YANCIN KI Page 21 to 30

naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da numfashi da karfi, ba zai iya rabuwa da NASREEN ba ballatana har ya kaita gidan makinyinsa da bai sonsa da kaunarsa sannan bai kaunar jininsa, duk duniya agurinsa bashi da wani makiya sama da mahaifin matarsa, tun daga haihuwar NASREEN har kawowa rashin lafiyarta bai ta’ba jin surukin nasa ya bud’e bakinsa da sunan yi musu ya jikin yarinyarsu ba, idan zatayi ciwo sau dari sai dai momy ko suhailat suzo dubata amman banda shi, dan haka bai ga haukan da zai kaishi wannan kasadar ba ,wasu zafafan hawaye ne suka cicciko idanunsa “duk fa rashin gata da galihu ne yajawo masa wanan tozarcin da kaskanci “Allah sarki inna………
” ina ma tana raye dayasan abubuwa bazasu yi masa tsanani haka ba, ahankali kalamanta na karshe garesa suka dinga zuwa masa daya byn daya “fu’ad ka kasance mai tsananin hakuri arayuwarka ,da kuma rayuwa tare da me’ad ,kayi hakuri kayi hakuri daita dan Allah ta maimaita kalmar hakuri tafi sau ba’adadi ,kayi hakuri daita domin tayi maka hallaci arayuwa ,duk runtse duk wuya karka yarda ka rabu daita saboda furucin mahaifinta gareta, wannan alfarmace da zan nema agurinka ba dole zan maka ba saboda rayuwa komai Kan iya canzawa D’an adam, Amman nasan zaka min wannan alfarmar ,Allah ya albarkaci rayuwarka data zuriarka …….
saurin danne hawayen dake makale acikin kwarnin idanunsa yayi zuciyarsa na wani irin harbawa kmr zata buga ta fito daga cikin kirjinsa.
“wayyo inna kmr kinsan wannan tashin hankali zai faru byn babu ke a duniya …” “Allah nagode maka da banyi saurin zautar da hukuncina akanta ba, bugu da k’ari ma tace kona saketa bata saku ba sai dai ayi zaman daduro, shi abinda bazai so faruwarsa kenan ba “amman wallahi ko bai saketa ba sai ya d’auki ‘kwa’kwaran mataki akanta ta yadda zata dawo haiyacinta.
tsawon lokaci yana zaune agurinsa dafe da ha’barsa yana tunanin rayuwa gbdy ya kasa cewa komai har sanda momy ta sake kiran sunansa “fu’ad bazan maka dole ba, sai dai akwai dalilin dayasa kaji na kawo wannan shawarar bazan so ku rabu da junanku ba duk da bansani ba ko me’ad ta ta’ba gaya maka gargadin mahaifinta gareta da sharudd’ansa akan aurenku , amman zabi yarage naka ka saketa ko kuma nasa akawo muku najma… …….
“dan ko agabana ka saki wannan jairar yarinyar mai shegen taurin Kan ba zai min ciwo ba ,saboda ita ta jawa kanta, son abun duniyarta ne ke neman rufe mata ido har take kok’arin manta abinda ya faru daita abaya.. ..
tunda momy tasoma magana nadama da danasani sukayi mata diran makiya wani irin mahaukacin bugu kirjinta keyi, yayinda tsoro da matsanancin fargaba suka mamaye ilahirin jikinta, hawaye ne suka shiga gangarowa daga cikin kwarnin idanunta zuwa bisa kuncinta tana gogewa wasu na sake biyo kuncinta “meyasa tayi abinda tayi a yanzu ?
“meyasa idan zuciyarta ta hau sama idanunta ke rufewa ta dinga aikata ba daidai ba……? “Why why why!!! Mead why did you do this to ur husband..?
“Ya Allah ka taimakeni kar ya sakeni, idan ya sakeni yaya zanyi da rayuwata ,ga kuma tarin kaunar danake masa ..?
“Allah na tuba, Allah ka ceceni ka sanyaya zuciyarsa kar ya sakeni, dan ina son mijina banason abinda zai rabumu….numfashi ta sauke da karfi kana muryarta cike da kuka tace “momy ki daina cewa son abun duniya ke damuna duk wannan wahalar fa danake saboda wa nakeyinta….?
” I think saboda shine da yarinyarmu nakeyi , kaso d’ari acikin albashina agidansa da yarinyarsa suke tafiya, nifa nasan abinda nakeyi momy kuma kema kinsani idan na zauna abgida rayuwa zata mana tsauri dayawa,yanxu idan wata matsalar ta taso ba fata nakeyi ba wa zai taimaka mana?
