YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 31 to 40

“Banason jin komai daga bakinka daman ka gaji dani har kana wulakantani tare da yunkurin sakina, am ready for it now “ka sakeni domin zanfi bukatar saki akan na zauna ka auri wannan abar da tare da wannan maci amanar “bazan iya sakinki ba me’ad da zan sakeki da tuni a wuce gurin ni dai plz ki natsu ki dawo haiyacinki koda ban auri sajida ba kibarni na auri najma bawai ina son yarinyar bane hk kawai take bani tausayi..

 suman tsaye tayi agurin jikinta na sake d’aukar rawa kmr wace aka jona mata wutar lantarki idanunta sukayi wani irin canzawa “dont don’t repeat it coz it’s not possible, how can this possibly ka auri wannan to ka kaita ina bakagani fu’ad juya ka kalleta up and down she’s not your type Amman tunda zuciyarka ta aminta bari na aunata barzahu takaraso inda najma ke tsaye tana kirma tana gama karasowa ji kake tasssss tassss saukar mari dama da hagu tasoma neman abinda zata buga mata. idanunta ne ya sauka akan wani karfi wanda duka daya idan tayiwa najma dashi tabbas zata tashi aiki .

gadan gadan tayi gurin karfin ta d’auka fu’ad yayo kanta “plz me’ad karki buga mata…..

gocewa tayi bata bari ya kai hannunsa jikinta ba , da sauri ta nufi Kan najma daidai lokacin da direban nasreen yasanyo hancin motarsa cikin gidan idanunta ya sauka akan abinda momy’ta ke shirin yi da sauri tun direban bai gama daidaita motar ba ta sanyo kafafunta waje ta kwaso aguje tana “furta momy karki buga mata plz ai bata gama rufe bakinta ba me’ad ta daga karfen sosai da iyakacin karfinta zata bugawa najma..

 nasreen ta tsaya cak tare da rufe idanunta saboda tsoro ta saki wata razananniyar kara sai gata tana kokarin yin kasa da sauri me’ad ta saki karfen hannunta wanda a sauka akan kafar najma itama ta saki kara har da fitsari. 

aguje me’ad da fu’ad sukayo Kan nasreen fu’ad ne yayi nasarar isa gareta ya tallafota zuwa jikinsa ya rungumeta yana kiran sunanta, itama me’ad jikinta na rawa take kok’arin amsarta daga hannunsa “barmin yarinyarta karki k’arasa kashe min ita ……..

Mmn sudais ce

????????????????????????

       ‘YAN CINKI

      ????????????????

????????????????????????

             ~NA~

 *AYSHA A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~   

FAIZA HAMMADU BARAU 

         (YAR NUMAN)

Page 76  

…….. wani irin k’ara ta saka tare da d’aura hannuwanta duka saman kanta “shikenan tawa tasameni nasreen Dina zata mutu tabarni ….”wayyohlly nasreen ki taimaki mamanki ki tashi karki ki mutu kubarni cikin wannan halin damuwar danake ciki ,idan kika mutu wazan kama naji dadi? “wayyohlly Allah,”nashiga uku nah … “help me to carry her to hospital this man, ka tashi ka wani zauna kana kallonta saboda kasan idan ta mutu baka da hasara zaka kuma samun madadinta ni kuwa fa wazan kama…?

a rud’e fu’ad ya d’auki nasreen da bata numfashi ya sa’bata akafad’arsa yasoma tafiya daita cikin sauri sauri, me’ad ma ta mike azumbur ta biyosa abaya rike da gefen rigarta tana wani irin kuka me ta’ba zuciya.

A haukace ya isa inda motarsa take parke ya bud’e gidan baya ya kwantar daita, me’ad tayi saurin shiga ta d’aga kanta ta zauna ta meida kanta saman cinyarta tana wani irin kuka jikinta banda kirma babu abinda yake ,shi kuma ya zagaya cikin sauri yashiga gaban motar ya zauna ya kunna motar yana mai danna hon da karfi ……..

me gadin gidan da tun sanda rikicin yasoma faruwa akan idanunsa yashige d’akinsa ya boye ya leko ta window, ganin motar fu’ad ne yayi saurin fitowa ya bud’e masa get sannan fu’ad ya figi motar aguje ya bar gidan .

wani irin gudu yake shararawa akan titi wanda yaja hankalin mutane dayawa kansa ,domin duk wanda yaga irin gudun dayake sai ya tsaya yabi bayan motar da kallo, cikin lokaci kankani ya isa asibiti tun bai gama daidaita tsayuwar motar ba me’ad ta fito jikinta na rawa tana ihun kiran nurse….nurse!! shima ya fito a kid’ime batare daya tsaya rufe motar ba, ya sake d’aukar nasreen dake kwance babu alamun numfashi atare daita.

