YANCIN KI Page 21 to 30

“Lfy fu’ad yace atakaice saboda ganin irin kallon kasan dayake masa mai had’e da maxurai da rainin wayo da murmushi ahad’e.
Hannunsu na sarkafe cikin juna safwan yace “gsky kanwata kin iya zabe …”allah ko yaya? “Kwarai kuwa…da gaske, kin kuwa gaya masa sakon dady ?
Numfashi taja ta sauke da kyar kana tace”Abinda nake shirin yi kenan kashigo “ok kiyi kokari ki sanar masa idan da wata matsala ki hanzarta sanar min “ok yaya na gode da kulawarka .
“No karki damu kanwata any for you ya juya zuciyarsa na farfasa, ya nufi cikin gidan kmr zai kifa tsabar duhun da zuciyarsa tashiga har yayi dayasanin zuwansa gidan bayansa fu’ad ya tsurawa idanu duk bai jiyo ba yana iya ganin yadda numfashinsa ke fita da karfi.
byn shigarsa cikin gidan fu’ad yayi mugu mugun tsareta da ido “kikace wannan mutumin yayanki ne ?
“eh tabashi amsa tana kallon cikin idanunsa.
“Uwa daya uba daya?
” no D’an aminin kuma mai gidan dady ne,”wani abu ne ?girgiza mata kai kawai yayi “yanzu dai kaji da kunnenka dady nason ganinka ya kenan?
“Ok badamuwa zuwa yaushe yake son ganina?
“anytime you are free ,”ok mubarshi nest week saboda gabadaya satinan zanyi busy kema bazaki samu damar ganina ba har sai nagama abinda nake, jin hk yasa ta narke masa fuska kmr zatayi kuka “har next week fa kace , kasan kuwa yadda nake ji idan nayi kwana daya ban sanyaka acikin idanuna ba ?
“Ji nake kmr ana fixgar numfashina ni dai kasan yadda zakayi, ko kazo ko sau biyu ne naganka ,ko kuma ni na sameka inda kake.
Murmushin yayi sannan yasoma rarrashinta sai daya samu ta dawo normal sannan ya wuce.
Kwanakin nan gbdy acikin kunci da damuwa mead tayisa sakamakon rashin ganinsa Dan hk randa yazo da zumar ganin mahaifinta tana ganinsa bata tsaya wata wata ba ta rungume shi ajikinta tana farinciki ,saurin d’auke numfashinsa yayi saboda jin diran nonuwanta bisa kirjinsa atare sukaji tmkr
Wani irin abu yana masu yawo a gabadaya ilahirin jikinsun me kama da shocking wanda take ya haddasawa nata kirjin bugawa yayinda shi km a take kwakwaluwarsa ta d’auki caji , cikin wani irin murya yace ” my love you kinzo min da wani irin salo mai tsayawa a zuciya, kar da kisa nayi abun kunya a gidan siriki, a yadda yayi maganar bakaramin rud’ata yayi ba ….jin yanayinsa nason canzawa yasashi zareta ajikinsa yana fitar da wani irin numfashi da kyar da sauri ta ita kuma ta fita daga cikin parlour fuskarta cike da fara’a, itama wani irin kalar numfashi take ,a yanzu ji take ina ma amatsayin mallakinsa take.
“tun bayan fitarta fu’ad yafara jin caji ajikinsa, ahankali yake jin wani feelings na bijirowa a gangar jikinsa ,lips dinsa na kasa ya ciza da matukar karfi kmr zai datse harshensa, sannan yayi saurin batsar da abinda yake jin yana masa yawo ajiki kana yacigaba da zaman jiranta.
Cikin wasu yan mintunoni da basu wuce biyar ba ta sake dawowa karamin parlour’n dayake zaune zaman jiranta “taso muje zuwa ga babban parlour’n dady inda anan dady zai ganka ,bakinsa d’auke da sallama yashigo cikin hadadden parlour’n ,inda suka iske parlour’n empty babu kowa cikinsa sai k’aran tv plazma dake manne da bangon parlour’n yana aiki acikinsa hannunsa ta kamo zuwa kan kujera “ka zauna yanzu dady zai shigo, gyaran murya yayi mata batare da yace komai ba illa idanunsa dake yawo a sansar jikinta, ta juya cike da rausaya ta nufi cikin gidan tana daddana number safwan kira daya ya dauka “ya’akayi ne kanwata?
