YANCIN KI Page 21 to 30

Fu’ad ya d’ago kyawawan idanunsa yana kallonta kirjinsa na wani irin mahaukacin buga domin sam baiyi tunanin zai ganta adaidai wannan lokacin ba ,itama kallonsa cikin kwayar idanunsa take wad’anda atake ta gane kankancewar da sukayi gashi sunyi ja alamun rashin wadataccen bacci kmr nata, kada tayi haufi inji zuciyarta shima ya kwana cikin kwatankwacin irin situation din data kwana.
Inna ta shimfid’a mata sallaya, tace “bismillah ki zauna ki kasance tare damu tasoma kok’arin zama idanunta na cikin mayatattun sexy eyes dinsa “tace anya kuwa inna ayi hk?”akan hanyar aiport nake .
“Duk da hk dai yar nan wannan sammakon da kikayi bai isa ace kin sanyawa cikinki abinci ba sai dai idan kalar namu abinci ne bai miki ba…
Tace”wallahi ba hk bane inna ,babu yadda mom dina batayi ba ,Dan na tsaya naci amman idan wannan jikan naki yayi min izini sai in ci ko acikin nasa ne.
Fu’ad ya ajiye kofin shayinsa dayake kur’ba ahankali ahankali ,idanunsa acikin nata yace “idan ni ne sai dai ince kada Allah yasa kici, me’ad da inna suka tsurawa bakinsa ido “kina kallona inna wace bataji mgnr mahaifiyarta ba, Dan me zataji tawa?
Tayi ajiyar zuciya tana mai nunasa da d’anyatsa hannunta” kai ko sannan tayi kasa da murya wanda shi kad’ai zai iya fahimtar abinda zatace “hidimomin tunaninka ne fa ya hana tsayawa na karya .
ya murmusa gently abinda bata ta’ba gani ba kenan a fuskarsa, shiru tayi tacigaba da kallonsa.
inna tace “manta dashi ki zauna kuci tare bari na qaro muku “a,a inna kibarshi kawai Dan banajin yunwa , ga sako can an shigo dashi karki ce bazaki amsa ba dan Allah inna ni dai fatana kin sanya min albarka “fu’ad ya runtse idanunsa Dan dadi yaji dadin abinda tayi amman bazai bari wannan kyautar shiga tsakaninsu ba ,ahankali ya bud’e idanunsa yasanya cikin kwayar idanunta sannan yakira sunanta”me’ad ..
wannan shine karo na farko da hkn yafaru taji sautin sunanta abakinsa wani irin abu taji yana yawo acikin jikinta. Dama kwalkwaluwarta gbdy ta amsa da “na’am fu’ad “ki koma da abinda kikazo dashi mun gode kwarai da kulawa….
tayi kicin kicin da ranta sannan tace “ina ruwanka da abinda na kawo?”inna na kawowa ba kai ba balle kace hk ta waiga gurin inna “inna ni zanyi tafiya zuwa abuja ki min addua sannan ki sanya min albarka, kai kuma sai kaji wayata ta mike tsaye inna na kwararo mata addua sukayi sallama.
Can dare har ya kwanta wayarsa ta d’auki kara yasan babu wanda zai kirashi a daidai wannan lokacin sai ita, ya mika hannu ya d’auka zuciyarsa na beating ya manna a kunnensa a kasalance yace baki kwanta ba ?
Tace “na kasa bacci ne ,na sauka lfy Amman tunani na neman mayar dani mara lafiyar karfi dayaji.
Ya rage muryarsa saboda kada ya tashi su kabeer yace ” ke kuwa tunanin me kike hk me’ad?
“Kai tsaye tace “tunaninka?
Yayi ajiyar zuciya mai sanyi cikin ransa yace “nima hk tunaninki ya hanani walwala da runtsawa ,bai san cewa a fili ya fad’a ba ita kuwa kunnuwanta sun rigada sun zuko mata sautinsa, tayi murmushin jin dadi wanda ya fidda sauti, cikin ranta km godiya tayiwa Allah daya takaita mata wahala da rashin tabbas din datake hangowa alamarinsa.
Daga nan sai me? Sai hira ta ‘barke tsakaninsu kmr ba fu’ad ba shi kansa har mamakin kansa ya shigayi ta yadda cikin kankanin lokacin me’ad ta tankwasa zuciyarsa ta sauya mata akidar tunaninsa, na bazai saurari kowace mace ba har sai byn ya samu aiki, tare da daidaita a rayuwarsa sannan zai bud’e shafin soyayya.
