YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 21 to 30

Cikin ƙarfin hali me’ad ta tashi daga kwanciyar da tayi bata san lokacin da bakinta ya buɗe ba ta fara zazzaga bayani.

“Daddy baxan iya rabuwa da fu’ad ba har abada saboda ina son shi, duk wannan halin da ya shiga ku ne sanadin sanya shi a wannan hanyar saboda kun nuna bakwa son talaka kuma baxa ku bashi aurena ba, saboda ba shi da abin duniya, xan sadaukar da raina da Dukkan farin cikina wajen ganin na fitar da shi daga Wannan halin da yake ciki”

Tashi tayi ta sauka daga kan gadon da kyar tasoma kokarin barin  bari d’akin sai taji dukkan ciwon da ke damunta ya tafi, sai ma wani ƙarfi da taji a jikinta.

 

Kai tsaye wajen wani abokin karatunta  ta nufa ,wanda yakasance  lawyer ne mai zaman kansa, tana xuwa ta labarta masa halin da fu’ad yake ciki ba ƙaramin tausaya masa yayi ba, ya kuma yi alkawarin xai bi diddigin shari’ar har a gano mai gaskiya.

Ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba lawyer ya fara aikinsa, inda aka je airport din da aka kama fu’ad aka gudanar da bincike mai tsanani, cikin ikon Allah aka gano cewa akwai hannun wasu ma’aikata a Cikin laifin waɗanda aka biya su don su kullawa fu’ad sharri.

A ranar da Court xata xauna don xartar da hukunci aka shigo da wadanda ake tuhuma, ba tare da bata lokaci ba kowannen su ya amsa laifinsa kuma suka shaidawa kotu cewa Safwan ne ya basu kwangilar yin haka, a nan take kotu ta bada umarnin a tafi a taho da Safwan, Cikin kankanin lokaci aka xo da Safwan, Lokacin da aka karantar masa laifinsa bai musanta ba sai dai ya nemi kotu tayi masa sassauci.

A ranar aka saki fu’ad shi kuma Safwan da tawagarsa aka tasa keyar su xuwa gidan yari.

Ba karamin farin ciki me’ad tayi ba ganin yadda Allah ya fitar da masoyinta daga cikin tsaka mai wuya, godiya mai yawa fu’ad ya yiyawa me’ad a lokacin ya tabbatar da cewa me’ad son gaskiya take yi masa, har gida ta raka shi, sannan ta tafi gidan su.

Bayan ya samu nutsuwa ya ƙara rubuta application na neman aiki a wani Company, cikin Sa’a Allah yasa aka ɗauke shi ana biyan shi naira dubu saba’in 70,000 kowane wata.

***********

Bayan wani   lokacin fuad ya sake zuwa ma ,mahaifin  mead da batun aurensu, amman still mutumin yaki amincewa, ita kuwa me’ad tace duk duniya babu wanda ya isa ya hanata auren abinda zuciyarta ke so, da kyar momy tasamu ta shawo kansa inda yace bisa sharadin, zai amincewa aurensu, momy tace “wani sharadi ne dady?”ni naso ka hakura ka barsu su auri juna tunda shi wanda kake son ta aura ga yadda takasance dashi. 

“Babu ruwanki da yadda takasance dashi saboda nasan ba halinsa bane, yayi hkn ne bisa wasu dalilai, amman tunda kema bayan diyarki kike ba damuwa kuyi duk abinda ranku yake so ,ni dai sharadina duk runtsi duk wuya ko wata matsalar mutuwar aure kar me’ad ta sake ta dawo gidana amatsayin ni ubanta ne idan ta amince da haka fine gobe ma ya turo a daura musu aure…….

Momy ta kalli mead itama momy din take kallo zuciyarta cike da matsanancin tsoron abinda dady yace Amman take wani bangaren daga zuciyarta ta shiga hasko mata babu abinda zai faru sai alkairi a tsakaninta da masoyinta fuad. 

Dan hk muryarta a sanyaye tace “shikenan dady Dan wannan ba zai zama da matsala ba ,na amince .

“Okay kice ya turo iyayensa wani sati  da sadakinsa kawai nake bukata Dan nasan bashi da abinda zai kawo, yana gama  fad’ar hk ya juya ya bar parlour’n a fusace kmr zai tuntsura. 

Sati na cika  kuwa mahaifin kabeer  yazo masa amatsayin wakilinsa ,inda aka saida zance mai karfi, akan sati mai zuwa za’a aure,  batare da ‘bata lokaci ba satin na cika wanda yakama ranar asabar din karshen wata, aka d’aura auren me’ad ediris takai da fu’ad Muhammad argungu bisa sadaki dubu talatin. 

A ranar da aka d’aura auren,  a ranar mahaifinta yace bazata kwanan masa a gida  ba tunda an d’aura taje can takarata .