“momy bamu da mataimaki fa sai Allah, kinsani nasani momy shima kansa yasan da haka , babu wanda zai taimaka mana , da d’awainiyyar rashin lfyr nasreen ma kawai akabarmu ya ishemu fama “nawa muke siyan maganinta ?
“Magani daya akwai wanda muke siya more than 100k ban da sauran magunguna “yaya yake son nayi da rayuwata idan dai ba kasheni yake son yi ba?
” wannan aikin nawa shine rufin asirinmu …….. tak’arasa mgnr tana zubda hawayen nadamar abinda tayi masa…
Momy dake fuskantarta ta gyara zamanta kana tace “nasan da haka me’ad amman ai baki biyo ta tsarin daya dace ba sam, yanzu dai kiyi shiru muji ta bakinsa” fu’ad me kace akan shawarata?
runtse idanunsa ya sakeyi zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugu da kyar yasamu ya iya bud’e bakinsa “shikenan momy azo da mai aikin kawai dan gsky bazan iya rayuwa babu yarinyarta a kusa dani ba……
“nagode nagode !! da mutuntaka fuad Allah yayi muku albarka ,ka girmamani kuma gani kai mai Allah yasa ayi maka fiyye da yadda kamin “ameen momy.
nan momy ta juya tashiga yiwa me’ad fad’a ta inda take shiga batan take fita ba, fad’a sosai tayi mata, hawaye sosai me’ad take daga karshe momy tace “kije ki durkusa gaban mijinki ki rokesa gafarar abinda kikayi masa ,idan kina bukatar rayuwarki ta daidaita, wani irin kuka mead ta fashe dashi sannan ta durkusa kasa tashiga Jan gwiwowinta domin isa garesa, yayi saurin dakatar daita da hannunsa”no momy ba sai ta bani hakuri……..
“Karkace haka fu’ad ,kuskure ne tarigada tayi kayi hakuri ka yafe mata” ki karasa garesa kibashi hakuri shashar banza kawai mara mayo da tunani,da sauri ta k’arasa zata rike kafafunsa yayi saurin janyewa yana watsa mata uwar harara , tana kuka tace ” kayi hkr honey na tuba bazan sake ba …….
batare dayace mata uffan ba ya mike tsam ya fice abunsa yana Jan tsaki Dan yasan da wuya ta canza halinta …..
bayan fitarsa fad’a dai momy tacigaba dayi mata, akan ta rike mijinta gam gam akwai mata akan titi suna neman irinsa basu samu ba ,sannan a wannan duniyartamu babu nmj irinsa , dan da wani nmj ne da yanzu zance ya sha bambam, “yanzu yarinyar nan da za’a kawo miki , kiyi kokari ki zauna lfy daita karki Mata mugun Dan nasan halinki,ko ki koreta idan kika koreta i don’t have any option sai dai kinsa yadda zakiyi da rayuwarki dan bazan bari matsalarki ta kasheni ba…
Har bakin mota me’ad ta raka momy still fad’a take mata da Jan kunne ,tana tsaye har sai data ga tashin motarta sannan ta juya zuwa cikin gida kai tsaye d’akinta tashiga tayi showel ta fito ta canza kaya zuwa riga up shoulder iya gwiwa, wacce aka tsaga gabanta har zuwa gwiwan kafarta ,ta nufi d’akin nasreen har lokacin bacci take ,dayake cikin magungunanta akwai wanda ke sata bacci sosai , kwanciyarta ta gyara mata ta sake lullu’beta tare da yi mata kiss a goshinta ta fito ta shiga kitchen domin girka musu abincin dare ,abinda tasan yafi so shi ta fara prepare din d’orawa ,wato doya Wanda zata sarrafa shi zuwa pounded yam ,da miyar egusi ,da busashen kifi da naman kaza, tana cikin aikin taji sautin k’arar wayarta dake ajiye agefe daya ta karad’e ilahirin kitchen din , ahankali ta bar abinda take tana duba screen din wayar, sunan data gani ne yasata d’aukar wayar ta manna a kunne “hello kawata ykk ,ya kwana biyu ?
Bangaren sajida tace “komai lfy ya mai jiki kuma?
“Da sauki kawata yau dai in gaya miki yakin karshe akayi agidan nan .
“Allah kawata me ya faru kinje aiki kenan inji cewar sajida?