YANCIN KI Page 21 to 30

Gbdy ta mance da wani safwan dake can wata kasa tattare da dakon soyayyarta ,a wani zuwa ne da fu’ad yayi tana zaune gabansa cikin less mai taushi fari sol da zanen silver ,dinki bakaramin kama jikinta yayi Dan har saman dukiyarta yana iya hangowa, shr yayi zuwa wani lokaci sannan yakira sunanta muryarsa a kasalance “mead, na zauna nayi tunani mai yawa akan lamarinmu dake, ni talaka ne sannan d’an talakawa gaba da baya, wanda yake karkashin kulawar kakarsa ,da bata da komai ,bata aje ba sannan bata bawa kowa ajiya ba,gani zaune babu aikin yi ina sonki sai dai bansa yadda zanyi ba idan batun aurenmu ya tashi .
Maganganunsa sun mata ciwo matukar da hk muryarta a d’an zafafe tace “duk nasan da hk fu’ad nace ina sonka.
Ya langwabar kansa tare da tsura mata idanu kmr zai cinyeta sannan ya bude bakinsa da kyar yace “zaki iya zama dani cikin halin babu, sannan bazan iya rayuwa babu innata a kusa dani ba saboda nayi aure, Dan tayi min komai arayuwa, byn kasancewarta kaka gareni uwa ce mai tattare da matsayin uba, ta taka matsayin komai gareni zaki iya tallafawa rayuwata data innata?
Ta lumshe ido cikin wata sabuwar kaunarsa dake mamayarta ta km lullu’be zuciyarta “kada ka damu baka da matsala dani fu’ad soyayyarmu had’in Allah ce ba dan wasu kyale kyalen duniya ba, kacigaba da tafiyar da rayuwarka hk ina sonka hk , ina girmamaka sbd dattakonka,ni fuad din kawai nake so bawani abu nasa ba ,ina matukar sonka ta yadda har bazan iya waiwaya ba, in hango hierarchy dinsa ,yake gani wanda shi so baya la’akari dasu…..sai byn data furta hkn kunya ta lullu’beta Dan ganin irin yadda jikinsa yajike yake tsuma km ya zubawa dan karamin bakinta idanu dake motsi yana fitar da kalamai masu sanyi garesa, tacigaba “ni dai fatana da burina ka rikeni amana ka yardani nima in yarda da kai, Allah yardadamu yabamu ikon mallakar juna idan kayi min wannan, ni km nayi maka alkwarin zama da kai muddin rai cikin kowani irin hali ,akwai ko babu dadi ko akasin sa….da sauri ya mika mata hannunsa tun kafin takarasa.
“shake my hands my love..nagode da soyayyarki gareni, ina rokon Allah ya fiddani kunyar soyayyarki..yabani ikon fita hakkokinta yabani ikon sanin mahimmantata fiye da duk wani alamarin da dan adam ke burin samu suka had’e hannuwa guri daya kmr masu kulla alkwari.
Ta lumshe ido jikinta na tsuma saboda had’uwar tafukan hannuwansu ,domin ji wani abu na fita daga cikinsu zuwa nata naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana sake damke hannunsa cikin nata sannan tace “sai batu na neman aiki fu’ad kabani CV’s dinka a samomaka aiki, ina bukatar ganin cikin office honey, ka yarda ka amince min….
Murmushi yayi “kibar wannan issue din, nima ina kan nema da kaina wanda ya amshi takarduna ina sa ransa samu, ki min addua yakarasa mgnr yana saka yatsun hannuta cikin bakinsa, bai tsaya bata lokaci ya fara tsotsarsu domin kwantar mata da hankali, aiko take abinda yake bukata daga gareta ya kau Dan jikinta ya d’auki kyarma dan ji tayi kmr yana zarar ranta da kyar tasamu ta kwaci hannunta fa fad’a jikinsa .
************
An yi bikin sajida na ban mamaki sannan aka kai amarya gidan mijinta dake cikin ajawo estate, ‘yan kai amarya mutun Hudu basu tsaya ba ,suna kaita suka juyo bayan kowa ya fita ne ta d’auki jakarta tashige d’aki ta kulle kanta har gari ya waye sannan ta shirya ta fito ta zauna cike da jin haushi emran ita fa fu’ad take so, zuciyarta ta kasa hakura dashi gbdy ango yarasa gane kan amaryarsa, duk yadda yayi daita taki haushinsa take ji, da ganin bai iya komai ba ,komai yayi bai iya ba fu’ad ne ya iya kwata kwata baya burgeta tana zaune emran yashigo yana fara’a wai shi me amarya ya samu gefen kujerar da take zaune ya zauna tare da zura mata ido baya ko kiftawa.
ita kuwa ko kallo bai isheta ba ta juya masa baya dama tagaji da kallon dayake mata kawai sai ta mike tashige dakinta .
yasha mamakin abinda ya faru shi daman tun kafin bukinsu yaga ta canza tmbyr duniya yayi mata taki amsa masa .
