hk “kuma har ga Allah komai ya wuce daga karshe ya karanto mata number fu’ad bayan tayi tsore, tace yabata nashi yabata sannan ya wuce .
” a she dai mutumin kirki ne nake masa wani irin kallo ta furta hkn tana kallon bayansa .. …….
juyawa sukayi zuwa cikin gidan suna shiga d’akin sajida tasoma neman layinsa amman kiran duniya tayi bai d’auka ba haka takarar da wunin ranar akan kiran layinsa bai d’auka ba.
shi kuwa malik a sanyaye ya karaso gida, duk da har cikin zuciyarsa yana jin abinda me’ad tayi masa ya wuce, amman gangar jikinsa takasa hakurin hk, ganin yanayinsa yasa sudais dake bawa kabeer labarin abinda ya faru a oil and gas a safiyar yau din nan ya karaso gurinsa yana tmbyrsa, shima kabeer yazo ya tsaya dayan gefensa “lafiyarka malik?
” me yasameka duk ka dawo wani iri hk? yayi masa tmbyr ajere. naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da gaya musu abinda ya faru har zuwa Number wayar fu’ad daya bata, dan basa boyewa junansu komai, daga karshe yace “karsu sanarwa fu’ad saboda ya sha ja masa kunne da gargadin abinda zai je yazo .
abinda malik bai sani ba gbdy mgnrsa acikin kunnesa yayita,wanda take ran fu’ad ya ‘baci zuciyarsa tazo har wuya tana tafarfasa sai dai ya kudirici aniyar zai ganar daita kurenta ta hanyar tarkonsa data fad’a .
sai gurin tara na dare me’ad ta sake gwada kiransa da dayan layinta, bugu biyu ya d’auka cikin dakakkiyar muryarsa duk da bai san ko number waye ba, “hello….. ji tayi tamkar an mata bushara da gidan aljanna ne dan dadi, lokacin dataji sautin muryarsa ta ratsa cikin dodon kunneta, tayi sallama cikin sanyayyiyar muryarta amadadin “hello din daya ce mata, ,” daga can bangarensa yayi shiru kawai yana sauraran yaji ko waye duk da zuciyarsa ta soma gano masa ko wace saboda sautin muryar mace dayaji, ita km hucin Numashinsa dake fita ta cikin wayar ne yayi nasarar kashe mata ilahirin jikinta har yasa ta kasa mgn, jin shirun yayi yawa ne yasa shi cewa “waye yake kok’arin shiga cikin lokacin hutuna?
murmushin fariciki tayi gefe daya kuma hawaye ya cika kwarnin idanunta sakamakon sake jin sautinsa a hassale , sai da ta sake kwantar da muryarta sosai sannan tace “me’ad ce.
“wace hk?
jin abinda yace ya sata mikewa zaune daga kwance datake “uhmm ammm dan Allah karka ce baka ganeni ba, gurin abokinka malik na amshi numberka ?
“kit taji ya katse kiran ta sake kiransa back bai d’auka ba daga karshe taji ya kashe wayar gbdy ranar dai kwanan zaune me’ad tayi ,duk inda ta juya fuskarsa take gani da komai nashi bata ta’ba tunanin zata fad’a tarkon d’a nmj irin hk ba. washegari bata tashi da wuri ba saboda rashin baccin dabata samu yi daren jiya ba. sai gurin 12 ta tashi tashiga wanka.
ta sake neman layinsa da wata number daban yana d’auka tace “barka dai me’ad ce take magana …kit taji ya katse kiran wani irin sarere tayi agurin ahankali tayi kasa ta zauna akan gadonta sai ga hawaye yasoma ciccikowa a idanunta ta tsurawa wayar ido tana kallo gani take kmr shine acikin wayar.
wani tunani tayi ,zuciyarta ke umartata data kira number malik, take batayi sanya a gwiwa ba tashiga neman layinsa, bayan ya ta sake bashi hakuri akan abinda ya faru sannan ta d’aura da damuwarta “hakuri yabata Inshaallahu zan masa mgn. “ok nagode sosai sai kaji kirana ta katse kiran shi km ya sauke idanunsa akan fu’ad dake tsaye yana shirin zuwa gurin inna kakarsa “fu’ad yakira sunansa.. ya d’ago kansa tare sauke kyawawan idanunsa akansa batare da yace komai ba “dan Allah saurari yarinyar nan ,ka duba kaga yadda ta ajiye jin kanta, gadara takama da komai nata akanka …
“an so what?
