YANCIN KI Page 21 to 30

“.ki gaya mana kowaye shi zamu san abin yi “a’a khadeeja koma waye shi sai dai ta hakura ,sbd ni bata ta’ba sanar dani tana son wani ba byn emran,wanda itace da kanta ta kawo min amatsayin mijin aurenta, kuma zuciyata ta aminta dashi,” kan wani dalili take son maidamu kananun mutane.?
likita ya dafashi alamun rarrashi yana cewa “ka kwantar da hankalinka ranka ya dad’e,ka natsu ka binciketa da kyau idan har batason shi wanda ta kawo din yanxu ,sai a hakura mana , “itace dai zata hakura da koma wani d’an iska ne . “Alamarin na soyayya mafi yawa masu kwalkwaluwa irin tasu su kan d’auketa da tsananin sai daga baya komai ya daidaita, kamata yayi kasamu lokaci kayi zaman sirri daita domin sanin kowayeshi yaron, “wallahi kaji na rantse sajida bata da miji daya wuce emran koda mutuwa ce sai dai ta dauke ad’akinsa Amman…
wata irin zabura tayi hjy Khadija ta rikota da sauri,wanda hkn yayi nasara katse acp ya tsura mata ido, shi kansa dady sai dayayi dayasani furuncinsa,saboda yadda yaga gbdy ta sake firgicewa, likita yayi kok’arin ‘ban’bareta da kyar daga jikin momy yana fad’a tana sakin momy ta sake Sumewa alamarin daya d’aga musu hankali kenan kuka kawai suke har da acp ,momy tace wannan wani irin maseefa ne ? A zuciyarta.
” Ga zance me’ad dake soyayya da d’an talaka ,wanda har yanzu mahaifinta bai sani ba ga lamarin sajida.
likita yana bata taimakon gaugawa yace “ban so ka dinga fad’ar irin wand’an maganganun ba,yallabai, irin wannan lamarin rarrashi da nasiha yake bukata da kwantar da hankali yakarasa mgnr yana mata allurar bacci sannan yacigaba “koda zata farka Insha Allahu zata dawo Normal”Allah yasa suka amsa gbdy,lamarin na sake d’aure musu kai.
Cikin ikon Allah kmr yadda likita ya fad’a koda ta farka tasamu natsuwar zuciya , bugun zuciyarta datake jin ya tsananta ,yayi k’asa sosai yasoma dawowa daidai, sai dai kallo daya zaka mata kasan tana cikin matsanancin damuwa. Lokacin da me’ad ta gama taimaka mata tayi wanka da sauransu ta matsa da tambaya.
“waye shi wanda kikarasa sajida ,da har yayi silar kwanciyarki hospital?tayi mata shiru taki cewa komai “to mai ma zata ce mata,tace akan fu’ad tashiga wannan hali ko mai? Ai ma abun kunya ne ita da aminyarta sun kama da soyayyar mutun daya kmr wani almara.
Tsawon lokaci me’ad na tare daita tare da son jin damuwarta amman sam sajida taki gaya mata komai”wato ni ban san ciwon kaina ba kenan danake gaya miki sirrukana da abinda ya shafi rayuwata ba ko ?
“shikenan sai kicigaba da rike damuwarki ke kad’ai mu km zamu cigaba da tayaki da addua, Dan ni tuni zuciyata ta soma zargin kin fad’a soyayya da wani mafi kusanci damu.
“ba karya kika fada….”ina ma zaki bar min shi da har karshen rayuwa bazan manta dake ba?tayi mgnr cikin ranta tana mai runtsa idanu.
Kwananta biyar a hospital likita ya sallamota duba da ganin samu saukin jikinta,domin tayi kokarin tsaida zuciyarta gurin soma cire fu’ad cikin ranta, ta sake maye gurbin gurin da emran kai tsaye gidansu me’ad aka wuce daita bisa umarnin mahaifinta daya bayar.
Kowa a gidan attention dinsa na kan sajida da bata duk wata kulawa tare da sanyata cikin nishadi, hkn nayi mata dadi sosai sai dai har lokacin tunaninsa yaki barinta.
*******
Yau me’ad da kanta tashiga kitchen sa’baninta lokutan baya,ta had’a dinner mai rai da motsi da taimakon ummi sannan tashiga wanka har ta fito ta tsaya gaban mirrow hankalin sajida na kanta tarasa dalilin da hk kawai take jin babu aranta, a game da wanka data shiga, ahankali me’ad tayi shafinta ta shirya cikin wasu had’ad’d’iyar doguwar riga swiss less ruwan zuma tana fesa turare a kowani lugu na jikinta kararrawar shigowa gidan tayi k’ara sannan wayarta ta hau ruri tabbacin fu’ad dinta ya iso kmr yadda sukayi dashi, daman tun a safiyar yau kai tsaye takira masu gadi ta gaya musu tana da baKo su barshi yashigo, tayi taku d’aya biyu taji sautin muryar sajida cikin rauni dayasa ta tsaya batare data juyo ba “fu….fu’ad ne yazo . ?”uhmmm ta bata amsa dashi tana gyara mayafin jikinta “ok ki gaida min shi “zaiji ta sanya kai fice daga d’akin ,mead na fita ta mike tashige bayi saboda kukan daya tunkuro mata mai had’e tari ,tana shiga ta fashe da wani tsumammen kuka.
