YANCIN KI Page 31 to 40

tana cikin wannan halin fu’ad ya fito yana dube duben nemanta can ya hangota zaune takure da jikinta tana kuka .
ya runtse idanunsa sannan ya k’araso inda take ya tsaya akanta “mead ya kira sunanta da sanyayyiyar murya “me yasa kika barni kika dawo nan kina kuka? Wannan karon Yayi mgnr muryarsa cike da tausayawa sannan ahankali.
Ya matso sosai kusa daita tare da durkusawa agabanta “why did you left me there and weeping outside ?
Bata kula shi ba tacigaba da kukanta tana goge hawaye, wasu na sake gangarowa ya sake matsota sosai kmr zai shige jikinta, “don’t do this to me plz ,the doctor has promised us that she will be fine let’s keep praying for her, after all ,we are not god dole mujira hukuncin Allah garemu …
ya kamo laulausar tafin hannuta cikin nasa “dan Allah ki natsu ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameta “am..am scared I don’t want lose her takarasa mgnr tana mai sakin wani irin kuka ..
ta kwanto jikinsa tana kuka yanyota yayi jikinsa ya rungumeta tsam ya manna fuskarta daidai saitin zuciyarsa dake bugawa, yasoma rarrashinta “you are not going to lose her ,okay? ” InshaAllahu zamu rayu tare da diyarmu, ki daina kawo mata mutuwa, Dan zamu iya mutuwa mu barta babu ruwan Allah.
Cikin halin datake ciki , ta tuno da abinda yake son shuka mata, ai batare da ‘bata lokaci ba ta fixge jikinta daga nashi ta Mike tsaye tana kallonsa kafin daga bisani tasoma tafiya cikin sauri tana kuka ,shima ya biyo bayanta yana kiran sunanta “mead ina zaki, ki dawo idan gida zaki na kaiki. tayi masa banza tacigaba da tafiyarta har takarasa bakin titi tana kokarin tsaida abun hawa “karki soma me’ad..karki soma shiga kowace mota.
“Zan shiga so that idan na shiga ka sakeni ,wanda daman abinda nafi bukata kenan daga gareka tana fad’ar hk ta juya a fusace daidai lokacin da wani me adaidaita ya tsaya agabanta yana tmbyr inda zata.
Tun kafin ta bud’e bakinta fu’ad yayi saurin cewa “ka wuce kawai tare muke daita, idan km kayi k’ok’arin d’aukarta sai dai wani ba kai ba ,yakarasa mgnr ya kamo hannuta da niyyar komawa cikin hospital, tasoma turturjewa” kabarni fu’ad banason abinda kake min, “me yasa kake son kasheni tun kwanakina basu cika ba ..?
“Kece kike son kashe kanki da kanki ,amman karki damu bazaki mutu yanzu ba ,har sai kinga aurena da matana guda biyu.
“Ina ai bazan so ki mutu tun yanzu ba matata, kece fa kikace am your husband for life, har tsufa muna tare ko kin manta da kin furta hkn ?
“Ki tuna idan kuma kin manta gashin na tuna miki,aurena da ‘yammatana babu fashi ,zance saki sakanina dake babu shi ,Dan HK muje kisamu natsuwar zuciya.
Ta tattara iya karfinta ta fixge daga rikon da yayi mata ta juya cikin sauri tayi tafiyarta ,sai dai taku daya zuwa biyu yayi ya damketa tare da yin sama daita jama’a kan titi da idanunsu ke kansu suka bisu da kallo, har sanda ya sanyata cikin mota shima yashiga ya kule yana me fuskantarta.muryarsa a matukar sanyaye yace “Keleni me’ad, sannan ki natsu kibani aron hankalinki muyi mgn ta fahimta .”matukar Akan zance aurenka ne bazan ta’ba fahimtarka ba ,ince ba’ayin aure dole?”Dan Allah dan Annabi ka rabu dani da nace ina sonka zan rayu da kai yanzu kuma banayi kaje byn sajida da najma ka k’ara wasu ,ni dai me’ad ban sake komawa aurnka Allah ya had’a kowa da rabon…bata k’arasa ba taji ya buge mata baki “idan kika sake furta wannan kalmar zan zaki had’u da fushina da baki ta’ba ganin ba ,yanzu dai mu ajiye komai har sanda nasreen zata samu lfy aure kuma babu fashi zanyi ,let me tell you good news, ki godewa Allah watakila najma kawai zan aura saboda mahaifin sajida yaki amincewa da batun auren ..tunda yasoma mgnr take kuka har yayi shiru,tana zaune ta dawo tmkr mutun mutumi ,jinta na neman d’aukewa ,Allah sarki a she hk rayuwa zata zo mata?
