YANCIN KI Page 21 to 30

juyowar nan da zaiyi yasanya hannuwansa ya goge fuskarsa sai yaga innarsa tsaye a bakin kofa tana kallonsu ,wacce tun da zu take tsaye agurin juyawa tayi cikin gidan, nan shima yashiga ya samu guri ya zauna agefen gadonta batare daya cire kayan jikinsa ba,inna dake sharar hawaye takaraso garesa ta dafa kafadarsa ahankali sannan tasanya dayan hanunta bisa kansa, inda gbdy ta fashe da wani irin kuka mai cin rai tare da rungume kansa a kirjinta shima kukan yake son yi amman ya dake.
***********
Yadda fu’ad ya kwana bai runtsa ba ,haka mead ta kwana juyi akan gadon ta,duk inda ya juya maganganun mahaifinta ke masa kuwa ya yarda ya amince ya saduda ya amince mead ta haramta garesa, soyayyarsu tazama mafarki mai dadi irin wanda dan adam kanyi, ya farka yana mai cizan yatsar kasancewarsa, tunda har mahaifinta yayi wannan hukuncin, dreams are conceived but not all dream ‘a are born alive some are aborted, others are stillborn ya juya ya kalli su jabeer baccinsu kawai suke cikin sukuni alamun basa cikin matsalar rayuwa sannan basu san menen kalmar da ake cewa so ba .
aganinsa babu masu saa aduniya kmr su ,tunda basu zuki gardi da dadin tattare da dacin dake cikin so baz gashi dai sun fisa rawar kai akomai amman basuyi gangancin sanya kansu cikin soyayya ba balle har tazo ta damesu tazame musu kmr cutar cancer, wanda abu ne dake yawo yayi can yayi nan tunda yana faruwa da zuciya ne kawai, amman daga baya sai ta kurda cikin kasusuwan mutun ta gyaraye koina bargo jijiya da jinin jiki har da gabadaya gangar jikin Dan Adam. wayarsa dake wuriri akarkashin pillow’NSA yasoma ruri ,tunin ya gane msi kiransa mead ce adaidai wannan lokacin yaki dauka hk tayi ta kararta tagaji “mai zata ce masa da zai fahimta?
Bazai sake yarda ta luguiguita masa zuciya ba, ya yarda ya amince tunda har mahaifinta yayi furuncinsa garesa bazai bashi auren yarinyarsa ba .
Ta kirasa yafi sau goma amman bai dauka, daga karshe ma yaka kashe wayar gabadaya ya kife kansa jikin pillow tare da lumshe ido cikin halin tausayin kansa, Dan ganinsa ita mead ba abar tausayi bace ….
Mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 63 to 64
……..Wannan ihun da karen ke yi babu kaukautawa ,yasa gabadaya jami’an tsaro dake harabar gurin, yi masa caa aka tare da saita bakin bindugunsu a daidai saitin kwalkwaluwasa suna mazurai da idanuwa tmkr zasu cinyesa .
nan take tsoro da matsanancin firgici ya bayyana a Kan fuskar fu’ad, ba iya zuciyarsa kad’ai ke rawa ba hatta gangar jikinsa kyarma yake, tsabar firgici da tashin hankalin daya tsincin kansa ciki a karon farko a rayuwarsa, sai zare manya idanunsa yake yana duban tarin jami’an tsaron dake zagaye dashi yake.
Kai tsaye jakar kayansa aka soma bincika , abin mamaki ana buɗewa sai ga cocaine , ba ƙaramin tashin hankali fu’ad ya sake tsintar kansa ciki ba ,zuciyarsa ta tsaya cak na wani lokaci ta daina bugawa ,kafin daga baya tasoma bugawa da karfi karfi kmr ana buga mata guduma , nan da nan aka yi arresting din shi, duk ƙoƙarin da yayi don nuna musu ba shida hannu a laifin da ake tuhumarsa dashi basu saurare shi ba, suka tasa keyarsa aka wuce da shi wajen Binciken manyan laifuka.
Tsaye yake agaban shugaban jami’an tsoro na jahar gbdy, hannuwansa duka goye abayansa, yana kallon mutumin dake gabansa kmr yadda shima yake kallonsa, tsawon minti goma sannan sir kola saraki ya d’auke idanunsa akansa yace ,”fu’ad sunanka ko?
Cikin sauri fu’ad yace “eh yallabai.
“Ka natsu ka kwantar da hankalinka ,yanzu ka gaya mana suwaye suka sakaka wannan aiki?
“ina mai tabbatar maka matsawar ka sanar mana da ko su waye suka saka ,zan sa a sakeka salin alin batare da wata damuwa ba .
