YANCIN KI Page 21 to 30

Bayan rasuwar inna mead tasha daukar masu aiki sai dai ,abun baya zuwa koina, take sallamarsu saboda bala’I datake musu duk abinda sukayi sai taci gyaransu .
Har takai ga rokon ummi mai aikinsu ta gida momy tabata, itama zuwa wani lokaci tace kallon mijinta take da sauransu ta tattarata ta meidaita ,a haka da yau ta canza wannan mai aikin ta kore wancan har nasreen ta girma.
Wannan shine takaitaccen had’uwar mead da fu’ad .
Back to the story
Mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
Page 65 t0 66
……nasreen kwance akan gadonta lullu’be cikin bargo mai taushi, tana sharar baccinta ,hankali kwance take fitar da numfashi yayinda me’ad ke zaune a gefenta tana gyangyadi , minti daya minti biyu zata bud’e idanunta, taga halin datake ciki, can dai taja naunayen ajiyar zuciya sannan ta bud’e idanunta gabadaya tana furzar da numfashi tana girgiza kai tare da furta “fuad kenan ….
Amman babu komai , komai zai zo qarshe, ba dai gobe Monday ba?” zan sa ido inga yadda gobe zata kasance garemu ” how could you ask me to stop my work?
“For what.?
” ai abinda ba zai ma ta’ba yiwuwa bane yake fad’a idan nabar aikin sauran abubuwan da aikin nawa yake taimakawa agidan fa ?
“Shi nawa yake amsa albashinsa da har yake kokarin cewa na ajiye aiki na zauna gida, ta taja tsaki,ba laifinsa bane zan je d’akinsa yanzu nasamesa muyita tak’are .
Jin motsin fitowowarsa yasa ta yunkura ta tashi had’e da kai hannunta saman sumar nasreen ta shafa ahankali sannan tak’arasa mikewa tsaye tana gyara zaman rigarta ta fito daga d’akin .
lokacin da fito parlour’n da niyyar nufar d’akinsa jikinta ne yayi mugu mugun sanyi sakamakon ganinsa kwance datayi akan doguwar kujera cike da matsanancin damuwa, amman sai ta kau da abinda ta gani atattare dashi tashiga aika masa da wani irin kallo kana tasoma takowa zuwa inda yake kwance tana kiran sunansa cikin d’aga murya”abban nasreen!!!
Duk kiran da take masa yana jinta sarai yayi mata banza tamkr bada shi take ba har taka’raso ta zauna kusa dashi ta shafa hannunsa zuwa wuyansa… “fuad still shiru yayi mata sai numfashinsa da yayi saurin d’aukewa dan ji kmr ta jona masa electric ne ajikinsa, ahankali ta kwanto jikinsa har nonuwanta na ta’bo fuskarsa ta saita fuskarta danashi tana shakar numfashisa domin son tabbatar Da baccin yake da gsky ko dai wani shirin ya fito mata dashi….
saurin sake d’auke numfashi yayi saboda zuciyarsa datayi saurin bugawa adalilin jin abinda yafi kauna atare daita sun kawo masa ziyara wanda take yanayinsa ya sauya,lokaci daya zuciyarsa da joystick dinsa tasoma harbawa ….
Ta d’ago daga jikinsa tana yatsina fuska da tsaki “yanzu kai har kaga gurin bacci?” koda yake kana sane fa kakeyi kmr kana bacci alhalin nasan ba baccin kakeyi ba ‘amman no problem I will give you as you want it…takarasa fad’ar
tana mai gyara zamanta zuwa kwanciya a gefensa.
“Nasan cewar kana da kafuri taurin kai, Amman idan kace kana da taurin kai nima mahaukaciya ce ,gurin taurin kai har ya zarta naka ,kaima kasan da wannan, kasan halina fa ,kasan halin wacce kake zaune daita ba sai na sake gaya maka ,nasan Kana sane kake wani baccin manufurci saboda bakason akawo karshen matsalar nan dake kasa saboda mugunta ,kasane kake yin abubuwa iri iri so that ranar monday sai gidan ya saura daga ni sai yarinyata ko Dan dai ka ‘bata min rai ?