“kazo yanzu ga fu’ad yazo dan Allah nafi son duk abinda za’a yi kana nan domin nasan zakayi controlling din dady . Tunda tasoma mgn numfashinsa ya nemi dauke amman yayi saurin sanyawa jikinsa jarumtar cewar”ok karki damu gani zuwa just give me some mint.
byn kmr minti 30 sai ga dady yashigo parlour’n yana dingisawa fu’ad naganinsa yayi saurin mikewa tsaye cike da girmamawa yana mai gaishe dashi “uhm kawai dady ya iya cewa sannam ya zauna tare da cewa “kana iya zama.
fu’ad ya Zauna zuciyarsa na d’ardar dan ganin yadda mahaifin me’ad ke kallonsa kasa da sama wanda hkn yake nuna alamun bai yaba da ganinsa ba .
yayinda me’ad tasake dawowa parlour’n tare da tsayawa a bakin kofar shigowa ta tsurawa fu’ad ido dady ya yi gyaran murya kana yace “me za’a kawo maka?
shayi ko lemo ko… “no no dady ba sai an kawo min komai ba ,nagode “uhmm kasha wani abu mana kai kuwa ?
cike da in ina fuad yace “to ruwa ma kawai ya isa .
“ruwa fa?
mahaifin me’ad ya fad’a yana jinjina kai .fuad yace eh shi kawai ya isa.
kai kuwa “ya zakazo gidan masu abun kace ruwa kawai zaka sha any how mead kawowa bakonki abinda ya bukata ta juya, jiki a sanyaye ta nufi kitchen dan sam bataji dadi irin tarban da dady yayi masa ba, byn fitarta dady ya fuskanci fu’ad yana tsare idanu tun kafin yasoma magana safwan yashigo cikin parlour’n cikin sallama sanye cikin kananun kaya wad’anda suka mugun amsar jikinsa sai kamshi dadden turarensa yake bazawa ya gaishe da dady sannan yakarasa ya mikawa fu’ad. Hannu”barkanmu da warhk?
Shima fu’ad Hannu ya mika masa suka gaisa sannan ya samun guri ya zauna shima yana fuskantar fu’ad , yasanya hannunsa daya yayi tagumi yana cigaba da kallon fu’ad “me yafi shi har da me’ad ta zabesa ta barshi?
kyau ilimi tattare makudan kudaden da shi kansa bai san adadinsu ba, duk yafi wannan dake zaune a gabanshi..
“a ina kake da zama sautin muryar dady ta karade parlour’n zuwa cikin dodon kunne fu’ad “ina zaune a gbegulori dake kan titi capito road “uhmm anan kake zaune tare da iyayenka?
“eh ana nake tare da kakata dan tun daga haihuwata mahaifiyata ta rasu byn wani lokaci shima mahaifina ya rasu yanzu dai ina tare da kakata nake zaune.
“ayya ina mai jajanta maka Allah ya jikansu.
“Ameen na.. na gode dady. Cikin hk mead tashigo ta ajiye tire dake dauke da nauikan abinci ta juya tanayiwa safwan alamar ya taimaka komai yazo karshe sannan tabar gurin.
Dady yacigaba”da dukan alamum kakarka tana riritaka dayawa ?
fu’ad yayi muushin jin dadi tare da sakin jikinsa kad’an dan da adirice yake ,sannan yace azahirin gsky hk ne Sabod tana matsananci sona sosai “ya isa me kakeyi ahalin yanzu aiki ko karatu?
“gsky babu abinda nake ahalin yanzu ina dai kan neman aiki a tun bayan dana gama digri Dina Amman har yanzu ban samu ba shiyasa na yanke shawarar soma sana’ar kasuwancin..
“idan na fahimci maganarka baka Da aikin yi, kai mutun ne dakayi karatu amman baka da tsayayen aikin yi, safwan kana ji fa da sanar da bai kai ga samu ba yake neman diyar babban gida ko dai baiyi karatun bane?
“a’a dady digre gareni nasan zuwa yanzu nasan abinda kake son kace amman na rantse maka da Allah zan kular maka da me’ad sosai fiyye da yadda kake tsammani “uhm kace kayi karatu geo ko history ka karanta? “aa kasuwanci na karanta zaka iya kallon abun wani iri Amman muddin me’ad na tare dani kusan babu abinda bazan iya mata ba, ko maye zanyi domim na bata farinciki da…..
“ya isa hk malam dady ya katseshi yana mazurai da “Karka cikani da wannan surutain banza da wofi “meye matsayinka? “kai fa ka kasance yaro ne mara zuciyar neman na kansa wanda kakarsa ke ciyar dashi tare da bashi kudin kashewa, yayi gantali yayi can yayi gantali yayi nan rayuwar kenan wadan nan takalman da kayan jikinka da machine din dakazo dashi da kudin wa kasiya? mu dubi komai a zahirance mana sannan musa gsky a hurumunta mana “ta yaya kake tunani zan dauki diyata me’ad nabawa mai matacciyar zuciya irinka?