Amman gashi a wannan daren ya kulla soyayya mai karfi mai ban mamaki da me’ad takai wanda bai ta’ba tsintar kansa ciki ba.
Tun daga ranar kullun sai sun raba dare suna wayar soyayya, har tabaro abuja, yanzu ne me’ad tasan tana cikin shaukin soyayya, ba soyayyar kuruciya ba da’ake son tursasa zuciyarta ciki . wasu emotion ke tangaliliya da rayuwarta da zuciyarta akan fu’ad dake aiki cikin zuciya da kwalkwaluwarta. bata ‘bata lokaci ba gurin sanarwa da aminiyarta sajida ba ,wanda wannan sakon yayi gigita ya haukatata har yayi nasarar kwantar daita a gadon asibitin ..
Mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
Page 55 to 56
…….bata san inda hankalinta yake ba, sai farkawa tayi ta ganta a gadon asibiti ,ta fahimci hakan ne ta hanyar ganin wata nurse a tsaye akanta, dan tana bud’e ido daita tasoma cin karo tana kokarin sanya mata k’arin ruwa.
tayi saurin mikewa zaune tana raba idanu tare da tuna abinda me’ad takirata a waya ta sanar mata wanda shine abinda ya haddasa mata zuwa asibiti , me’ad wace dawowarta kenan daga tafiyar datayi zaune take abayanta tana mata sannu , jikinta a matukar sanyaye, sai dai kallo daya sajida tayi mata abinda ta gaya mata ya sake dawowa cikin ‘kwa’kwalwarta da gangar jikinta, idanunta gbdy sun rikid’e sun dawo kamar gauta al’amar taci kuka tagaji dan har lokacin hawaye ke bin kuncinta,tana jin tmkr ranta ake zara gbdy takaicin me’ad take ,a halin yanzu bata jin akwai halitar data tsana sama da emran daya nacewa aurenta sai km me’ad datayi wa rayuwarta karan tsaye ,tana matukar son fu’ad kmr tayi hauka aganinta ita tafi cancanta yaso ba me’ad,saboda tafi tsananin son shi da buk’atarsa .
“Me yasa so yayi mata yanka kauna irin hk?”me yasa idanunta suka had’u dashi? “Ina ma batayi mata rakiya ba a wannan ranar, ranar datayi silar dagulewar duk wani lisafin rayuwarta…..takarasa zance zuci tana sake fasa wani irin gigitaccen kuka tare da fizge hannunta daga rikon da nurse tayi mata,sannan ta bar jikin me’ad ta kakkame misna tana wani irin kuka “shikenan narasa shi ko misna ?
Ta furta hkn a bayyane ta sake tafiya luuuuuuu sai gashi ta kifa k’asa daga misna da me’ad har nurse din sun gigice har aka rasa wanda zai yi wani abu akai.
me’ad ta durkushe bisa gwiwowinta tana jijigata cike da matsanancin tashin hankalin ,da kiran sunanta cikin k’araji, yayinda kukan datake ta rikewa tun d’azu ya kwace mata, ita kuwa nurse da gudu ta fice daga d’akin dan kiran likita atare suka dawo wannan karon har da dady da acp da hjy Khadija mahaifiyar me’ad suka biyo bayansa.
likita ya d’agata da taimakon su dady suka maidata kan gadon yayyafa mata ruwa sukayi, sai kuwa ta bud’e idanunta tare da sakin wata ajiyar zuciya da karfi ,idanuta ya d’auro akan mahaifinta da iyayen me’ad “Allah sarki uwa mai dadi,ina ma tata uwar na raye da wata killa tazamo sanyi idaniyya mai share mata hawaye, acikin wannan halin datake ciki.
kallon mahaifinta take tana kuka sosai a zuciyarta ta sake furta “shikenan narasa shi ko?
gbdy suka k’araso gareta cikin tashin hankali saboda jin furucinta a she a filli tayi mgnr batasani ba “waye shi din wanda kika rashi?
me’ad da momy suka rungumeta suna gunji kuka cikin kuka momy tace “sajida waye shi ki gaya mana ko waye shi da kike ikirarin kin rasashi, “a tunaninmu emran kike so kuma yana raye bai mutu ba, asalima yanzu muka gama waya dashi.
Girgiza kai tasoma yi tana fidda numfashi sama sama “bashi ba..bashi nake nufi ba ni kad’ai nasan kowaye ,wanda nake nufi yana raye sai dai narasashi…..