YANCIN KI Page 21 to 30

Qakarasa maganar yayi tare da bud’e mata kofar motar tashiga ya mayar ya rufe mata, shima ya zagaya ya shiga suka bar gurin, ascot da direbobinsa suka biyosu abaya .
Kai tsaye babban parlour’n gidan suka shiga, tayi tsaye nesa kad’an dashi ta rike kugunta tana cika tana batsewa, ta matsu bai fara maganarsa domin kawowa karshen zancesu ,saboda ita Sam bazata iya aurensa ba , sannan duk duniya a halin yanzu babu wanda zai takurata akan zancen aurenta dashi “kayi sauri kayi maganar sannan idan zakayita ka takaita saboda ina da abun yi ta qarasa mgnr tana furzar da iska ta bakinta “ki duba yanayina ,da yanayin shekaruna Wanda yaci ace zuwa wannan lokacin nasamu natsuwar ajiye iyali atare dani ,mead ina sonki son mai yawa, son da bansa lokacin daya shigeni ba ,amman dai yanzu ajiye wannan a gefe, a ina maganarmu ta kwana dake?
“ta kwana ne, a in da nace maka bana sonka,bazan iya aurenka ba ,ka nemi wata matar ka aura period ta fadi HK tare da runtse idanunta..
Shima runtse idanunsa yayi tare da cewa “Amman ke kad’ai ce a zuciyata ,shekara biyar kenan ina dakon sonki me’ad kuma har yau bansamu wata wacce naji ina sonta kwatankwacin naki ba, sai ke mead.
duk maganar dayake mata ahankali take fita kamar yana mata rad’a ita kuwa har lokacin , kasa bud’e idanunta tayi balle ta sake furta komai ko ta kalli kwayar idanun safwan wanda ke fitar da wani irin abu acikinsa mai kama da kibiyar so ……
jin ya qara yin kusa daita tare da riko laulausar tafin hannuwanta ahankali, shi yasa tayi saurin ja da baya daga tsayen datake.
“safwan idan saboda kyawuna ne I thought kaima kana da naka kyawun daidai gwargwado, sannan akwai yammata masu kyau wad’an da suka fini suke da duk abinda kake gani ajikina dakaji kake sona ka zabi daya daga cikinsu ka aura mana zakaji dadin rayuwarka dasu , zaka samu tattali fiyye da yadda kake tunanin samu a wajena, safwan ina son fu’ad fiyye da son kowa a duniya idan har ka fitar da iyayena “har ni me’ad kin fi son shi akaina yayi mgnr muryarsa na kmr zaiyi kuka?
“daman kai ni ban ta’ba kawowa zuciyata kai a matsayin mi….
yayi saurin janyota jikinsa ta fad’a cikin fad’ad’d’en k’irjinsa inda bai tsaya wata wata ba ya rungume tsam sbd yarigada ya fara rud’ewa daita, “karya kike me’ad bakya son shi ni kike so, shekara biyar din da muka d’auka tare, ban ta’ba jin kin ambaci sunan wani d’a nmj ba ,asalima sunana ne acikin bakinki meyasa kike son ki gujeni yanzu alhalin ina mutuwar sonki ……… ?”ki aureni zan mallaka miki komai nawa dana mallaka ke ko rayuwata kike so zan baki amman karki barni…
Tayi saurin janye jikinta tare da sake ja baya sosai tana fitar da numfashi sama sama sai alokacin ta lura babu mayafi ajikinta balle abinda takama gashinta dashi, ta bata fuska sosai tmkr zatayi kuka “me yasa ka cire min mayafi?ko kayi zaton nima kmr irin mutanenka ce ,to bari kaji na gaya maka nifa ba yar is…
“Me ya kawo wannan batu mead?su waye km mutanen nawa? Yayi tsoki yana dafe gefen kansa daya ji yana sara masa kad’an kad’an sannan yace “ki samu guri ki zauna muyi mgn, naji na janye zance aurenmu hk yayi miki?”kije ki gayawa shi wanda kike son din ya turo iyayensa kawai musha biki .
“da gaske!!! kake safwan ka janye batun aurena ?”sosai kuwa ai nafi bukatar farincikinki akan nawa..”sai me ?” Sai ga me’ad ta dawo kusa dashi ta zauna rike da hannuwansa “nagode nagode safwan Allah yabaka wace tafini “ai kibar wannan adduar me’ad saboda bazan ta’ba samun kmrki ba ,dubi surar jikinki fa meye baki dashi me’ad?
Take ta had’e rai “Ka d’auke idanunka ajikina ,ni dai na…….gode sosai, sannnan ina neman alfarma agurinka “uhmmmmm ina jinki ki roki komai kike so?
“ina son ka gayawa dady ka janye batun aurenmu sannan kayi masa zance fu’ad dan Allah idan kamin hk ka gamamin komai a duniya, kuma zan tabbatarwa kaina lallai kai mai sona ne da son farincikina.