“na aiketa ko nasata?
“kai nifa banida lokacinta yakarasa shirinsa tare da barin d’akin ..misalin karfe 11 :00 na dare kiranta yashigo cikin wayar malik ya d’auka dan lokacin idonsa biyu yana kallon ball tare da su kabeer fu’ad ne dai ke kwance har yasoma bacci ,gaisawa sukayi sama sama “dan Allah malik ka had’ani da fu’ad “ok ya mike tsaye yayinda su kabeer suka bishi da wani irin kallo har yakarasa inda fu’ad ke kwance ya manna wayar a tsaitin kunnenshi ,sautin muryarta yasashi bude idanunsa ahankali yana duban malik dayayi saurin had’e hannuwansa guri daya yana rokonsa daya saurarera. lumshe ido kawai yayi batare da yace komai ba yaji ta sake mgn “fu’ad… dan Allah kayi hakuri da kiran danayi adaidai lokacin nan dole ce tasa hk gbdy na kasa runtsawa.. lip’s dinsa ya ciza da k’arfi kmr zai huda, sannan ya kamkame jikinsa guri daya sakamakon jin muryarta, kai bazai iya cigaba da sauraronta ba, saboda zai iya shiga wani yanayi a dalilin jin muryarta da kuma ya birkita masa lisafi idanunsa ya rufe gam yana kawar da tunaninta tare da tunanin hanyar da zai bi ya musguna kmr yadda ta wulakanta malik….. “ina son mu had’u da kai gobe a coster coffee domin akwai bayanai masu matukar mahimmanci danake son mu tautauna da kai “gud dama tasamu ya furta acikin zuciyarsa, wanda a zahirance cewa yayi “okay.
“nagode sai mun hadu gobe karfe biyar na yamma ya katse kiran batare daya tanka ba.
bai je kmr yadda ta bukata sai dai shi yana tabbacin taje tagama tsamanin ganinsa ta wuce sai bayan kwana biyu malik ya matsa akan zance,sannan suka had’u a coster coffee dake awolowo waya gabadaya ta rame fuskarta tayi fayat kallo daya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta da hankalinta tsawon minti talatin tana tsaye kmr ance ta juya taganshi sanye cikin riga green me adon pinky a gabanta, gashin kansa a gyare sai sheki yake” kallo kallo sukewa juna kafin daga bisani ya runtse idanunsa tare da zube hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa muryata na rawa tace “ammmmm uhmmm sannu da zuwa gsky ka ..kayi kyau ..wannan ce maganarki mafi tsada ?ya fad’a tare da meida idanunsa ya runtse .
“eh but ta mika masa karamar flower ga wannan kai na kawowa ,dan girman allah ka amsa koda kuwa bazaka amshi tayin abinda nazo maka dashi ba.
a banzace ya kawar da flowers yasamu guri ya zauna yana juya mata baya zagayowa tayi ta zauna ta gabansa tana fuskantarsa “me zaka sha ice cream coffe ko shayi da madara?
“da kyar ya fizgo numfashi kmr zaiyi mgn sai kuma ya fasa .
Zuciyartace tayi tunanin watakilla zai bukaci coffee
Dan hk take tabawa masu kula da gurin umarnin akawo masa coffee ta meida idanunta a kanshi tana satar kallonsa juyar da kanshi gefe yayi kmr baisan me takeyi ba tare da datse lip’s dinsa ….