YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 31 to 40

Can gidan kuwa najma taci kukanta kmr ranta zai fita da kyar tasamu ta yunkura ta mike tsaye tana d’ingisa kafarta da k’arfe ya saukar mata kai, tasoma tafiya jikinta na karkarwa ,kai tsaye hanyar cikin gidan ta nufa inda tashiga ta d’auki kayanta kwaya daya dake cikin bakar leda ajiye, har lokacin hawaye take sharewa ita bakincikinta bai wuce yadda zatayi da rayuwata ba ,domin a matukar tsorace take da halin data ga me’ad din take ciki , gara ta gudu tun bata dawo gidan ta kasheta ba , kmr yadda tayi niyya ba.

 ahankali ta fito harabar gidan inda idanunta ya sauka akan sajida dake kwance kmr gawa, nan da nan hankalinta ya sake tashi sai lokacin ta tuna yadda akayi take kwance cikin wannan halin, girgiza kanta tayi tana takaicin hali irin nata nacin amanar aminiyarta datayi, ta isa inda me gadi yake tsaye tare da direban nasreen yana labarta masa abinda ya faru akan idanunsa, ta nuna musu inda sajida ke kwance”ku taimaka mata Dan Allah karta mutu mushiga uku ,duk da ni dai tafiya zanyi yanzu .

sai lokacin hankalinsu ya kai gareta ai kuwa da sauri me gadi yaje dibo ruwa shi kuma direba ya isa gareta yana dubanta atsoroce, daidai lokacin da me gadi ya kawo ruwa tuni najma ta fice daga gidan .

Ruwa suka zuba mata sosai sannan ta sauke ajiyar zuciya da karfi dishi dishi take kallonsu kanta na jujjuyawa had’e da sarawa kusan minti goma da kwara mata ruwa ta dawo haiyacinta sosai tana sake dubansu dafe da gefen kanta “ranki ya dad’e wai me ya had’aki da hjy ne har hkn ta faru atsakaninku?”gsky zan so ki tashi ki fice daga gidan nan tun kafin ta dawo ta sameki tak’arasaki. maganganunsa tsab suke shiga cikin kunnenta , ahankali tasoma mikewa har ta mike tana bin bango tare da cewa direba “ahuwa taimaka ka kaini gida dan Allah, bazan iya tuki ba … da sauri ya zaro duka idanunwansa waje “wa ni zan kaiki gida ranki ya dad’e?

Ta d’aga masa batare datace masa komai ba “a’a wallahi bazan iya ba ,,Dan idan hjy ta dawo tasamu labarin ni na kaiki gida kashina ya bushe ,ki dai lalla’ba kija kanki shi zai fi miki alkairi .

Sororo tayi agurin tana kallonsa da mamaki , me’ad kenan jarabar duniya kowa tsoronta yake ji tayi maganar acikin zuciyarta “ita me’ad tayi yunkurin kashewa Akan d’a nmj, nmj da zai iya rayuwa babu ita aduniya. Nmj da tabbas garesa balle alkwari yanzu inda takasheni fa me take tunani zai faru?”ita ba matsiyaciyar me aikinta bace daba gata da galihu bace balle tayi tunanin idan ta kasheta ta kashe banza. 

Tafiya take ahankali tana zance zuci har ta iso inda motarta take tashiga ta zauna tana jin yadda gefen kanta ke cigaba da sarawa, wayarta ta d’auka takira direban gidansu ,cikin minti goma sai gashi ya iso yana rusuna mata cike da girmamawa tace “ya kai ta asibintin da take zuwa …

**********

Sai gurin takwas din dare nasreen ta bud’e idanunta tana wani irin kukan bakinciki, nurse ta shigo d’akin cikin sauri ta ajiye karamin tiren hannunta wanda ke d’auke da kayan aiki akan table tare da janyo wani flat table gaban gadon nasreen wace tana ganin shigowar nurse ta d’auke kanta ta meida gefe tana cigaba da kukanta .

nurse ta meida tiren kan flat table had’e da sanya safar hannu nasreen ta juyo gefenta hawaye na bin kuncinta “nurse ta kirata muryarta na rawa “I don’t want to see you don’t come near me plz ,I don’t want to see ….

nurse ta bud’e baki da hanci tana dubanta kafin daga bisani tace “ki bari nayi treatment dinki mana ,amatukar tsawace nasreen ta mike zaune “go I don’t want to see you, sannan ta koma ta kwanta tana Janyo numfashi da kyar. 

