YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 21 to 30

“me kike bukatar daga gareni sajida? 

“Amatsayina na ubanki nafi kaunar ganinki karkashin inuwar aure amman kika watsa min kasa a ido “Mai kike tunani duniya zatace akaina dake karon kanki? 

 

“Ina dai rokonka baba kayi hakuri ka kasamu yakini acikin zuciyarka akaina ni bazan sake baka kunya ba….ko fushin karya ma bana iyawa dake driya tayi sosai  sannan ta mike ta bar d’akin cike da matsanancin farinciki mara misaltuwa . 

Mmn sudais ce

????????????????????????

       ‘YAN CINKI

      ????????????????

????????????????????????

             ~NA~

 *AYSHA  A BAGUDO*

~DEDICATED TO~

      MRS ADAM

( YAR MUTAN KAGARA)

Page 59 to 60

Not edit

……..Sajida ta nufi d’akinta ta fad’a kan gadonta  cike da matsanancin farinciki ji take tmkr tasamu fu’ad tagama , tunani ne ya fad’o mata a rai ta mike zumbur tayi bathroom tayi wanka, ta  canja kaya zuwa wasu hadaddun kananan kaya, riga da siket blue da dan ratsin yellow,tasanya abaya ta yafa mayafi  ta fito ,she look very attractive parlour’n kasa ta sauko adaidai lokacin da motocin mahaifinta suka bar gidan,sai aunty nadiya  mai aikin da’aka samo musu ce a tun sanda aurenta ya mutu a zaune ,sajida batayi mata magana ba sai ita aunty nadiyar ce tace, dining fa ya kammala .

“No karki damu aunty,zan fita ne but yanzu zan dawo takarasa mgnr idanunta na  ga duban agogon bango parloun dake walwalin haske kwan fitila ya sake kara haskawa, karfe 12 na safe yanzu ta wuce, aunty nadiya tace sai kin dawo. .

kai tsaye motarta tashiga ta nufi gidansu misna, kmr koda yaushe momyn misna tana kitchen tana aiki domin akwaita da kaunar girki, wanda hkn ke sata tuno da amminta sam itama hk take da son girkin tsiya dan wani lokacin babanta kance “Kyan ‘ya tagaji uwarta amman ke sam baki d’aukota a komai ba…

Ita kuma sai tace masa” ai shi ta gado tunda ba asan nmj da shiga kitchen.  ba…

ta gaidasheta kana ta nufi dakin misna straight ,akwance ta tarar daita tana kallo a zeey world misna naganinta ta mike zaune da murnarta ta rungume sajida  ajikinta tana jin dadin ganinta cikin koshin lfy bakamar kwanakin baya ba, itama sajida ta rungumeta tana jin dadi aranta, tana matukar jin dadin yadda misna ke nuna mata kauna sajida tace “wani guri mai mahimmanci nazo ki rakani “a tunanin misna ko gurin shakatawa zasu kasancewar tasanta da son zuwa irin wuraren.

 da azama misna ta diro daga kan gadonta tare da daura after dress akan riga da wando datake sanye dashi domin fitowarta wanka kenan , tare suka fito misna na rolling mayafin after dress akanta umman misna tace “sai ina adaidai wannan lokacin?  

Sajida tace “umma fita zamuyi amman yanzu zamu dawo, umma tace ” karfe 1 ta kusa kuje kuyi sallah sai ku zo kuyi lunch sannan rana ta fara yin sanyi sai ku fita, babu musu suka bi umarninta suka koma d’akin sukayi sallah sannan suka ci abinci Wanda sama sama sajida taci dan ta matsu bata isa inda zuciyarta ke bukatar zuwa ba,

 sun fito suna yiwa umma sallama tace “karsu dade .

tafiya suke ahankali sajida ke jan motar muryarta a raunane sajida tace “kawata baki tmbayeni inda zamu ba ?

“tambayar mai zan miki byn nasan wata killa wajen shakatawa zaki. 

“No kin sa’ba tsaitin tunaninki ,domin kuwa ba nan zamu ba ,kina jina ko a watanin baya da suka gabata kin sha ganina cikin tashin hankali da damuwa wanda kowa ke bukatar son sanin abinda ke damuna alokacin, amman naki bada wannan kofar  ,sai dai a yau zuciyata ta aminta da nasar miki da damuwata ,bisa aminta da zuciyata tayi dake, me’ad itace wacce tafi cancata tasan matsala fiyye da kowa a duniya, sai dai al’amarin damuwata ya danganceta..kina saurarata kuwa?

“Ina jinki sajida sai dai maganarki tasanya kuzarin jikina yin rauni .

“karki damu da furucina nasanki, nasan halinki da zurfin ciki duk wuya duk runtsi akayi sirri dake baza ta’ba jinsa akoina ba shiyasa nasanyoki cikin abinda yashafi sirrikan rayuwata.

