YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 21 to 30

..idan kai cikakken nmj mai cikakken  hankali da tunani ne ,nmj da yasan yadda ake amfani da kwalkwaluwa ne bai kamata mu tsaya muna jainja akan matsalar nan ba balle argument kawai kana embarrassing your self..

Momy tayi saurin fuskantar fu’ad jikinta na wani kyarma gabadaya ta kasa furta komai illa kirjinta datake shafawa alamun ya kwantar da hankalinsa yayi hakuri zatayi wani abu akan lamarin, shi kuwa wani irin tsuma yake gbdy kokarin cafkota yake but momy ta kasa ta tsare 

Mead ta zabga masa wata katuwar harara “ok anayi maka yes sir yes sir agurin aiki ni bana   ce maka yes sir yes sir agida ?

“If you call me, how do I respond to you? Bada girmamawa nake amsa maka ba ?

A matukar fusace yace “kin gadama fadar haka da kinsani karkice sir , Like you have a choice  ,aikin me kika amsa agurina dakikiyar banza kawai da batasan ciwon kanta ba ..

” tambaya aikin Dana amsa kake, if I want to sarve ur food ,don’t I always kneel down? 

” you should have stood and placed it on my head stupid kawai, wannan ba aikin bane  ..,”ok wannan aikina ne ko ba abinda kake nufi kenan ba ..?

“Naji aikina ne , idan nagama naje gurin aiki  ta buga hannunta tana rike karamin Dan yatsanta “karfe nawa kake tashi ,karfe nawa nake tashi? 

“Did you tell me? ” zuwa wannan lokacin I will wake up early, I would have gotten to work by past seven, seven din da tuni na kammala da break wanda kai sai alokacin zaka tashi kace wanka zakayi “wai bazakiyi shiru ba me’ad ina tsaye kike gaggayawa mijinki mgn son ranki Amman ina mead taki yin shiru inda take shiga bata nan take fita ba Dan haka momy ta sake juyowa ta fuskanci fu’ad kmr zatayi kuka “kayi hakuri …”karki damu momy, tayi duk abinda  tagadama ba har gorin banda dangi tayi min ba ..

“An yi maka gori har da goroba ma, indai akan wannan banzar promotion din dazaka samu ne na yes sir yes sir wallahi baka ga komai acikin gidan tun duk wahalar danake akan baka gani nayi maka hidimar gidanka tsab nagama na tafi aiki nagama dukkanin wani wahala Wanda kai alokacin karfe hudu agida zata maka, you always get home by 5pm and be watching football match Chelsea man you here, ni zan dawo gida around 6 PM Wanda kafin na dawo idan nasan bamu da abubuwan amfani a gida haka zan tsaya  a kasuwa na tsiya  kayayyakin damuzamuyi amfani dashi da sauransu sannan na kamo hanyar gida kuma alokacin zance zan shiga kitchen kai duk kana zaune kana  kallo …

” no karkije mana kiyi zamanki, ni kike expecting naje miki kasuwa na tsiyo miki abubuwan amfani? “Meye aciki idan kaje da wannan  zaman kallon da kake ,ai zaka iya zuwa kai har girkin ma sai kayi meye aciki ?”ko kai sudais meye baka wa matarka idan bata nan , I think har momy kake  kiranta dashi ko ba hk ba ? Sudais Yayi saurin girgiza mata  kansa sannan yace “Exactly …

“Ok kana ji ai da kunnenwaka, kodayake AI abakinka na fara jin  momy sudais dayake kiran matarsa dashi  yayinda  kai har wani zaben kalar abinci dazakaci kakeyi ni pounded yam zanci, ko kaza zanci banason kaza kalli yadda hannuna ya dawo agidanka ,ko haka ka aureni da shayayen hannu ,my arms got bigger as a result of pounded yam I pound every night..

“No karki tuka ai da kince bazakayi ba kin jira nazo nayi da kaina,shasha banzar kawai ?

