YANCIN KI Page 21 to 30

Umma ta girgiza kai cike da bakinciki sannan tace “shikenan babu komai tunda da kanki kikace yayi miki kishiya zakuwa ayi da yardar Allah, Dan kuwa zan tabbatar da d’ana emrana ya auro santaleliyar budurwa yar gidan mutunci.
“To ni hjy manene zai dameni ,byn nima har yanzu amatsayin budurwa nake babu nmj daya ta’ba takani , ni da zaki taimakamin ma da kinsa wannan d’an naki ya sallemi na huta…
emran ya yunkura ya mike jikinsa na rawa zai d’auketa da wani gigitaccen mari, hjy tayi saurin taresa “kul karka soma … akwai abinda yafi duka ko mari zafi arayuwar d’an adam, shi yafi cancanta kayi mata ba mari ba Dan ko ka mareta bazaka huce ba.
Gabadaya jikinsa kyarma yake “yanzu har sunzo gurin shi sajida,?wulakantashi da iyayensa zagaye dakin yasomayi zuciyarsa na masa daci da tafarfasa, ita dai umma bata sake cewa komai ba ta tashi ta fita tana jin zafin abinda sajida tayi mata, sai dai tayi kanta alkwarin duk runtse sai ta aurawa emran mata har biyu sai dai idan shine baya so.
Kwana hudu tsakani abinda daya faru da daddare suna bacci kaddara ta fad’o gidan, domin barayi ne sukayiwa gidan diran makiya, saboda jin labarin emran yashigo da wasu makudan kudi masu yawa xshiyasa sukazo dan su amshi rabonsu, gabadaya mutanen gidan suka tara a falo daya, duk sukace kowannensu ya kwanta flat a kasa ,kowa ya kwanta amman banda sajida saboda jin itace diyar acp , taki kwanciya babu yadda emran bai yi daita ba amman taki, babbansu yace” da kyau yar kanwata kinfa burgeni sosai, dan kina da zuciya mai dakiya ke matar ‘barawo yakamata kizama bana na maikacin BBC ba , amman duk da hk za’a shafa miki bakin fanti da iya rayuwarki idan kika tuna zaki ji zafi, ke ba iya ke ba har ya’yanki sai bakin fenti ya shafesu, yakarasa mgnr ya kalli wani baki mummuna daga cikin yaransa yace “kai shigar min daita turakar mai gidanta, in sha jinita sannan nayi maganin abinda ke damun kwalkwaluwarta. Take yaron ya isa inda sajida take ya kama hannunta da karfi ya fixgota xuwa jikinsa, tayi waya siririyar kara tare da kiran sunan emran da mahaifinta cikin tsananin tsoro da razana.
Emran yayi saurin d’agowa ya dubi ogan zuciyarsa na beating yace “Dan Allah oga kayi hakuri wallahi duk abinda kake so zan baku in dai zaku kyalemin mata amarya ce ka duba girman aure.
Ogan yayi dryr mugunta yace “kada ka damu abokina zan koyar daita komai sannan zai koya mata hankali da ilimin rayuwar duniya ba cutar daita zaiyi ba, idan kuma ka sake mgn abakin ranka ya afka d’akin daaka shigar daita,shi kuwa emran bai sake cewa komai ba yana jiyo ihun sajida tana kwalla ihu da gudu ya tashi ya nufi hanyar d’akin yana kiran sunanta Amman Kan ya karasa wani ya daki kansa da tsinin bunduga anan ya zube kasa a sume bai sake jin komai ba, sai farkawa yayi ya gansa kwance a d’akin ummansa su km kannensa sun zagayeshi ya dubi umma yaga fuskarta tana cikin damuwa ya sauke ganinsa Kan wasila kanwarsa yace “wasila sun kashe min sajidata ko?
Sun kashe min yar amana,” amanarta mahaifinta yabani, sun kashe min ita ko?
Wasila ta girgiza kai tace “kayi hkr yaya basu kashe kowa ba sai dai sunyiwa sajida fyade , wata irin zabura yayi ya mike tsaye cikin takaici, tabbas sajida ta cucesa wata daya da yin aure Amman bata ta’ba zuwa dakinsa ba kullun akwai wulakanci datake masa daban daban akan hakinsa tace”bai isa ya kusanceta, yau gashi wani katon banza wanda bashi da imani yazo har gida kuma har cikin dakin aurenta ya keta mata alfarmar aure, tabbas hakkinsane ya kamata tun baaje koina ba.
Ya dawo da kallonsa wajen ummansa yace “umman yanzu tana ina?
Umma ta d’auke kanta daga kallonsa tace”ina zata? “Tana dakinta mana ,wannan mugun halin nata da kunya bazai barta ta zauna cikin mutane ba .