“Wallahi wallahi!! yallabai bansan komai ba akan abinda ake tunhumata dashi ba ,salima ban san yadda akayi wannan rud’anin ya faru ba …
“Dakata malam ,karka mana karya mana, ko bakason ka tsairatar da rayuwarka ?”yimana karya daidai yake da salwantar da rayuwarka a gidan yari. ..
Cike da matsanancin tashin hankali fu’ad yace “wallahi ni dai babu wanda yasani ,sannan bansan lokacin da hodar ibils tazo cikin jakata ba,ka taimaka yallabai wallahi bansan komai ba yakarasa mgnr hawaye nabin kuncinsa……
Sir kola yayi shiru kawai yana kallonsa yana nazarinsa batare dayace masa komai ba ,tabbas alamomi sun suna kmr bashi da masaniya akan abinda ake tuhumarsa, amman kuma zai iya yiwuwa yakasance yana sane tare da sanya hannunsa ciki , Dan kusan mafi akasarin wad’an da ake kamawa da wannan laifin kowa haka yake cewa.
Kai tsaye sir kola yace a fita dashi, ana fita dashi d’akin horo akayi dashi ,aka shiga dukansa domin ya fad’i gsky Yin duniya akayi dashi Amman yace shi bai san komai ba ,Dan haka akayi magark’ama dashi, ranar sam bai runtsa ba ,tunanin duniya yayi akan lamarin Amman ya rasa ta inda wannan abu ya faru dashi..
*************
Bayan watanni uku da faruwar wannan al’amari, me’ad na xaune tana kallon labarai sai kawai ji tayi an ambaci sunan fu’ad tare da cewa ana tuhumarsa da babban laifin xuwa ƙasar England da hodar iblis, ba ƙaramin tashin hankali me’ad ta shiga ba, gaba daya ji tayi hankalinta na kokarin fita daga gangar jikinta ,saboda damuwa da halin da fu’ad ke ciki, ihu mai ƙarfi ta saki ta zube kasa sumammiya, bata tashi farkawa ba sai ganinta tayi a gadon momy ,tana tambayar ta
“Tunanin me kike yi haka me’ad kike so ki jefa Rayuwar ki cikin haɗari?
idan wani abu kike buƙata kamata yayi ki fad’a mana amma ba ki rika ƙoƙarin hallaka kanki da damuwa ba.
Cike da ƙarfin hali ta d’ago idanunta dake cike da ruwan hawaye ta kalli momy dashi sannan ta bude bakinta da kyar momy”ina cikin tashin hankali da damuwar da ku kad’ai ne xaku iya yi min maganinta, amma nasan ba lallai ne ku lura da halin da nake ciki ba”
Cike da tausayawa momy ta tambaye ta “fada min ko menene Ni kuma nayi miki alƙawarin xan yi miki maganin matsalar ki matuƙar dai Abin bai fi karfina ba”
Muryarta na had’ewa tace “momy fu’ad nake so shi nake son gani a tare da Ni shi kad’ai ne farin cikina idan baki nemo min shi ba hakan xai iya xama silar ajalina”
A razane momy ta kalleta “Amma ba ki da hankali me’ad ban san har yanzu ke shashasha bace sai da kika yi wannan Maganar me xaki yi da fu’ad ?
“yaron da aka kama shi da babban laifi irin wannan, yaron da ƙarshensa mutuwa ce makomarsa me xaki yi da gawa me’ad?
A daidai wannan lokacin da suke magana dadyn me’ad ya shigo, cike da nutsuwa yake takunsa har ya karaso inda suke.
“Lafiya momyn me’ad me yake faruwa?”
Sauke ajiyar zuciya tayi, “wai yarinyar nan har yanzu bata hakura da yaron nan fu’ad ba, a kansa xata jefa rayuwarta cikin haɗari, anya yaron nan haka ya bar me’ad kuwa abin yayi yawa haka”?
Dady na jin abinda momy ta fad’a fuskar sa gaba ɗaya ta canja babu annuri ko kad’an a tattare da shi.
“Me’ad!!!”
A hankali ta d’ago ta kalle shi tare da cewa “Na’am daddy”
Gyara tsayuwarsa yayin “indai Ni na haife ki nayi rainonki na hidimta miki kamar yadda kowane uba yake yiwa d’ansa baki isa ki auri fuad ba ko da hakan xai yi sanadiyyar mutuwar ki, don haka ki sa a ranki babu ke babu tarayya da ɗan matsiyata mara tarbiyya,mai safarar hodar iblis.