  Da sauri me’ad ta durkusa agabansa tana kuka tana bashi hakuri, batasan cewar tayi kuskure ba sai a lokacin datake ganin zatayi nisa dasu gashi har lokacin mahaifinta na fushi daita “dady kayiwa Allah kayi hakuri ka yafe min , Dan Allah kasanya min albarka acikin rayuwar aurena ,kamin fata alkhairi kada na tafi kana fushi dani, na tuba dady ba laifina bane so ..so…ne .

Komawa yayi ya zauna a bakin gadonsa cikin daga murya yace ” aure kike bukata kuma nayi miki , addua ko sanya albarkata ce dai bazan yiwa auren dana banaso ba ,kuma banga wanda ya isa yasani aikata hkn ba ki tattara kibar min gida sannan karki manta duk wuya duk dadi karki nufo gidana ….

Momy ta janyota zuwa Kan kujera ta zaunar daita kusa daita tana kuka itama  mead tana kuka “kukan ya isa haka me’ad ni mahaifiyarki ce ,naji na amince na yarda  ina son abinda kike so ,kuma ba zan tsinewa aurenki  ba ,San sanya miki albarka cikin rayuwar  aurenki, shima dady  nasan daga baya zai sanya miki albarka, sai dai  zance da zan miki yanzu bai wuce, kinsan rayuwa aure, ba rayuwa ce irin wanda kika saba bace ,  akwai bambamci dayawa acikinsa, hakuri shi ke Jan ragamar rayuwar aure, dan hk ki zamo mai hakuri Allah yayi miki albarka da rayuwar aureki…. takarasa fad’ar hkn a daidai lokacin da kanwarta hjy rahmatu ta turo kofa d’akin tashigo.

“Taso muje me’ad kowa yashiga mota ke kad’ai ake jira. 

Ta mike tsaye jikinta  na rawa hjy rahmatu ta janyo hannunta ta riketa gam dan karta fadi, momy tabi bayansu tana wani irin kuka shi kuwa dady ya koma saman gadon ya kwanta lamo yana tunanin, Allah ne kadai yasan halin daya shiga a wannan lokacin, ta yaya rayuwarsa zata cigaba da gudana batare da me’ad dinsa na cikin jin dadin dayakeson ya ganta ciki ba ?

,rashin Jin dadinta a yanzu ya zame masa babban gibi …..

Kai tsaye sai gidan mijinta dake new okoba estate, wanda da tarin gudunmuwarta aciki aka kama hadadden 3 bedroom flat din aka nufa daita. 

Tana zaune a tsakiyar gadonta lullu’be cikin mayafi sai baza kamshi take cikin hadaddiyar gezner, yayinda su misna da wasu daga cikin kawayenta ke zaune gefenta suna hira  sama sama amman ban da sajida data gocewa zuwanta, wanda ita kanta mead din take cike da mamakin rashin hallararta .

ango da abokansa suka shigo d’akin cike da barkwanci bayan sun siyi bakin amarya kmr yadda yazama al’ada suka wuce gabadayansu tare da kawayen amarya ,gidan ya saura su kad’ai . 

Ahankali K’arasowa  gareta , ya zame mayafin dake lullu’be da kanta, ya tsura mata Mayan  idanunsa , itama kallonsa kawai take,bata  ko kiftawa ,ga wani kalar murmushi datake sakar masa wanda ita kanta batasan tana yinsa ba,ahankali ya hura mata iskar bakinsa da sauri tayi kasa da kanta, take wani irin kunyarsa ta rufeta, gbdy jikinta ya d’auki rawa ta ja baya kad’ai ta zuro kafafunta kasa domin saukowa daga Kan gadon, cikin sa’a ya riko laulausar tafin hannunta, kasa juyowa tayi ta kalleshi, saboda wani irin kwarjini daya k’ara mata. 

Cikin wani salo yakira sunanta “me’ad my love my everything, yau kuma ni kike jin kunya ,sannan ina zaki tafi kibarni a daidai wannan lokacin da nake tsananin bukace dake?

“Wannan ranar farinciki ce garemu gbdy , bazan ta’ba manta wannan ranar ba saboda mahimmancinta ,ina sonki….

A yadda yayi maganar da kuma yanayin sunan daya kirata dashi bakaramin rud’ar daita   ya sake yi ba,cikin wani irin shauki ya janyota zuwa jikinsa rungumeta ajikinsa tsam yana shafa bayanta tare da aika mata wani salo na musamman mai tsayawa a zuciya ,wanda hakan ya saukar musu da kasalar da ba basu ta’ba jin irinta ba ajikinsu, kusan minti Goma  suna rungume da juna suna aikawa junansu sakonnin  soyayya sannan suka je sukayi alwala domin sake godewa Allah daya nuna musu wannan ranar, bayan sun idar fu’ad ya dade yana masu adduar zaman lafiya mai dorewa haka zalika itama tayi musu addua sosai inda yayi mata tambayoyi Akan addini ,yayi mamaki kwarai da gaske saboda tasan komai ta fanni abinda ya shafi sallah da tsarki ,ta wannan bangaren ya jinjinawa iyayenta .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button