YANCIN KI Page 21 to 30

“na d’auki diyar dana fi so na aurawa ga wanda gabadaya rayuwarsa sipili ce a tunaninka hkn zai yiwu?
fu’ad da kansa ke sunkuye ya dago a matukar firgice yana duban dady kamin yayi magana dady yace “ysushe kasan me’ad? “karkari tsawon wata shida.
ran fu’ad ya sake kaiwa kololuwa gurin tashi ganin ga safwan zaune amman yaki takawa dady burki gashi dady bashi alamun saida zancesa hkn kuma still safwan na kallonsa A wulakance yana masa murmushin da bai san ko na mene ba, ya bude bakinsa da kyar yace “yallabai ni dai nasan idan kabani auren yarinyaka zansata farinciki “me kake bukata atare da mutun adali ince na natsuwa nagarta mai kamun kai mara shaye2, to duk ina cikin abinda na lisafa maka, ince duka matsalar akan ta rashin aikin yi ce? “ka zuba ido kagani nan gaba da kayan aiki zakaganni ,zan tabbatar maka da kai.. “meye abun tabbatarwa yaro byn gaka agabana da shirman rayuwarka zaka tabvatar min da kanka ko me?
dady yakarasa mgnr yana murmushi safwan kaji fa, “wai shin wani shirin wasan kwaikwayo akeyi anan ne ko me?
“wai tabbatar da kansa yake son yi wa uban me’ad yakarasa mgnr yana dry “babban magana kenan “mai yawo a gari babu aiki yake son tabbatar da kansa shi dai safwan bai ce ta tafar ba illa dryr dayake ta kunshewa saboda gabadaya maganganun dady sun matukar yi masa dadi da sanyaya ransa.. “kasani diyata me’ad nada alkwarin auren wani akanta attajiri Wanda ya fika a komai na rayuwar duniya dan hk kwarya tabi kwarya a gidan baka da matar aure period mgn ta karshe kar na sake ganin kafarka gidana..
fu’ad yasoma kokarin mike tsaye “sai anjima yallabai nagode da lokacin daka bani wani irin kallon kaskanci dady yake binsa dashi yayinda har wannan lokacin fuskar safwan kumshe take da dryr mugunta.
jiki a sanyaye fu’ad yakarasa mikewa yana gyara rigarsa ta baya sannan yasoma daga kafafunsa kmr kazar da kwai ya fashewa aciki ya nufi inda yayi parking din machin din kabeer daya aro, ya hau ya zauna amman ya kasa tadashi sai dai ya kwantar da kansa kan mashin din, bai yi auni va sai jin danshi yayi akan fuskasa ya mika hannunsa ya shafo hawaye ne, shi kansa yayi makakin dalilin zubarsu akan mead ne da zai rasa ko kuma akan tozarcin daaka masa ne ?
yafi minti talatin a haka kamin yasoma kokarin tayar da machine ,masu gadi suka bude masa kofar get ya fita, ya yarda bazai samu me’ad ba har abada. shi ba aure yadamu dashi ba da wuri kasancewarsa saurayi da bai taba aure ba, km ba shashanci yake ba balle ya tancance yanada bukatar mace yanzu ko aa, me’ad din kawai yake so, soyayyarta ce tasanyasa son yin aure a halin yanzu.
meyasa mead tayi masa hk ?”me yasa ta boye masa akwai alkwarin auren wani akanta? tayi masa wasa da zuciya da hankali har ya iso gida bai san inda hankalinsa yake ba kuma tmbyr dayake son yayi mata kenan “hakika tayi masa wasa da zuciya, dan bazai iya cewar ta yaudaresa ba ,dan ya yarda da son datake masa na gaske ne, sannan na tsakani da Allah ..
Da yammacin ranar sai ga mead tazo gidansu sakamakon abinda safwan yagaya mata daya yayi masa, da kunneta km taji lokacin da safwan kebawa dady hkr da kokarin shawo kansa daya amince da auren albashi sai su tsaya masa yasamu aiki,inda ta lsamu fuad zaune kofar gidan inna ,yana kallon sararin samaniya, da yadda hadari ya hado agarin,a zahirin gsky zaka dauka yana nazarta yanayin zuwan ruwan saman ne, amman sam abun ba hk yake ba tunanin rayuwa yake, tunani yadda rayuwa take shirin tagaliliya dashi yake, har sanda takaraso garesa bai sani ba sai jin laulausar tafin hannuta yayi saman nashi, wanda hkn yasa shi juyowa ahankali tare da sauke naunayen ajiyar zuciya ganin itace ,sai dai ganinta ya zafafa mikin dake cikin zuciyarsa, atake ransa ya sake dugunzuma, ya cire hannunsa daga nata yana mai basarwa sannan muryarsa a dakile yace”mai ya kawo gareni?
