YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 21 to 30

Jakar ya ajiye akan table dinta da file file  sannan ya nufi office dinsa yana kwashewa da wata uwar dry “shegiyar maseefaffiyar mata kawai  karshenki yazo zamuga yadda zaayi zaman aiki ana takama sauran abokan aikinsa yakira suka hadu suka dinga zaginta . 

**********

Yau kwana biyu kenan da zuwan suhailat gidan me’ad Amman Sam hankalinta yaki  kwanciya akan matsalarta, Wanda tasan a kashi dari yayarta ce mai ragamar laifi acikin dukkanin abinda ke faruwa, tayi zurfi sosai cikin tunani dan gashi har yau monday batasan yadda lamarin zai kasance ba ,sun daidaita ko kuwa har lokacin suna Kan ra’ayinsu ,tana nan zaune har sanda momy ta fito cikin shirin fita tana mata sallama , har ta kai bakin kofa ta dawo ta tsaya akanta ta kira sunanta “suhailat lafiyarki kuwa tun d’azu ina miki magana ?

Firgigib suhailat ta dawo haiyacinta tana sauke naunayen ajiyar zuciya kana “tace wallahi momy ina cikin matsanancin damuwa , gsky banso gaya miki ba saboda banason ke ma damuwar tashafeki amman nayi duk wani nazarina naga ke kika fi cancantar nagayawa..jin haka yasa momy ta samu guri gefenta ta zauna “me ya faru? “Menene ki gaya min damuwarki.?

Wani ajiyar zuciyar ta sauke sannan tace “shekaranjiya danaje gidan aunty me’ad tun daga harabar gidan na dinga jin haiyaniyarsu .Amman tunda fita zakiyi yanzu ki bari idan kin dawo zan gaya miki komai..

“Kinga gaya min yanzu, Dan gabadaya hankalina a matukar tashe yake..

“Momy ki tafi kawai idan kin dawo zan gaya miki..”ke dakata bam ma son sake jin wani exucuse saboda duk inda zani zuciyata bazata samu natsuwa ba can zuciyata zata koma ni dai gaya min koma menene…

“Shikenan momy lokacin da naje gidan basu san na shigo ba ,ina daga waje na dinga jin ita da mijinta suna jayayya sosai, mutsu fa sosai ita dashi har ma sun fara yin fad’a atsakaninsu ..

“Sun fara fad’a fa kikace ?

“To me kuma zai hadasu fad’a su da suke zaune lfy? 

” ni dai lokacin Dana shiga shine aunty me’ad take koramin abubuwan dake faruwa duk dai akan matsalar rashin lfyr nasreen, ni dai na fara jin tsoro kar yadda suke sainsan nan kar yazamota daga karshe yazo ya saketa fa …

” uhm Allah ma ba zai sa ba,InshaAllahu babu abinda zai faru atsakaninsu sai alkairi ,irin wannan gidan bazai ta’ba hargitsewa  ba ,balle wani abu shi saki …

“Ki daina saurin kawo zance saki cikin lamarinsu ,karki sake fad’ar hk Dan ba haka ake magana ba ,koda yaushe ki dinga yiwa yayarki fatan alkairi arayuwar aurenta..

“Yadda nake ganin  kansu ahad’e kmr zasu cinye juna  ina farinciki da murna Allah bazai kawo abinda zai shiga tsakaninsu ba, albarkacin annabi Muhammad s.a.w mugunji da mugun gani bazasu ganshi ba ,badamuwa dai InshaAllahu zan kirasu. 

“A’a momy kira fa ,ai wannan matsalar ta wuce a tsaya akira, koda ma zaki kira miijinta zaki kira kice zaki zo duba lafiyar nasreen  Dan banason tasan ma nagaya miki kin dai San halinta….

“Oh ni khadeeja wannan wani irin tashin hankali ne ?”Allah ka taimakeni akan lamarin yarinyar nan, kai na ma fasa zuwa koina bari na koma ta mike ta nufi hanyar step..”ki tafi inda zaki mana koda zuwa gobe  hk sai kije, irin hk fa yasa tun dana dawo naki fad’a miki..

“Ke nace ban zuwa na fasa gbdy ma na rikice narasa gane kaina gara kawai nayi zamana..

“Oky kawai suhailat ta fad’a itama tattara kayayyakinta tayi d’akinta.

Wunin ranar me’ad kusan a tsaye tayisa acikin office dinta, wanda daga karshe shi kansa office din yasoma mata tirarin azabar azafi ata koina ajikinta ,idan tayi yunkurin zama saman kujerarta sai taji kmr ana tsira mata allurai ga km tiririn azaba zafi  haka ta dingaye office din har ta hakura ta fito daga cikinsa. Yayinda idanun mudansir Dana abokansa ke kanta sai lekenta suke suna kwashewa da dry. .