“Momy bai tsaya anan ba fa ..I will wash  press and pack my daughter school uniform ready for school the next day  ,gajiya zata kamani zanje nayi sauri nayi wanka domin na kwanta akan gado na huta nayi bacci har da min shari, lokacin ne shi kuma zai zo  min da shegen jikinsa yace  tashi tashi ni kiba hakina ni kuma zance ya kyaleni nagaji dayawa, Amman Sam bazai yarda zai ce shi hakinsa yake so…

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun fuad yasoma furtawa acikin  zucciyarsa yayinda gbdy ilahirin jikinsa ya mutu murus wata irin kunya ta kamashi yaji kmr kasa ta tsage agurin yashiga, ya kula bashi kad’ai yaji kunyar maganarta ba har momy,ganin taki yin shiru tanata zubo zance, yaga kunyar mara kunya hasara ne ,yayi saurin katseta ta hanyar cewa “wannan shirmen da kike fad’a bashi bane ainihin matsalar da’ake magana akanta ,idan kuma shi zaki meida topic ,but  before komai yagama tabar’barewa atsakanimu bari kiji…..

“Me zanji babu?” Ai babu  abinda zanji ,kai banson jin komai daga wannan bakin naka fu’ad ,kamin shiru dole na zayyane abinda ke cikina asan  ba zuwa aiki kawai ne amfani ba cikin gidan ,gbdy rayuwar danayi da kai azaba kake gallaza min naje aiki na dawo nayi maka girki ,dare mahutar bawa zan huta amman kazo min da matsalarka ,bani da ikon cewa nagaji kayi fushi, idan kuma na baka had’in kai ka meida kmr bad’ad’ashiyar kaza akan bed, you just starte laying with me bama kayi cike da tausayawa ba a,a ka dinga  channise dani kenan akan bed……

Wata irin razananniyar tsawa ya buga mata ba wannnan surutun naki yayi matter ba ,ki ajiye wannan maganar banzar mara ma’ana da tushe , me’ad mead !!! Wallahi kina bani tausayi saboda zaki had’u da fushina da….

” ba fushinka zan hadu dashi ba, ka kasheni idan zaka iya, karya ne bakayi duk abinda na fad’a, Baka d’aukar kafata ka jefata can dayar ma ka jefata can ka d’auki kaina ka dukar kasa, kafafuna suyi ciwo, hannuwana su rike gbdy jikina ya d’auki caji  sannan washegari zan tashi zuwa aiki byn nagama girki

” kai let me tell you something you are ready for it wallahi sai ka zauna acikin gidan ka kula da yarinyarmu..

“This all rubbish  you are saying is nt the issue on ground shasha kawai mara hankali da tunani ai ni bansa mahaukaciya nake aure ba ..

“Aaàaaaaaa ya isa ya isa but am telling sai ka zauna mutuwa ce kawai  zata dakatar da haka, Amman babu D’an kutumar babakeren da zai hana hkn kasancewa kai you must stay at home, even your mother dare not….

“Ummmm my mother?  Ya fad’i haka jikinsa na sake d’aukar kirma”my mother Zan sakeki fa ,wallahi me’ad zan sakeki kuma saki na har abada.

“I will surprise  you with divorce lest bet ki rubuta ki ajiye zan sakeki daga karshe  na kara aurena za kiga ikon Allah ba dai ni kikewa wannan wulakanci  Ba?” zan nuna miki ba zuciyata ce banida ba, abubuwan da suka faru abaya nake duba amman wallahi zan sa…

Wata irin firgiracciyar k’ara ta saki da karfi wace tasamu nasarar karad’e ilahirin parlour’n ,take gumi yashiga keto mata ta koina a ilahirin jikinta , nan take jikinta ya d’auki rawa kar..kar.. zuciyarta ta nemi tsayawa na wucin gadi ,wani irin tsalle tayi sai gata agabansa tana huci “let giv you good news your great grandmother dare not..baka isa ba fu’ad wallahi idan ka isa ka sakeni  shigiya nake you dare not ganin yadda jikinsa  yake  rawa yasa……

momy tayi saurin shiga  tsakaninsu tare da rufe mata baki jikinta na sake d’aukar rawa, zuwa  lokacin kuka momy take da idanunta “kiyi shiru me’ad kar bakinki ya jawo miki maseefa ..

  Wani irin  gumi ne sake keto mata “momy shi bakiji abinda yace ba daga wannan yar magana sakina fa yace ,wallahi fu’ad your grandmother not dare bazan saku agareka..

“Ba uwata da kakata kika zaga ba, sai dai taki uwar, yakarasa  mgnr yana d’auketa da wani gigitaccen marin dayasata durkushewa kasa da sauri dafe da kuncinta “uwarki kike  zagi stupid kawai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button