Ganin hankalinta na neman gushewa yasa ya matsota ya kamo hannuwanta duka cikin nasa yasoma massaging dinsu yana kallon cikin kwayar idanunta dake tsiyayar hawaye, Yasan tana mugu mugun son shi ,sannan yana da tabbacin duk duniya babu macen dazata so shi fiyye daita ..ahankali ya janyota jikinsa yana k’ok’arin rungumeta ,ta kasa saida shi saboda zuwa lokacin gbdy jikinta bai da laka kallonsa kawai kmr wata ta’ba’bbiya ,tsawon lokaci suna manne da juna batare da suncewa juna k’ala ba ,kusan a mota suka kwana makale da juna, sai dai mead bata runtsa ba kwance kawai take ajikinsa numfashi kawai take iya fitarwa shima Dan tasan dole ya fito tunda akwai rai ajikinta.
******
Washegari babu laifi nasreen tasamu natsuwar zuciya, daman firgici da tsoro ne ya haifar mata da suman datayi , sai dai fad’uwar datayi kasa yasa hannunta na hagu ya D’an bugu, har gurin ya kunbura abinka da sickle cell k’ashinsu bashi da kwari, koman yaya suka ji ciwo yanzu gurin zai kunbura. suna zaune tare daita kowanensu na rike da hannunta daya ,suna k’ok’arin bata kulawa doctor yashigo dubata yanayin jikinta, sosai ya ji dadin yadda ya isketa atsakiyarsu me’ad na bata apple abaki sannan tayi mata hira, irin sanya farinciki.
Tashi sukayi atare suka tsaya ajikin bango, batare da sun kalli junansu ba,doctor yashiga aikin duba jikin nasreen yana mata wasa.
Kwana nasreen biyu a hospital doctor yabasu sallama, lokacin fu’ad bai nan yana can tare da me gidansa, kai tsaye me’ad hanyar gidansu ta dauka da nasreen, Dan bata jin zata koma gidansu da sunan cigaba da rayuwa fu’ad, zuciyarta cike da bakinciki, wai shin me zatawa sajida da najma arayuwa ta huce?
Kodayake bata jin najma, tafi jin sajida Dan a yanzu ta sauya shawarar akanta ,Dan har in takashe sajida, bata more rayuwa ba ,tunda bata zauna a duniyar ba balle taga bakinciki, yanzu tafi yarda da shawarar zuciyarta wanda babu tantama abinda zata mata har ta mutu sajida bazata ta’ba mantawa daita ba,gaba idan ance ta kalli mijin wata tace tana so ,ko taci amanar wanda ya Aminta daita bazatayi ba ,murmushin mugunta tayi adaidai lokacin da ta iso bakin get din gidansu inda tashiga matsa hon, madu gadi na ganin motarta ce suka hau k’ok’arin bud’ewa cikin rawar jiki, tasanya hancin motarta tana hura hanci, tayi parking a inda aka tanada domin ajiye motoci sannan ta fito har lokacin fuskarta a murtuke take, ta dubi nasreen dake zaune tana kallonta, dan ita a tunanita gidansu suka nufa sai kuma taga momy’nta tayo gidan kakaninta dasu, me’ad ta Dan saki fuskarta kana tace “bby fito muje …
*”Uhmmm to ga dai me’ad an kwaso jiki an dawo gida uba…ko yaya zatak’aya da mahaifinta ?” ko kuwa ta manta furucinsa akanta ne?*
[ad_2]