“karki damu swe …am kanwata an gama, ba sai hira ta barke tsakaninsu ba har inda take gaya masa zatayi tafiya zuwa abuja gobe, amman kwana biyu zatayi ta dawo Dan Allah tana son kafin ta dawo yayi mata kok’ari, har kusan la’asar suna tare makale da juna kmr tun farkon shakuwarsu, kafin shakuwar ta juye zuwa soyayyar da iyayensu suka karfafata, har farfajiyar gidan ta rakashi suna cigaba da tautaunawa da kanta ta isa ta bud’e masa mota yashiga ya zauna yana d’aga mata hannu tana daga masa har motacinsa suka fita daga harabar gidan , safwan ya bar gidan zuciyarsa na wani irin tsalle da zafi tmkr ana zuba masa ruwan dalma acikinta.
**********
ta bangaren sajida kuwa, tana cikin tashin hankali mara misaltuwa ,ganin yadda kullun kwanakin aurenta ke sake. matsowa ,gbdy ta rame tayi baki ta fita haiyacinta ,bata samun ishashen bacci akan mutumin da bai san da zamanta ba ,lamarin aikinta ma tattara shi ta ajiye agefe ,sai zaman d’aki da kuka, har ta kai ga kiran emran dake k’asar London yana aiki da BBC, tana kuka take gaya masa ita tafasa aurensa ba ,shima kukan ya fashe mata dashi yana tmbyrta dalili had’e da rarrashita tare da bata hakuri ” idan narasaki sajida Zan iya rasa raina nima ,byn sun gama waya daita,ya kira acp yake gaya masa abinda ake ciki, acp yace” ya kwantar da hankalinsa tare da bashi tabbacin mutuwa ce kawai zata hana yiwuwar aurensu , tunda gashi ma lokaci ya kusa ,a daren acp bai runtsa ba sai daya dangana da d’akinta in da ya sketa kwance tana kuka “yayi mata kaca kaca sannan ya k’ara”matsawar kika butulcewa auren emran bani babu ke ,sai dai ki nemi wani uban Amman bani ba… wannan tashin hankali ke hanata sukuni da walwala tasha gwada kiran fu’ad, amman ko ya d’auka bata mgn ,sai dai ta saurari sautin muryarsa ta kashe, a ranta take aiyana ko ta auri emran zata kashe auren domin cikar burinta.
**********
Dare yayi nisa amman fu’ad ya kasa runtsawa ,shi yasan ya dad’e da tsintar kansa cikin shaukin soyayyarta, sai dai yasan rijiya ba gurin wasan yara bane, dan haka yasoma yaki da zuciyarsa, ta hanyar yakar sabbin kibiyoyin dake hud’a kowanne sako na cikinta. Sai dai duk iya kokarinsa a wannan daren baccin dayake bukatar samu ya gaza samunsa ,surar me’ad kawai yake gani cikin kyakkwan murmushinta ,Dan hk da yayi sallar asubahi ma ya dad’e zaune yana rokon Allah saukin al’amarin amman ina mead ediress takai ta kankane koina na zuciya da kwalkwaluwarsa ta karasa gangar jikinsa bata barshi da ko saqo daya da zai sanya tunanin kansa..
*********
Kmr yadda fuad bai samu runtsawa ba hk rayuka uku nan ,basu runtsa ba mead sajida safwan, safwan na kokarin ganin ya cire me’ad da lamarinta acikin rayuwarsa, ita km sajida tashin hankalinta yadda kullun me’ad take nacin son mallakarsa wannan takaicin ke hanata runtsawa . Yayinda me’ad abubuwa guda biyu ne suka hanata runtsawa da fari farincikin janyewar safwan da kuma tunanin yadda fu’ad zai fuskanci lamarinta, wanda kusan nashi tunanin ne ya hanata runtsawa, abinda tabasayi, shi mike domin yi wato sallar dare, allah yayita da dabi’u mabanbata Amman sai ya tsaida ita,da yawon son ibada acikin zuciyarta, duk iskancinta bata bari alokacin sallah ya wuceta ,wannan kuma Allah shi ya barwa kansa sani akan manufarsa gareta , alwala tayi domin gabatar da nafilfilinta data saba, tana nan zaune har sanda aka kira sallah sannan ta tashi ta gabatar, bata yi yunkuri komawa bacci ba tasoma shirinta, Dan hk washegari byn tayi sallama da iyayenta itace mutun ta farko data yiwa inna sallama a bakin kofarta , tazo ta bud’e ita kuma ta umarci direbanta daya kwaso kayan dake bayan boot din yashigo dashi sannan tasanya kanta cikin d’akin bakinta d’auke da sallama, Zuwansa gidan inna kenan yana kalaci.