YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 31 to 40

Najma tayo hanyar waje tana ihu inda shima Fu’ad ya biyota ya riketa gam sai ga Sajida tashigo gidan a matukar firgice takaraso Me’ad ta tsaya tana haki wallahi sai na kasheki …..

cikin kidema Sajida ta sake motsosu zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu take tambayar Me’ad abinda ke faruwa “sajida nashiga uku wai agabana Fu’ad yake rokon wannan yarinyar da ta taimaka ta aureshi.

 “ke Me’ad Sajid ta furta da k’arfi jikinta na wani irin rawa zamuyi mummunar sa’bawa dake, ta yaya zaki dubi wannan abar kice Fu’ad d’ina danake burin mallaka matsayin miji zaice yana sonta wannan maganar ma ai karyace wallahi bazata’ba zama gaskiya ba, takarasa mgnr cikin daga murya …..

tunda Sajida tasoma mgn zuciyar Me’ad ta tsaya cak ta daina aiki na wunci gadi sakamakon sakon da kunnuwana suka jiyo mata daga cikin bakin Sajid, idan dai kunneta ba karya ya jiyo mata ba fu’ad dinta taji ta furta cikin yanayin na tashin hankali “to me hkn yake nufi itama sonshi take ko shine yake sonta kmr yadda yake son auren najma?

 kusan minti goma tana tsaye jikinta na kyarma har lokacin tsaye kawai take bisa kafafunta babu wani wadatacen numfashi dake kai kawo ajikinta har sanda taji sautin muryarsa cikin kunnuwanta suna mata kuwa “kina mamaki jin abinda tace ko? 

“kina mamakin jin furucinta ko akaina ? 

“tabbas nasan zakiyi mamaki jin hk , har zuciyarki tayi kokari tsayawa ta daina aiki.. “kwanakin baya na tab’a gaya miki wata mgn alokacin da kika fasa wayata nace “idan kikaji wace nake waya daita zuciyarki zata buga sabida tashin hankali abun..to bakowa bace wace muke waya daita adaidai wannan lokacin face aminiyarki Sajida dake tsaye agabanki ayanxu , babu daren da zai zo Sajida bata kirani ba sannan babu garin da zai waye Sajida bata kirani ba sakoninta kuwa basu kirguwa acikin wayata domin son mallakar abinda yake mallakinki wanda ke , kike k’ok’arin bazantarwa bisa wani bazan dalili naki , gata nan ki tambayeta batace tana sonta ba , zata ajiye aikin da ke kika gagara ajiyewa dan dai kawai ta aureni gata nan ..

“Kin raina albashina Amman ni ban rainasa ba har ina yunkurin kara aure har biyu dashi..

Me’ad ta juyo zuciyarta kmr zata tarwatse ta fito daga cikin kirjinta, jikinta ne dauki rawa kar kar idanunta Kan kallon Sajid.

Sajida ta kalleta ido cikin ido tace “tabbas gsky fu’ad ya fad’a miki tunda muka had’u dashi a wancen lokacin naji ina mutuwar sonshi wanda Allah ne ya jarabeni da sonshi ada na boye amman a yanzu bazan iya boyewa kowa irin son da nake masa ba.

  cikin rawar murya Me’ad tace “so fa kikace Sajida me yasa zaki min haka? “Ki rasa Wanda zaki so sai mijina? 

“na aminta dake kece mafi kusancin abunda na yarda daita a duniya na kuma aminta daita “why why why sajida zaki min hk “so fa kikace kikayiwa fu’ad anya kuwa kina cikin haiyacinki? 

“anya cutar hauka da mantau bata kama kwawaluwarki ba da zakice kina son mijina fu’ad? “Cikin kuka ta matso kusa daita tare da kamo hannuta”kice karya ne sajida bakya son mijina..

“Ta yaya zance banason shi aminyata?

“Alhalin ina son mijinki fu’ad so kuwa me tsansni son da ni kaina bazan ce ga daga inda ya fara ba balle insan inda zai tsaya, ina sonshi bazan ji shaka ko shayin furta shi akoina ba ko gaba kowaye saboda so ba karya bane, kuma bazan miki karya ba wallahi ina son fu’ad mijinki so na hakika wanda nake fatan zai kai mu gayin aure..

 “sajida me’ad ta furt da karfi tana dafe kirjinta tare da furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun cikin matsancin damuwa sannan ta juyo tana fuskatsrsa idanunta cike da ruwan hawaye tace “da gaske ne abinda kunnuwana suke ji ayanzu “dan Allah fu’ad kace karya ne bakason yarinyar nan da tun sanda na fara sanyata cikin idanuna naji na tsaneta fiyye da komai sannan ka karyata min kallamar wannan maciya amanar abota ….