Mmn sudais ce

????????????????????????

       ‘YAN CINKI

      ????????????????

????????????????????????

             ~NA~

 *AYSHA  A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

      MRS ADAM

( YAR MUTAN KAGARA)

Page 67 t0 68

….gabadaya Kasa xaman office din tayi, ta shiga ta fita ta yi haka yafi sau ba adadi, ga tarin aiki birjik a kasa zaman jiran sanya hannunta amman kasa  aiwatarwa saboda  ji take kamar ana xuba mata tafasasshen ruwan xafi a jikinta, idan tayi yunkurin zama a kujerar kuma sai taji kamar ana sukarta da allura, haka ta dinga sintiri tana shiga tana fita, yayin da kuma su tahir da da ma’aruf da mudassir suke kyalkyale mata da dariyar mugunta.

Mudassir ne ya dafa kafadar Tahir, “mutumina kana ganin matar nan fa gaba ɗaya ta rasa sukunin rayuwarta”

A jiyar xuciya ma’aruf ya sauke tare da cewa “Kai dai bari ai yau ina ganin ikon Allah dama akwai irin wadannan Malaman a duniya, wanda suke aiki kamar yankan wuka, ai ni duk tunanina zancen da muka yi da kai wlh ya bi ruwa, baxa a taɓa samun malamin da xai iya yi mata aiki ba da jikinta zai dinga irin wannan tururin xafin gaskiya malamin nan gaske ne”

“Ai kaɗan ka gani ma domin ni malamin nan ya tabbatar min da cewa Wannan aikin da take tunkaho da takama da shi har take wulakanta mutane a kansa sai ya fita a hannunta, na tsani yarinyar nan saboda irin wulakancin da take yi mana, da sannu sai aikin nan ya dawo wajen mu”

Murmushi Tahir yayi tare da cewa “Fatana aikin nan yana fita a hannunta wajena xai dawo, ni ne xan dawo Manager Kuma bana so ku yi kin baƙin ciki, idan matsayinta ya dawo hannuna fa kamar  komai yana wajenku ne tare xamu juya Kamfanin nan yadda ranmu yake so”

Kallonta suka yi suka ƙara bushewa da dariyar mugunta, haka suka xauna suna ta tsine mata albarka a wajen nan duk juyin da tayi sai sun mata dariya, ta koma sai kace zautacciya, sai kaiwa take tana komowa duk wanda ya ganta sai yayi mamakin ganinta saboda abinda ba a taba gani bane a history din rayuwarta, saboda a kullum me’ad taxo office tana xuwa take shigewa ta xauna sai dai idan wani abu ne mai matuƙar muhimmanci yake fito da ita amma bata irin Wannan zaryar.

Tana cikin wannan halin ne tayi wani tunani, da tsayuwar nan da take yi me xai hana baxa ta kira sudais ba, (sudais aminin fu’ad ne dama kuma sun yi magana da kawarta sajeeda cewa xata kira shi ta faɗa masa matsalar da take ciki a gida ko akwai abinda zai iya yi a kai)

Wayarta ta dakko a gida ta shiga duba number sudais, tayi Sa’a kuwa kira ɗaya tayi masa ya ɗauka,  bayan sun gaisa ne ta faɗa masa cewa tana son ganinsa yanzu a gida akwai magana mai matukar muhimmanci da take so su yi da shi. Amsa mata yayi da xai zo kamar yadda ta buƙata

Suna gama wayar ta nufi bakin motarta da sauri ta shiga tayi mata key ta nufi hanyar gida, tana cikin driving taji wayarta tayi ƙara tana dubawa taga number mahaifiyarta ne, ɗauka tayi cikin ladabi ta gaisheta, tambayarta tayi jikin nasreen, amsa ta bata cewa jikin nata da sauki, magana mahaifiyarta ta cigaba da yi.

Insha Allah da misalin karfe 4:00 xata xo ta sameta a gida tana so ta duba jikin nasreen. 

 dariya tayi bayan gama sauraron bayaninta kaf “mead am so disappointed of you “Meyasa kike son maida mijinki bawa ko ince mijin hjy ni haka kikaga ina yiwa naki uban dan baki da kunya kike cewa maganar da mijiki ya fada ba maganar arxiki bce. 

“ence yarinya bata da lfy likita yace lallai sai daya daga cikinku ya ajiye Aikkns ya zauna tare daita domin kula da yarinyarta amman saboda maseefar son aiki kina kokarin batawa mijinki duniyarki kuma aljanarki rai .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button