YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 21 to 30

fad’a sosai dady yayi mata sannan ya bawa acp hakuri da nasiha “akan hk Allah ya kaddaro  babu yadda zasuyi sai adduar, sannan yace tazo ta roki mahaifinta yafiya. 

akan hanyar komawarsu gida “yar baba dady yakirata “na’am babana “kwana biyu sai nake ganin wasu canje canje agame dake sannan safwan baya zuwa gurinki ,fatan  dai lfy? Dan bana son asamu matsala irin na sajida dake. 

tayi shiru tana souronsa batare  datace komai ba har ya dasa ayar  mgnrsa, a zahirin gasky taso gaya masa gdkyr lamari amman ganin zuciyarsa a hannu take akan lamarin Sajida ,tayi  tunanin tabari har su isa Gida.

suna isa gida direba yayi parking atare suka fito tare da dady. 

 “barka da cikar k’arin shrkara ….me’ad ,saitin data jiyo kenan ,wanda yasa ta waigo daidai inda tafi zaton daga nan sautin ya fito safwan tagani tsaye  ajikin motarsa yana mata murmushin mai cike da farincikinki  ganinta, da wasu kayayyakin kyauta gareta ,har da cak ,yakarso gurinsu yana murmushi ya mika mata wannan naki mead yayi mgn yana gaisar da dady cike da girmama”aiko dai  na gode sosai tare da fadada murmushin fuskarta. dady yace “dan albarka mgnrka nake acikin raina ,suka karasa cikin gidan inda sukayi masauki a babban parlour’n gidan dady ya dubeshi “ya baban naka yake yana dai lfy ko? “yana lfy ,tare da kai cup din coffe bakinsa ita km me’ad tana daga gefen hannun kujerar dady”yana Dai kula da sukari ko? “narasa dalilin dayasa ya kasa barin shan sukari gashi yana tattare da ciwo , ga itama wannan hk take kmr sha xumamu  take .

“kai dady yaushe kake barina nasha ,duk wasu abu da suka danganci sukari in dai ba wai baka kasar nan ba mutun yasamu yasha gidanmu ya dawo tmkr sanssani sojoji takarasa mgnr tana me mikowa safwan tiren hannunta “a’a ki ci kawai na gode yayi mgnr idanunsa na kanta  “dady bari na baku guri ina zuwa ta mike tashige ciki  ,inda hira ta barke atsakaninsu har inda safwan ya zayyanewa dady komai dake faruwa fada dady ya rufe shi dashi “dan me zaka min hk?” idan ka daina sonta sai akace kabata damar cigabada soyaya dan talaka dan matsiyata “dady safwan yakirasa “karka damu wallahi ina son me’ad har yanzu, na dai barta ne saboda akwai taku dana shiryawa lamarin kasan yaran yanzu sai da rarashi da dabaru ta hkn ne kadai zamu samu abinda muke so, yanxu ma hk nazo ne mu fita domin tayata murna karin shekarrata,  numfasawa dady yayi duk da yaji dadin rashin janyewarsa amman hankalinsa a matukar tashe yake banda gumi babu abinda ke fitowa daga cikin jikinsa.

 Safwan ya  mike dady sai kajini zamu fita daita yanzu, km Dan Allah karkayi mata zance “dady bai yunkurin cewa komai ba ya fice yacigaba da zaman tunani da mamakin abinda ya faru agurin  ina ai baya jin zai iya  hakura da wannan tashin hankali yana zaune yaji tashin motarsu sannan yasamu ya yunkura da kyar gefen kansa na wani irin sara kmr zai rabe gida Biyu..

Washegari 

Da misalin  Karfe tara na dare ranar ta yiwa fu’ad rakiya ya tafi tana dawowa ta cimma dady, zaune a parlour’n ya zabga uban tagumi yana huci takarasa ta sauke masa tagumi tace “dady’nmu lafiya ka zuba wannan uban tagumin hk? “Har nashigo bakasan nashigo ba.

Ya dubeta sosai da idanunsa  da babu sauki a cikinsu yace  “mead. 

Bata amsa ba illa zuba masa idanu datayi saboda yadda yakira sunan nata cikin kakkausar murya. 

“Waye wancan yaron da kika  raka yanzu? 

Ta sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta sunkuyar da kanta kasa batayi mgn ba saboda batasan abinda mgnr nata zai haifar ba, har da dady ya buga mata tsawa  yace “Dan ubanki ba mgn nake miki ba?

 cikin sarkewar murya tace “dady kayi hakuri  da…daman dady ina son sanar maka ko waye shi, sunansa fu’ad kuma muna son juna dashi dan har mun yanke shawarar yin au….ji kake dau..daun..dady ya dauketa da wani gigitaccen marin har guda uku dayasa ta hantsila tayi bayan kujera tare da ganin wasu taurari sun gilma ta cikin idanunta, take ta nemi ji da ganinta tarasa, dady yana huci yacigaba “yanzu abinda zaki mana kenan?  “Tozarcin dazaki mana kenan? 

