YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 21 to 30

Jikin momy na rawa tace.”na nagode ko ka zageni fiyye da haka fu’ad bazai min ciwo ba ,AI kamin mutunci kuma ka mutuntani nasani. “kiyi hakuri momy  ba dake nake ba Amman yau sai naci uwar uwar me’ad acikin agidan nan” ba  uwata kika zaga ba  har da hadawa kakata,?” wallahi sai kin  gane kuranki.

 “ai nice uwarta kama zageni babu  abinda za’a yi amman dai  kayi hakuri Dan girman  Allah ka duba mutuncina karka biyewa wannan yarinyar wanda zata kashe take nema. 

“kiyi hakuri momy “no don’t worry fu’ad kana damar zagina ma,ka daina bani hkr waja min har ga Allah banji ciwo… 

“Hakuri me kike bashi momy  byn zaginki yake, ba uwata kazaga kasan wanda kazaga  ,momy ta buge mata baki kiyi min shiru yar iskar yarinya mara hali,ba dai kina biyewa yan iskar kawayenki ba ,zasu kaiki  su kaiki su baro, ke gari zai waya idan kikayi kuskuren daya sakeki wallahi babu ruwana babu hannu sai dai ki karata da matsalarki, ni  wannan mugun halin naki bansan inda kika samo shi ba….iya tashin hankali momy  tashiga  sai faman hakuri take bawa fu’ad , yayinda Sudais yayi wuki wuki da idanuwa yana zaro su waje ya had’a uwar gumi yana kadawa fu’ad kai saboda gbdyya kasa mgn yayi illa idanu dayake zarowa, shi kansa cike yake da matsanancin mamakin me’ad yana ganin  rashin mutuncin matarsa a she a she akwai mamanta a rashin sense..

 “Ba dai kina biyewa kawaye ba zakiga abinda zan miki wallahi sai kinyi mamakina “ni momy babu wasu kawaye dake zigani gsky na fad’a kuma daman shi baya son gsky ..

” gsky gidan uwar wa kika fad’a, fuad ya furta hakan a matukar fusace yana duban sudais “kai kuma k’aramin D’an iska bawan mata ai kagama had’in husumar data kawoka ko ,sai ka kama gabanka tun ban had’uku tare ba ,”kodayake  da alamun kmr kana sonta ne ko ?

“bawani yana sona ,kai dai gidan ne bakason zama sai kuma  ka zauna gida ko kaki kokaso you will stay at home. 

Cike da rawar jiki da murya sudais yace ” wata irin mgn ce hk fu’ad?” wallahi ba abinda kake expecting bane karka manta da …..

Fuad Yayi saurin katseshi da cewar  “no  karka damu kai dai  kajira na saketa sai ka aurenta..

Momy tayi saurin had’e hannuwa guri “Dan girman kabar zance sakin nan , wani irin mgn kake gayawa abokinka  da babu dadin ji..?

” momy bakiji duk maganganunsa ba ,saboda shi soko ne a gidansa  juyasa akeyi tunda sonta yake ni kuma zan saketa so that shi sai ya aureta ..

“Oooooooo let me tell you  another good news fu’ad..ko ka sakeni bazan ta’ba sakuwa ba ,matsawar  akan wannan matsalar wallahi bazan sakuba you are my husband for life bazan saku ba mutu kara ba…. 

“Ke da wa kike wannan mgnr ?

 “ke ai ba matar mutu karaba bace saboda ke ba  matar arziki ce…

“Kina ji kina gani zan sakeki kuma nayi aurena , kuma idan kin zauna kula da nasreen uwarki da ubanki zina sukayi suka haifeki, ai  idan na sakeki  dole kowa yakama gabansa  ,ki sa ido kiyi kallo this time around I will surprise you yakarasa mgnr yana kokarin juyawa ..

Mmn sudais ce

????????????????????????

       ‘YAN CINKI

      ????????????????

????????????????????????

             ~NA~

 *AYSHA  A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

      MRS ADAM

( YAR MUTAN KAGARA)

page 69 to 70

……..sudais ne yayi saurin kamo hannunsa cikin kid’ima “dan girman  Allah fu’ad kayi hakuri ,karka yanke hukunci cikin fushi, ba’ason mutun yayi saki alhalin yana cikin fushi, idan sakinta zakayi kabari ka natsu, hankalinka ya dawo jikinka  amman ba acikin wannan halin da kake ciki ba.. …

A matukar tsawace me’ad tace “meye haka ne sudais ..?

“kana hauka ne ko ka fara shaye shaye ne bansani ba,da har  na d’add,akoka cikin maganata? 