Taja numfashi ahankali ta fitar tana mai karya kwana wanda kai tsaye inda tasan fu’ad yake zama tare da abokansa ta nufa daga nesa kad’an da gurin tayi  parking ta tsura masa idanunta sosai kmr zata fixgosa gareta, yana zaune tsakiyarsu kabeer suna hira wanda ba kasafai yake sanya bakinsa ciki ba.

 kallonsa kawai take bata ko kifta ido, ga wani irin kalar murmushi datake masa wanda ita kanta batasan tanayi ba balle wanda ake dominsa, tsawon lokaci tana zaune tana kallonsa taji an hura mata iska a idanunta, tayi firgigib ta dawo haiyacinta tana duban misna  dake zaune a gefenta ,” misna a yau nake son shearing wani abu daya danganci rayuwata dake “waye wancan dake zaune tsakiyar maza uku din can sanye  da t shirt fari da bakin wando?

tayi mata tmbyr tare da d’auke idanunta akanta ta maida kan fu’ad da bai san wainar da’ake toyawa ba .

Ahankali misna tace “Idan dai har idanuna nagani kmr yadda nayi zato fu’ad din me’ad ne zaune…….

“yauwa yar gari sai dai kinyi kuskuren kiransa da fu’ad din me’ad ne ,kice fu’ad din mai raboz saboda shine mutumin da zuciyata ta kamu da matsanancin kaunarsa, shine mutumin daya hanani walwala da sukuni, shi mutumin da tuaninsa ya dusashe tarin soyayyar emran acikin zuciyata ,har nake ganin duk mazan duniya mata ne shi kawai ne tsayayen nmj… “what ..kina mafarkine sajida?

“Idan mafarki kike maza ki farka “karki manta halakar dake tsakanin iyayenku daku kanka, “meyasa zakiyi hk sajida?

“Gsky banji dadin furuncinki ga abinda aminiyarki take so tmkr ranta ba ..”nasani misna amman ya na iya da rayuwata, me’ad ce silar faruwar komai “itace ta nuna minshi daga kallo dayan dana masa narasa gane kaina,”yanzu dai ki taimakeni ta yaya kike ganin zan mallakesa shine abinda nafi bukata daga gareki?

Naunayen ajiyar zuciya misna ta sauke da karfi “azahirin gsky ni banida wani taimako da zan iya miki daya wuce kiyi hkr ki hakura dashi domin shine zaman lfyarmu da kwanciyar hankalinmu kafin mead tasan da wannan zance.

 “haba haba sam wannan abu baiyi min dadi ba,aminan juna daku kuna son abu daya…….”ki hakura dashi sajida ,a gsky banji dadin yadda kikace saboda shi kika kasa zama da emran ba domin emran masoyinki ne na hakika wanda samun irinsa ke wuya .

“shawara nake bukata daga gareki bawani zance emran ba ” matukar shawara kike bukata daga gareni ki cire soyayyar fuad acikin ranki ki fawwalawa Allah komai shi yasan yadda zaiyi da al’amarinsa ,babu mamaki akwai manufar da Allah yake nufi daku ,da har yasa kuka kamu da son mutun daya, mutun dayan kum wanda ya kasance bakowa ba face talaka …

Sajida ta daina sauraron misna ta meida hankalinta sosai gurin cigaba da kallonsa har sai dataji zuciyarta tasamu natsuwar datake bukata sannan taja motarta ta gabansa suka  wuce amman bai san ko su waye ba kasancewar glass din motar baki ne, ta sauke misna a gidansu sannan ta koma gida cike da tunanin misna. 

“An  kuwa zata iya rabuwa dashi?

“idan ta rabu dashi tayi yaya da rayuwarta?

“kenan rayuwarta zata zamo abar tausayi babu emran babu shi babu budurcinta…… ina da  sake. 

Zuwan fu’ad biyu amman me’ad batayi kokarin sanar masa da sakon mahaifinta  ba ,yanzu ma tsaye suke a harabar gidansu tayo masa rakiya motocin  safwan suka sanyo kai cikin harabar gidan, tundaga nesan daya hangosu kirjinsa ke bugawa har zuwa sanda suka isa inda aka tanada domin ajiye motoci ,bayan an yi parking,ya yunkura da kyar yasamu ya fito sanye  cikin riga da wando sai yar saman suit dake saman farar  longselve, ya kirkiro  dariyar dole  yakaraso zuwa inda suke alokaci daya zuciyar  fu’ad data safwan ta buga rasssssss atare batare da suncewa juna komai ba sai me’ad ce ta bud’e baki tana murmushi “fu’ad ga yayana safwan….safwan yayi saurin runtse idonsa sbd zuciyarsa dake na wani irin harbawa kmr zata fasa kirjinsa dan ji yayi kmr an diga masa ruwan dalma, sannan  ta juya ta kalli safwan tace “yaya safwan ga fu’ad Dina….ahankali ya bud’e idanunsa ya daura akan fu’ad daya tsareshi danashi idon kana jiki a sanyaye suka  mikawa junansu hannu domin gaisawa ” mlm fu’ad ya gida da aiki? 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button