Satinta daya a gidan
da yamma emran yashigo yace taxo yana son ganinta, bata kulashi ba dan bai isa ba shi km ya dawo parlour’n ya zauna yana jiranta ya jima yana zaune a parlour’n amman bata fito ba hkn yayi maseefsr ‘bata masa rai ya tashi ya koma cikin d’akin yasameta a kwance a inda ya barta batare da niyyar tashi ba ,ya daka mata tsawa da cewar sajida wai me ke damunki ne da har zan dinga miki mgn kina jina byn ba dole nayi miki ba ?
“wai ma me kike nufi ne tun sanda aka kawoki gidan nan kin kasa zuwa ki gaida iyayena, dan baki d’aukesu abakin komai ba,
sannan ko ruwan zafi baki tab’a dafa min kin kawo min nasha ba balle kiyi min girki irin na mata da miji ki kawo naci to kisani bazsn dauka ba..
sajida dake kwance jin yayi shiru yasa ta tashi zaune tana yiwa emran wani kallon tsana tace “amman emran kabani dry dan ina jin kana da matsalar kwalkwaluwa, banda hk ka dubeni da kyau kace wai ni zan maka girki ashe zaka mutu da yunwa bakaci ba,dan ni ba yar aikinka bace kuma ba tun yau ba kasani ko ruwan zafi ban iya daurawa ba, idan kuma ka manta na tuna maka saunawa me’ad na sanar dakai sajida bata iya komai ba?
Dan hk ko ruwan zafi dazaayi wanka dashi ban iya dafawa ba ,kai ko gas ban iya kunnawa ba balle km yin girki dan hk ka nemi wace zata dafa maka abinci sannan zance inje ingaida iyayenka ai basu na aura ba su dan girman kai tinda nazo gidan basu zo ganni ba balle su girmamani amatsayina na matar d’ansu, kaga nima bazanje in gaidasu ba don neman gindin zama bazanje koina ba kaji ko?
idan km sai naje ne sai dai ka sakeni nakara gaba..
“au haka kikace ko?
Emran ya fad’a cikin ‘bacin rai “Kwarai na fad’a itama ta mayar masa tana cewa dama kasakeni naje nayi yakin neman auren fu’ad shi kawai zuciyata ke muradi ba kai ba ta fada aranta.
bai kuma cewa komai ba yasanya kai ya fita yana mamakim abinda ya canza masa sajidarsa ,shi ba zance rashin girkinta ne yafi damunsa kmr yadda take nuna kiri kiri bata sonshi yanzu.. idan rashin girki ne ya Dade dasanin hkn, km har yayi tunanin nema musu me aiki amman kwata kwata yarasa meyasa ta tsiro masa da wannan halin to ko dan taga yana maseefsr sonta ne?
amman yasan yadda zai yi mata momysa zai gayawa watakilla yasamu kanta .
yana fita sajida taja wani dogon tsaki ta koma ta kwanta lamo tana tunanin fu’ad.
Mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
Page 57 to 58
………Emran na fita kai tsaye bangaren ummansa ya nufa bakinciki duk ya cika masa zuciya,umma ta sarawa d’an nata lokacin daya gaya mata irin abinda sajida take masa .
Umma da kanta taje bangaren sajida domin yi Mata fad’a saboda tana mutuwar sonta kmr yadda emran dinta ke sonta, Amman abinda sajida tace ya kusan sumar umma dake zaune cewa tayi ” hjy ai ba nice kawai mace ba a duniya , idan yaji haushi kuma bazai iya da halina ba ya sake aure tunda yana da kudin da zai iya auren ko mata nawa ne,Dan ni ba ruwana ,abinda nake son ya gane kuma ya fahimta banzo gidansa Dan in yi masa biyayya ba,ko wani bauta, shima yasan da wannan, in karya ne ki tmbayeshi gashi nan zaune agabanki .