“uhm duk ina sonsu kuma aurensu zanyi kmr yadda na aureki ,aduk abinda ya faru kece silar faruwarsa”wallahi fu’ad bazaka ta’ba auren wannan yariyar ba haka zalika bazaka auri wannsn maci amanar ba takarasa mgnr tana juyowa tare da damk’ar wuyan sajida “mijina sajida mijina kike so?

” daman abinda ke ranki kenan shiyasa kullun kike hanyar zuwa gidana da sonji halin dayake ciki …….?

“shiyasa kullum kike adduar samun miji irinsa ta a she sonshi kikeyi ta d’auketa da wani gigitaccen mari wanda yasa taga gilmawar wasu taurari ko numfashi sajida ta gagara yi yau zan kasheki so that nima na hakura da duniyar gabadaya.

 a gigice fu’ad yayi kanta yana kiran sunanta “wai kin haukace ne ko me da zaki dinga neman kasheta “eh na haukace maciya amana kawai sai Allah ya saka min na barku da fitowar Rana da faruwarsa .. ..

ta sake dauke sajida da wani Marin gabadaya tagama birkicewa kallo daya zaka mata ka tabbatar da cewar bata cikin hankalinta ta wujijiga sajida da karfi wacce gabadaya numfashinta yagama tsayawa ,tsaye kawai take bisa kafafunta ,sannan tayi wani irin jifa daita , sajida tayi luuuuuuu zata fad’i kan dutse cikin zafin nama fu’ad ya banbare najma dake makale ajikinsa ya kai hannunsa zai tarota ,a matukar tsawace tace “kar …….kar ta ‘bata fu’ad Wallahi idan ka sanya hannunka ajikinta zan aikata abinda sai kashiga uku …. cak ya tsaya jikinsa na rawa. Yana kallo Kan sajida ya bugi da dutse kara daya tayi bata sake motsawa ba .

Ta wawuri wukarta da subuce ta rike gam kana tace “ke kuma karamar yar iska tayi mgnr da iyakacin karfinta har sai da najma ta zabura ta zura aguje tsabar tashin hankali data riski kanta ciki .”tsaya Dan ubanki tambayarki zanyi kafin na yankaki da hanuna, kuma kinsa idan na yankaki na yanka banza saboda babu abinda za’a yi kasancewarki mara galihu, ina son ki gaya min yaya kike jin mijina aranki kema kina son shi ne kmr yadda wannan sumammiyar ta fad’a….?

Najma tayi saurin girgiza kai idanunta cike da ruwan hawaye “ki bud’e baki stupid ki gaya min kina son mijina zaki aureshi kamar yadda yace “wallahi tallahi aunty banason shi ko kad’an Dan bamu dace da juna ba 

Ni iyayena talakawa ne Dan haka zan auri irina bazan ta’ba auren mijinki ba duk runtsi ..

“yi min shiru Dan ubanki munafukar Allah kasheki zanyi in kuma kikaga ban kasheki ba to kwanakin ne bai cika ba tana gama maganar ta zabura ta sake yin Kan najma rike da wukar tayi mata yanka yafi biyar a hannunta Amman Dan azabar naci take rike daita sai alokacin fu’ad yayi karfin halin daka mata tsawa da cewar “kawo wukar nan tunda naga abun naki ya zama iskanci ga wata kin sumar kina kokarin kashe wannan ,yana mgnr yana takowa zuwa inda take tare da kokari son kwace wukar hannunta “fuad kada kazo wajena Dan kai nayi nufi ba wannan munafukar ba zan kashe kowa a huta Dan bansa amfanin badi babu rai ba bata sauraresa ba ta sake nufar najma cikin zafin rai ta sameta a gefen kafad’a ai kuwa nan da nan jini yasoma zuba.

 fu’ad yayi saurin dosar wajenta bai tsaya wata wata ba ya fixge wukar yayi jifa daita saman zink sannan ya wanketa da wani mari ta fashe da kuka tare da durkushewa kasa bisa gwiwowinta ” Dan abinda ya faru daita ko acikin mafarki bata ta’ba zaton zai faru ba fu’ad yayi mata wannan cin fuskar akan wasu banzaye ahankali cike da matsanancin sanyi jiki yakarasa gareta inda take durkushe tana kuka yasanya hannuwansa duka ya d’agota yana share mata hawaye, rungumeta yayi ajikinsa tsam yana Dan dukan bayanta Amman ina kuka take sosai , yayinda har lokacin sajida ke kwance sume akasa babu alamun numfashi atare daita ,cike da bakinciki mara misaltuwa tasoma kokarin barin jiknsa “fuad ka cuceni ka cuci rayuwata , “me na maka dana cancanci wannan wulakanci da tozarcin ?”yar aikina da aminyata kake yunkurin aure alokaci daya..”duk Akan aikina wanda shine rufin asirinmu …”am really sorry love I didn’t mean to hurt you Amman…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button