“What’s wrong with you nasreen?

” bakiga halin da kike ciki ba, kina bukatar kulawarmu,

Kibari na dubaki mana ….

“please, go!

Ihu kawai take tana furta go “I don’t want to see likita ne ya fad’o cikin d’akin da sauri yana tambayr abinda ke faruwwa “doctor I wanted to treat her,but she asked me not to touch her, nor come close to her .

doctor yayi shiru yana duban nurse din sannan ya meida idanunsa Kan nasreen dake kwance tana kuka har da shesheka ,”ammm ya fad’i hk tare da k’arasawa gadon da nasreen take ya tsura mata ido kawai yana kallonta gbdy ya kasa cewa komai.

 yarinyar na mugu mugun bashi tausayi lamarinta na ta’ba zuciyarsa ,waigowa yayi tare da cewa nurse “you can go. 

“Ok sir ta fad’a tana cire safar hannuta kana ta bar d’akin .

Doctor ya matso tare da tura table din dake d’auke da magani gefe sannan yasamu guri ya zauna daga gefen kafafunta yana kare mata kallo ahankali ya kira sunanta “nasreen, you will be fine, okay? 

“Ammm permit me to take of yourself I will treat you by my self and you will be fine is that clear?

Ahankali ta waigo hawaye nabin kuncinta tace ” doctor all i want from you is to kill me ,”give me poison ,i just want to die ,I ,i heter my self banason cigaba da wannan rayuwa ,ina bukatar barin duniyar nan ….sororo doctor yayi tare da bud’e idanunsa yana cigaba da kallonta kirjinsa na wani irin bugawa saboda jin lafazinta “abun mamaki yarinya karamar irinta ke furta wannan kalmar ..

tana son tasha poison ta mutu to akan me kenan ?

 “Ina son na mutu doctor bana bukatar cigaba da rayuwa a duniyar nan ta sake maimaitawa tana kuka…. 

Cike da matsanancin tashin hankali ya furta kalmar “death.?

“Yes doctor I want to die….ta juyar da kanta…

“What ?

Ya sake furtawa yana dubanta a matukar tsorace , kasa tashi doctor yayi daga cikin inda yake zaune illa dubanta da yaciga da yi tare da rafka tagumi .

Shiru shiru me’ad na jiran ganin fitowar likita Amman shiru hkn yasa ta nufi d’akin din da gudu tana kuka shima fu’ad cikin sauri yabiyo bayanta, gbdy kallo daya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta, tunda suka zo asibitin batayi yunkurin komawa gidan ba , “to idan ma ta koma tayi me ?

” ne zata koma tayi a wannan gidan ?

Haka tayita zariya acikin asibitin har zuwa wannan lokacin, sannan bata kira kowa daga bangarenta ba ,Dan har gara fu’ad ta lura da yaje gidan ya dawo, Amman ita zuwansa ba damuwarta bace, damuwarta ahalin yanzu bata wuce ta lafiyar tilon diyarta ba . 

Zaune suka iske doctor ya tasa nasreen gaba yana dubanta, da sauri tayo gurin nasreen tana kiran sunan “doc……

AI kuwa nasreen ta zabura ta mike zaune tare da dakatar da uwar ta hanyar cewa “go back mummy I don’t want to see you, plz go !!!! Shi kansa doctor sai dayayi shock a zaune agurin,wannan abinda me faruwa gaske ne ko mafarki ne ?

A matukar firgice me’ad da fu’ad suka shiga kallon kallo atsakaninsu suna zare ido. da kyar fu’ad yayi karfin halin cewa “did you hear her? Yana kallon kwayar idanun me’ad. 

“Did you hear what she said? 

Runtse idanunta tayi hawayen bakinciki biyu biyu na gangaro mata, magana take son yi Amman ko tace zatayi maganar bazata fito ba saboda cikin halin tashin hankali datake ciki ,Dan haka ta bud’e idanunta dake cike da ruwan hawaye ta d’aurasu Akan yarinyarta tana mata kallon karta mata …..

 Hawaye sha’be sha’be a kwance a kuncinta nasreen ta sake cewa “I don’t want to see any of you here, Plz just go…

doctor ya d’ago ya dubesu yana girgiza kai sannan yace “fatan kunji abinda yarinyarku tace ? 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button