“Karamar yarinyar dake kinsa kan mugunta, kina kokarin yiwa iyayenki bakinciki saboda yanzu kina daukar salary mai tsoka “kina nufin bazaki auri safwan ba mai kaunarki da son farincikinki “me wannan tantirin yake dashi wanda yafi safwan? 

“Ke yanzu ko kunya bakiji ba ki rasa Wanda zaki so sai  wannan mai wuyan kmr marakin leman dan talakawa Dan matsiyata?

 Me yake dashi ? “Me zai baki?  Bashi da abinda  zai baki tunda shima bai ci ya koshi ba ,wannan rayuwar kike ganin yayi miki daidai?

 ga mamakin dady sai  jiyo sautinta yayi” ni babu ruwana dady da wani babunsa ,matsayi ko mukami ni shi din kawai nake so,  km ni bakin safwan nake ba, kawai dai bazan iya aurensa bane nabar fuad ,ni dai dady kayi hakuri ka amince na auresa shi zuciyata take so muddin ban  auresa mutuwa zanyi fu’ad nake so  km shine zabin zuciyata”inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yashiga furtawa yana maimaitawa tare da maida idanunsa kan momy da hayaniyarsu tashigo daita da suhailat  momy kuka ta fashe dashi ita da suhailat ganin dady na fada tana fada akan nmj da bashi da tabbas .

dady yace yanzu nufinki bazaki auri safwan ba ko me ? Ni dai kuyi hakuri wallahi banason aurensa “ashe kuwa zaki mutu ashe kuwa lokacin mutuwarki tayi kusa matukar baki auri safwan ba sai dai ki canza uba  ” mayaudariya maci amanar kauna, kin ci amanar safwan ,yaron na yana sonki ba tun yau ba, muryarta cike da shesheka tace “nifa ban ci amanarsa ba amman idan kuna bukatar lallai sai ya auri yar gidan ga suhailat nan kubashi ya aura ,wani marin ya sake d’auketa dashi “kinfi shi ido ne bai ganta ba yace ke yake so shashar banza da wofi  maza tashi kibani guri kafin na tsine miki albarka keda zabin naki  …

kafin ta yunkura yayi wani kwallo daita sai ga ta zube ajikin safwan da shigowarsa gidan kenan, tsam ya rungumeta jikinsa batare daya fuskanci iyayenta ba, hankalinsa yayi kololuwar tashi ganin yadda kamaninta ya sauya hawaye ne suka zubo masa lokacin dayaga nata hawayen na tsiyaya daga cikin kumburarun idanun “haba dady zaka kasheta dan tace bata sona?

 “Shi fa soyayyar d nan baa ayinsa dole dan Allah dady karka sake dukanta akaina nifa tuni na hakura ya fadi hk tare da mikar da tsaye bisa kafafunta “sorry kanwata kukan ya isa hk babu me miki auren dole”Ba dai fu’ad kike so ba? 

 Ta daga masa da kyar “to kice ya turo iyayensa “no no karka min hk safwan ba dai iyayensa ba  sai dai  shi kadan sa tukun , yakarasa mgnr yana juyawa tare da  goge hawaye .

suhailat kuka momy kuka hatta safwan kasa rike kukansa yayi ita kuwa uwar gayya ji take idan duk duniya  nan zasu taru akanta bazata auri wanda zuciyarta bata so ba fu’ad take so kuma shi zata aura.

********

 Bangaren sajida kuwa  babu laifi, ta saki ranta kad’an  banda murnar rabuwa da emran babu abinda take, sai dai  idan ta tuna tarasa budurcinta ,ranta idan yayi dubu yakan  baci, acp na zaune a d’akin baccinsa yana sauraron BBC sajida tashigo  jikinta a matukar  sanyaye tasamu waje ta zauna kusa dashi jigun ranta a dan jagule saboda ganin halin damuwar dayake ciki a dalilinta, kallo daya yayi mata ya dauke idanunsa akanta, sannan cigaban da sauraron BBC, ahankali tasoma magana cikin sanyayyiyar murya” baba kasaki ranka Dan Allah akan yarka, kasamu yakini akaina na maka alkwarin cewar bazan baka kunya baba , ina tabbatar maka babu wani haufi akaina ni kaina nasoma nadamar abunda na aikata …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button