” to wallahi baka isa ,Dan ba yarda zanyi ba ,shine ka wani zo ka kwanta Dan da gari ya waye ka lalla’ba ka shirya da wuri ka wuce aiki batare da nasani ba ..”so that I will not have any choice than to stay at home with our child…saboda kasan zuciyata ba zata iya d’aukar barin yarinyata a gida ita kad’ai ba,that’s why you are playing different prank, am really ready for you…” wallahi tallahi kaji na rantse da Allah kowa zai gaya min zance ni yakamata na zauna tare da nasreen a gida bazanji ba infact I will not listing to any body ,kai koda kuwa ubana ne zai tako kafafunsa gidan nan adaidai wannan lokacin wallahi bazan yarda ba…
“kai ko inna ce zata ta fito daga cikin kabarinta tabani hakuri bazan hakura ba ,kai kuma daman kasan ina da wannan taurin kai fiyye da naka both of us must iron out the issue on ground before everything could have mess up.
shine kazo kana wani baccin gulma baccin tsiya, baccin munafurci, kai yanzu bacci ne agabanka?
“bansan yaushe ne kake son komai namu yazamo daban Dana sauran mutane ba …yanzu kai abun alfaharinka ne nasreen tazo tasameka shame shame anan wai kai ubanta kana bacci alhalin ana bukatar solutions ga rayuwarta, ka bud’e idanunka kaga yadda ni bacci ya kaurace nawa idanuwa ….
“But no problem na godewa Allah da yasa yarinyata ta samu bacci ,ni kuma daman ina da lokacin kowani irin wahala coz am ready for trouble tare zamu kwana anan har garin Allah ya waye, bazan baka chance din tashi da wuri ka gudu aiki ka barni da yarinya a gida ba, kana farkawa daga wannan tsinanen baccin naka da kakeyi da kwayar idanuna zaka samo cin karo dashi zaka san dani kake zance zan tabbatar maka da me’ad din dakasani tana nan bata canza ba ,in dai akan wannan matsalar ne bazaka ta’ba samun yadda kake so .
“You know me and I know you uhmmmmm wallahi yau bazan runtsa ba ballanatana bacci ya d’aukeni sai mun samu maslahar wannan matsalartamu tukun .
shi dai fu’ad juya mata baya yayi yacigaba da kwanciyarsa, can wuraren karfe 3 na dare ,wani naunayen bacci ya kawo mata ziyara bata San lokacin data bingire agurin tasoma sharar bacci ba ,shi kuma lokacin yasamu damar mikewa tsaye da kyar yana mika had’e da salati yana dubanta yace “wahalalliyar mata kawai, wa yagaya miki ana yiwa bacci wannan salon iskanci?
“” muna nan mu zuba inda ke zamuga wanda zai ci riba, wallahi matukar nine mijinki ,kuma ni nake rike da igiyoyin aurenki sai kin zauna gida kin kula da gida da yarinyarki zance zuwa aiki nayi cancelling dinsa inga dinsa kuma banga uban da ya isa yasani janye raayina ba yakarasa fad’ar hk tare da shigewa d’akinsa.
ba ita ta farka ba sai gurin asuba ta bud’e idanunta wayam taga babu fu’ad babu al’amunsa, Dan haka kai tsaye ta nufi dakinta..
Washegari bayan tayi duk wani abinda ya zama al’adarta ce sallah, wanka ,girka abinda zasu ci, ta tsaya kan wanka nasreen da shirinta ta bata abinci taci ta koshi da bata magungunanta ,sannan ta zauna ta kamo tafukan hannuta cikin nata suka zauna a gefen gado tashiga karanto mata aduoi iri iri na neman tsari da lafiyar jikinta ,ta tofa cikin ruwa ta bata tasha sannan tacigaba da yi mata addu’a yadda zan fita na barki cikin gidan nan lfy ,hk zan na dawo na sameki gidan nan lafiya lau cikin koshin lafiya da kuzari kina wasanki koina batare da wata damuwa ba albarkacin Annabi Muhammad s.a.w.
“mugun ji da mugun gani Allah bazai sa naji ba ,na godewa Allah dayasa zuwa wannan lokacin kina raye sannan muna raye dake, ina sake godewa Allah , Allah yacigaba da karemin ke ya raya min ke yabaki ingantacciyar lafiya mai daurewa, duk maganar datake da adduointa a kaikaice nasreen take kallonta tana furta ameen acikin zuciyarta har sanda me’ad tagama ta sakar mata murmushin tare da kokarin mikewa tsaye nasreen tace “a’a momy ,are you going out?