Emran bai ce komai ba ya mike cikin sanyin jiki tana can kuryar gado ta had’a kai da gwiwa tana kukan nadama da cutar kanta datayi bisa rashin kunya wanda ba halinta bane a da.
Ya tsaya abakin gadon ya tura hannuwansa duka biyu cikin aljihun wandosa “ina ganin bamu ya kamata ki zauna kinawa kuka ba, kamata yayi ki bisu kiyi musu kuka ina tunani hk ne zaifi ,tunda su suka miki laifi ba mu ba, in km baxaki gane inda suke ba ya zame miki tilas kiyi hakuri Dan ba zai yiwu ki cika mana kunne ba.
Sajida tayi saurin kallo emran cikin mamaki ,cikin sanyayyiyar murya daya santa dashi tun farko haduwarsu tace “amman emran ai ya kamata..
“Yi min shiru muguwa in mugunta ce ai kanki kikayiwa bamu ba, Dan hk tun kan dare yayi miki ki nemi wanda yayi miki fyade kiyi masa wannan banzar kukan naki bani ba ,yakarasa mgnr yana saukar da numfashi zai yi mgn sai km ya fasa ya juya ya fita cikin bakincikinta.
Sajida ta km fashewa da wani kuka yanzu ya zatayi kenan ? Tarasa fu’ad tarasa emran tarasa budurcinta tyi biyu babu…..
**********
Kwana goma kenan sajida bata saka emran acikin idanunta ba ,kai ita kan tana cikin taskon rayuwa duk batagane abinda yake nufi da hkn da yayi mata ba ,ta mike jiki a sanyaye ta nufo hanyar parlour’n inda tasame shi zaune yayi tagumi itama ta nemi kujera kusa dashi ta zauna tana kallonsa kafin daga baya tayi ajiyar zuciya da numfashi atare sannan tace” emran ina son kasakeni….gabansa yayi wani irin bugawa saboda har ga Allah yana sonta ransa a matukar bace yake daita shiyasa ya shareta, amman ji mgnr banzar datake gaya masa,wani kallon wulakanci yayi mata sannan a matukar hassale yace”ai kin san yadda ake yin sake, ki dauko takarda da biyo kiga yadda bazan sakeba, aikin banza kawai yakarasa mgnr yana furzar da iska ta bakinsa.
tsam ta mike ta shiga dakinta ta fito hannunta rike da fallen takarda da biro tazo ta mika masa gashi” ka sauwake min yanzu na bar maka gidanka dan konace zan cigaba da zama da kai ba daraja zanyi ba ,batare da bata lokaci ba ya amsa yasoma rubuta mata yana cewa “idan akwai gaba da gidana kije me ya dameni..
Cikin minti biyu yace “gashi ya miko mata takardarta “na sakeke saki biyu yana gama fadar hk ya mike ya bar parlour’n yana goge zafafan hawayen da suka zowa kuncinsa ,wannan shine karo na uku daya zubar da hawaye akanta Dan tunda yake baitaba jin bacin rai kmr na yau ba yadda ta nuna kiri Kiri bata son zama dashi ,alhalin shiya kamata ya gujeta gashi har yanxu zuciyarsa na tsananin sonta yana fita harabar gidan yakira mahaifinta ya sheida masa daga ya kashe wayarsa da zumar barin kasar a gobe goben nan.
“dady yasoma tsarguwa aKan rashin zuwa safwan gidansa, alhalin yana kasar , amman kiran Gaugauwan da mahaifin sajida yayi masa ya hanashi nemansa a wannan lokacin, yana fitowa mead na fitowa agigice saboda labarin mutuwar auren sajida yasameta atare sukaje, koda ya isa tarin bakinciki ya iske,domin yana xuwa acp ya mika masa farar takarda da sajida ta bashi, yana masa karin bayani “bansan abinda yarinyar take nufi dani ba?
“ta kashe aurenta batare da wani mahimmin dalili ba ,” yanzu emran din ya kirani yake gaya min abinda ya faru sam banga laifinsa ba sai na wannan yar iskar yarinyar, ya dubi gefen inda take rukube yace “ba dai zaman gidan kike bukata ba gaki ga gidan ina tabbatar miki har ki kare rayuwaeki bazaki taba samun miji irin emran ba, tunda dady ya rike takadar yake zabga kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun “amman sajida baki kyautawa rayuwarki ba ke yanzu a tunaninki zaki samu kmr emran? ita dai kuka kawai take har da shesheka “dady ka rokon mun babana ya yafe min dan Allah nasan fushinsa atare dani babbar matsala ce “kinsa da hk kika ki zama a gidanki byn duk abubuwan da suka faru dake ,a wannan zamani wani nmj zai iya hkn?