 sautin muryar me’ad yasa 

wasu daga cikin likitoci fitowa da hanzari suna tura gadon marasa lfy domin sunsa duk me irin ihun nan hk a matukar bukace yake da taimako,batare da ‘bata lokaci ba aka kwantar da nasreen.

 kai tsaye d’akin likita aka nufa daita aka akwantar daita akan gado sannan aka soma bata taimakon gaugawa ,likitoci kusan guda biyar ne suka rufa akanta domin k’ok’arin dawo da numfashinta ,wanda da kyar aka samu numfashinta ya dawo daidai sai dai bata farka ba. 

Yayinda fu’ad da me’ad gabadayansu sun fita haiyacinsu ,sai zariya suke suna kai kawo a reception, most especial me’ad da hawaye yaki tsayuwa acikin kwarnin idanunta, kuka take sosai kmr wace akace mata tarasa nasreen din, ahankali fu’ad ya waigowa gefen datake zariya tana kuka ya tsura mata ido yana duban yadda gbdy ta gama birkicewa ta hargitse ta dawo abar tausayi ,matsalarta kenan a duk sanda nasreen ke cikin wani hali gbdy zata rasa sukuni da kwanciyar hankali Amman ta zauna domin kula daita da lfyr ce bazata iya ba …

ahankali ya d’auke idanunsa akanta had’e da Jan tsaki… shi kansa cike yake da matsanancin fargabar abinda likita zai fito ya sanar musu,cikin hk suka hango fitowa wata nurse daga d’akin da’aka kwntar da nasreen ,gbdy sukayo kanta “how is she?

 suka furta atare cike da matsanancin tashin hankali? 

“she’s feeling better now ta basu amsa atakaice cike da tausaya musu sannan tacigaba da mgn “doctor is already attending to her, Dan haka kusamu natsuwa ku kwantar da hankalinku InshaAllahu babu abinda zai faru da yarinyar ku…..”you said doctor is with her inji cewar fu’ad?”haka ne likita nabata kulawa just keep praying for her, everything will be fine okay.

sannan ta barsu tashiga wani d’akin opposite dinsu.

 suna nan tsaye ta sake dawo ta wucesu cikin sauri tashige d’akin .

me’ad ta k’arasa jikin bango ta d’aura kanta tana wani irin kuka …, sai alokacin abubuwa suke dawo mata daki daki , “sajida aminiyarta, aminiyar datafi yarda daita a duk cikin aminanta, wai itace yau aka wayi gari take son mijinta har take burin mallakar aurensa, wannan wace irin cin amana ce …?

“Sajida kin cuceni kin ci amanar yarda da amince dana miki ,kin cuceni kin yaudareni, kin ha’inceni.. Amman nasan Allah bazai barki haka ba ,da yarda Allah sai allah ya nuna miki illar cin amanar wanda ya aminta da dake , matukar yarda da na miki ta tsakani da Allah ce sai Allah ya nuna miki atafin hanuna, saboda daidai da rana daya ban ta’ba tunanin zaki yi min hk ba ,na yarda dake kin cutarda dani …na aminta dake kin ha’inceni “me na miki kika za’bi ki min haka? 

“Duk duniya ki rasa wanda zaki so sai mijina..kuka take sosai tana maganar ashe har maganar ta fito fili batasani ba .

 Tausayinta ne yashiga ratsashi ,da bin lungu da sako na sansar jikinsa , jiki a sanyaye yak’araso zuwa inda take ya kai hannunsa ya dafa kafad’arta, da sauri tayi wata irin juyowa tana kallonsa cike da zallar tsana da ‘bacin rai sannan ta cire hannunsa tayi jifa dashi “karka sake kai hannunka jikina mayaudari maci amanar kauna…….abinda ta iya fad’a kenan ta bar gurin zuwa harabar asibiti tana kuka kmr wata zautaciya…” yau tazo mata da abubuwa daban daban wanda kowane daga cikinsu akwai d’aci da muni gareta, mijinta ke son me aikinta da aminiyarta…. alhalin tana raye bata mutu ba wannan abu da matukar ciwo ..”why fu’ad ?”ban cancanci hk daga gareka ba ,bansa zaka min haka ba ,Amman tunda wannan shine besty solution dakake ganin zaka d’auka akaina I will live you for them wallahi na hakura da kai nabar musu kai ta karasa mgnr tana kuka ahankali ta durkushe kasa tare da d’aura kanta saman gwiwowinta tacigaba da kuka …..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button