Me’ad na k’arasawa farfajiyar gidan,ta d’aura kyawawan idanunta akansa sai ta nemi daburcewa , kasancewar wani azababben kyawun dataga ya kara mata, suka dubi juna da wani irin kallo mai kwantar da zuciya, kafin kowannensu ya saki murmushin mai d’auke da boyayyar ajiyar zuciya.
Gaba tayi ya biyota abaya yana kallon kugunta dake juyawa ahankali wanda yasoma tayar masa da boyayyen tsumin shaawarsa da bai san yana daita ba ,da sauri ya d’auke idanunsa zuwa yanayin tsarin gidan , adaidai wani karamin parlour’n baki ta tsaya tare da kaucewa tabashi hanya yashigo parlour’n cikin kodaddiyar shadda mai hasken sararin samaniya gilashin idanunsa fari ne dan siriri, wanda ya fiddo da zahirin cikar kamalarsa na cikakken d’a nmj wanda rayuwa ke yayi ,matsalarsa dai rashin aiki da kudi, ita kanta tana da tabbacin da zai kasance mai aiki a hannunsa, matan da zasuyi rubibinsa suna dayawa da wata killa ma bata had’u dashi ba me’ad tayi nisa sosai a kallonsa, yayi murmushi yasoma busa mata iskar bakinsa a idanunta tayi firgigib ta dawo haiyacinta .
“kallon ya isa hk me’ad ,sosai taji kunya abinda yace, ta wuce ciki suka zauna cikin kananan leather da suka yiwa qaramin parlour’n nasu qawanya.
Tace “sannu da zuwa honey ya hanya? Yayi murmushi tare da lumshe idanunsa kmr bazai amsa ba sannan yace “lfy . tayi D’an jim tana kallonsa sannan suka gaisa gbdy suka kasa boye soyayyar dake zuciyoyinsu sun jima suna bayyanawa juna sakonni zuciyoyinsu daga karshe ta gabatar masa da abinci da abun sha amman Sam yaki ci komai “iya ganinki kad’ai me’ad ya isheni ….taji Dadin wannan furuncin nasa sosai har kasa boye farincikinta.
Sajida takira mahaifinta dayazo ya d’auke da kansa, Dan bazata iya tuki ba, ta gwammaci zaman kadaitan gidansu akan tacigaba da zama tare da mead, wacce bata iya boye son fu’ad ako gaban waye,nunawa take, da yammanci ranar tana kwance tasoma jiyo jinia, ta tabbatar da mahaifinta yazo, har cikin gidan yashigo sun dade da dadyn su mead suna tautaunawa akan yadda bikinta zai kasance ,sannan daga baya yasa akayi kiranta nasiha da rarrashi sosai dady yayi, har gaban motar dazata shiga ya kai ya bude mata da kansa yana sake rarrashita ,dady na tsaye har sai daya ga wucewarsu sannan ya koma cikin gida yana girgiza kai.
********
Soyayya fa mai karfi tashiga tsakanin me’ad da fu’ad, cikin salo mai ban mamaki basu iya sati basu sanya junansu a ido ba ,kullun yana kan hanyar zuwa gidansu idan kuma bai zo ba, suna makale a waya, duk wannan wainar da’ake toyawa babu wanda ya sanarwa dady har safwan dan koda ta tmbyesa ko ya sanar masa “cewa yayi bai samu had’uwa da dady ba,gashi tafiyar gaugawa tasameshi American sai ya dawo tukun.
Bata damu ba, tacigaba da bawa fu’ad kulawa, fu’ad shi din yasan me Nene so? yasan darajar abinda yake son,ya km iya tafiyar dashi ta hanyoyi daban daban, ta yadda duk wanda zata so shi,zata so shine da dukkanin zuciya, ruhi da gangar jiki koda taki Allah shi ba dan bariki bane, amman ga matar dayake so, mugun dan soyayya ne kmr ba indiye dan irin kalaman dayake furta mata azahiri da cikin waya idan ka ganshi a zahiri rantsewa zakayi kace bashi yake fad’arsu ba ,sbd tsare gida da rashin son raini ,Dan hk ne bai sha wahalar sake yiwa zuciyar me’ad kamun kazar kuku ba, bata da wani tunani sai na fu’ad ,bata da wani ra’ayi sai nashi bata da wani buri sai na mallakarsa matsayin abokin rayuwarta har karshen rayuwa.