“wani irin maganar banza  ne yake fitowa daga cikin wannan banzar  bakin naka irin na marasa hankali da tunani kuma ‘yan shaye shaye?”saki ko me ..ko me naji  kake maimaitawa ,?

” wayace maka sakina fu’ad zaiyi da kake wani shirmen hauka anan .? 

“wai naga kmr… “short up there  …….”kaga kmr me ai idan ma ‘kwa’kwaluwarka na hasasho maka  saki tsakanina da fu’ad maza kayi saurin cirewa domin tsakanina dashi babu wannan kalmar har abada, mutu karaba  tare zamu qarasa rayuwarmu dashi har tsufa his my husband for life…. dan ko ya sakeni bazan ta’ba sakuwa ba, kuma babu inda zani, zama daram sai dai nida shi muyi zaman daduro ,amman wallahi bazan saku ba agurinsa zama daram agidansa no going anywhere…. Dan hk kazo ka wuce ka bar gidan yanzu bana bukatar sake ganin wannan fuskartaka fool kawai ….

a matukar harzuke fu’ad yace “dan ubanki idan na sakeki karki tafi ,ki zauna zaki ganewa idanunki kowaye Asalin fu’ad, zan sakeki.. sai dai idan na sakeki ki fad’i ki mutu amman sai kin d’and’ani radadin da zafin saki arayuwarki ,”kuma karkiyi tunani idan na sakeki zan dawo dake wallahi wallahi me’ad matsawar na furta na sakeki ,na barki kenan har abada sai dai idan mutuwa zakiyi kiyi shashar banza shashar wofi kawai da batason ciwon kanta ba ,”nayi danasani nayi danasani aurenki arayuwata, ban san haka zaki zamemin ba, wallahil azim da ban  aureki na gur’bata zur’iata ba, domin aurenki bashi da wani faida da amfani agurina facce tarin bakinciki da nadama,” a gaban mahaifiyarki gaban abokina kike  bayyana sirrin da Allah ya  boye, tur da masu hali irin naki ….”Amman babu komai da sannu zaki gane kuranki Dan komai yazo karshe atsakaninmu… ya sake juyawa fuuuuuuuu… daidai lokacin da sudais  ya isa  bakin kofar barin parlour’n yana kokarin fecewa…. 

“fu’ad yayi taku daya biyu ya jiyo sautin muryar momy cikin kunnenshi wanda yasa take ya  tsaya cak agurin , zuciyarsa na wani irin harbawa da sauri sauri, tsayuwa yacigaba dayi agurin batare daya juyo ya fuskanceta ba har sanda  ,

 momy ta sake kiransa  ” fu’ad ka dawo ka zauna dan girman allah ba dan ni ba  …….

runtse idanunsa yayi gam saboda yadda zuciyarsa ke tafarfasa ,domin  ahalin bakin cikin dayake ciki Allah Allah yake yak’arasa d’akinsa ya aiwatar da niyyarsa gareta, ko zai samawar zuciyarsa sukuni, amman yadda momy tayi masa magana bazai iya wulakantata ya wuce  ba,ko babu komai tana da wata daraja da kima agurinsa, dan hk ya juyo ahankali ya zauna yana huci tmkr mayunwacin zaki.

 momy ta numfasa ta koma ta zauna tana fuskantarsa sosai cikin mayunwacin hali da ita kad’ai tasan halin tashin hankali datake ciki , sannan tasoma magana atsanake cikin tausasshiyar murya “kayi hakuri fu’ad, wanda aka cuta shi ake bawa hkr, kayi hkr dan girman allah ba dan na kasance suruka ko mahaifiyar matar gareka ba , dan wannan yar iskar yarinyar bata bani wannan girman da matsayin ba, kayi hkr saboda girman allah da kuma girman da Allah yabani dan nasan a haife na haifi kmr ka in dakace nayi haihuwar wuri.

“bazan hanaka sakin me’ad ba har idan kaji bazaka iya cigaba da zama daita ba saboda tayi  maka abinda ya cancanci saki agurinka, sannan bazan hanaka cigaba da zama daita ba saboda nasan har yanxu kuna matsananci son junanku, iya shekarun aurenku ban ta’ba jin kanku ba sai a wannan lokacin, yanxu tunda abun yazo da haka ni adawo da NASREEN  gurina nacigaba da  kulawa da lafiyarta tunda ni zaune nake yanzu bana aikin komai ko kuma nasa akawo muku kanwar ummi tsohuwar mai aikina tazo ta dinga kula da nasreen, yarinyar na da natsuwa da hankali sosai …. amman me kagani akan NASREEN ta dawo gidana ko kuma nasa akawo najma…….. ?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button