“Dan Allah kibar nan tun raina bai gama dagulewa akanki , banason kusancina dake.”to saboda meye fu’ad? “Saboda kin kai ni ga mahaifinki ya tsarkafeni da sarkafaffun tmbayoyinsa marasa maana da tushe , ya bata amsa a matukar fusace yana mai maida idanunsa sama jin har ansoma yayyafi.
“karkayi wannan maganar fu’ad daman irin tambayar da iyaye sukayi kenan , kasa kanka amatsayin mahaifina ka duba Alamarin….dan Allah dan Annabi malam ya isa hk kawai kin gayuaceni zuwa gidanku dan aci mutuncina akaremin tanadi da tozarci ,shi kuma wannan tantirin safwan din yana zaune agurin yana min dariya “ka daina magana ta shirme mana safwan mutumin kirki ne karka tuhumaishi acikin wannan matsalar “oho ni kuma mutumin banza wanda bayada aikin yi, dan jagaliyar titi daya fada soyayya da yar babban gida, in da kace masu kudi kawai suke da alhakin da yancin fadawa soyayya ,da soyayya tayi karanci a duniya, fuad ka daina daga murya mana kana jawo hankali mutane garemu.
“Gara na daga sautin muryarta ansa kece kebibiyata har kikayi silar da yau aka tozartani, banki kowa yafito yasani ba, kece kika tallata min kanki akan soyayyarki ina zaman zamana cikin rufin asirin Allah “dan Allah karkayi magana cikin fushi har da kake wani shir…datse harshenta tayi da karfi takasa karasawa.
“.Kwarai kuwa dole kice hk tunda kina son kare gidanku da ahlinki, an wulakantani sam baki damu ba suna kina sona kin wani kwaso shirmen jikinki kinzo kina kara gaya min maganganu banza, sai danazo na fuskanci mahaifinki nagane irin kuskuren danayi ,ba dai aiki ba,to bazan nemanba ,km Zan aureki da rashin aikin nawa domin na tabbatarwa mahaifinki ko babu aiki zan iya kula dake yadda yakamata .
wai mgnr tawa ahlin gidanku suka meida abar dry, wanda wannnan abun daaka min ina da tabbacin safwan yana da hannu aciki kuma shine ya ziga babanki akan hk.
“Fu’ad ka daina magana hk mana, domin magana cikin fushi bashi da fa’ida, sannan ni ina da tabbacin babu ruwan safwan cikin wannan matsalar, “ai magana ce ta gsky idan tazo a fadeta baka da aikin yi, ko kana da? Ta jiho masa tambayar tana kallon cikin kwayar idanunsa wani irin kallo yayi mata ..
“Kuji wawiya da wata wawiyar magana ya furta hkn adaidai lokacin da ruwan sama ya sauko kmr da bakin kwarya,yacigaba “ai ban tabasanin cewar ke din shasha bace sai yau, tun farko da kika nacewa sona aikinsa bana aiki ko baki sani ba ? Shima yayi mata tmbyr yana tsare gira da kamewa “oho zuwa yanzu soyayya da mutuntakan dake tsakaninki da safwan zai iya sa ki mance hk ba..?
“Bari kiji nagaya miki abinda bakisani ba nasan komai tsakaninki da safwan, tundaga farko har karshe ko last week da kuka fita yawon celebrating din birthday dinki ina sane…nasan kunyi soyayya dashi …,a yanzu kuma yaudararki yake,da furuncin ya janye batun aurenki, kina sona zaki aureni amatsayin danake. .ki tabbatar da kin rabu da safwan rabuwa ta har abada, idan ba hk ba kisawa zuciyarki fu’ad ba rabonki bane na wata ne ,yana gama fadar hk ya juya yasoma daga kafafunsa.
jikinta na rawa tabiyo bayansa tana kiran sunansa fuad ka tsaya dan Allah …
Bai tsaya ba har sanda ta isa garesa ta riko hannunsa ya juyo a fusace yana dubanta “idan na tsaya na miki meye?”narigada nagama magana period sannan ki tsaya daga nan domin idan kikayi gangancin biyoni,har kikayi silar shigar innata damuwa zan miki abinda bakiyi expecting dinsa daga gareni ba.