YANCIN KI Page 31 to 40

ta tsaya shiru tana duban kofar sannan ta tura tashiga ciki ta iske shi gaban mirrow yana balbale sauran botiran gaban rigarsa”fuad takira sunansa “karkamin haka wallahi na tuba karka kara aure me kake son nayi maka ka gaya min am ready for it, zanyi amman karka min kishiya ,banason kishiya,saboda na tsani sharing din duk wani abinda nake so .
yayi mata banza yacigaba da abinda yake zai shige bathroom tayi saurin riko hannunsa cikin nata hawaye kwance acikin kwayar idanunta ” fu’ad Dina da inna karka min haka Dan Allah bazan iya ba I can’t take it ……
“Kayiwa darajar Allah da inna ka yafemin abinda nayi maka, sharrin sheid’an ne dana zuciyata..
Ya fixge hannunsa a fusace ” innar da kika meida kmr tissue, kullun kika tashi iskancinki akanta kike karewa…bama wannan ba karki damu rayuwata plz.. “ai kin daina sona shiyasa kike wulakantani ,to kibari masu sona su shigo suyi min abinda nake bukata .
durkushewa tayi agabansa tana kuka “waye yace maka na daina sonka ..?
“wallahi ina sonka kai kanka kasan wannan ranar bazata zo ba ,bana ma faran ranar da zan daina sonka, kai ne dai ka daina sona tunda gashi kana kokarin kasheni tun kwanakina basu cika ba “ka gaya me kake son nayi maka ?
“Zan canza wallahi zan dinga baka had’in kai a shimfid’arka sai yadda kayi dani ,komai kake so zanyi maka wallahi bazan sake sa’bawa umarninka ba ….
Kuka take sosai tana rokonsa .
Jin kukan na ta’ba masa zuciya yasashi runtse idanunsa tare da cewa “naji kin fad’i komai baki fad’i batun ajiye aiki ba, ok shi fa tare aka halicceki dashi ko bazaki iya ajiyewa ba?
“No karkace hk honey wannan aikin nawa shine rufin asirimu ni da kai da tilon diyarmu kamin uzuri, “ni dai kayi hakuri dan Allah am really sorry for what I did…
Bai ce mata komai ba yashige bayi ya barta durkushe yana shiga ya sakarwa kansa ruwa, kafin ya fito ta kwashe kayan daya cire ta nufi washing room dashi sannan ta sake dawowa d’akin inda ta iske ya fito sanye da jallabiya “muje kaci abinci “a koshe nake….
“honey…… yaushe rabon kaci abincina ?
“Ka daina cin abincina ka daina mua’mula ta aure dani gbdy kokarin cireni kakeyi azuciyarka ,ka taimaka fu’ad nasan nayi …plz ki takaita mgnrki hk ina bukatar hutu kina iya fita plz……
tsimi tsimi kmr baita ba ta fito daga d’akin ta nufi nata d’aki tana rike da kugunta tashiga zagaye d’akin”komai fa yana neman tsaya min ni me’ad,” yanzu me yakamata nayi na dawo da mijina hannuna? Ina bukatar shi banason rasashi ,ya Allah ka taimakeni karkasa fuad ya juya min baya..
” ko sajida zan kira ta bani shawara akan wannan sabon lamarin dake shirin kuno kai cikin gidana “no no bana tunani zata iya min magani wannan matsalar .
“Ke kanki ki zauna kiyi tunanin zaki iya shawo Kan matsalarki inji cewar zuciyarta gbdy ta kasa zama hawaye take sosai damuwa tayi mata yawa ga matsalar gurin aikinta data rasa dalilin dayasa idan tashiga office dinta take jin zafi ajikinta ga matsalar rashin lfyr nasreen yanzu kuma ga abinda fu’ad yake son Bullo mata dashi..”ya rabbi ka taimakeni …
***********
Shiru yana zaune a inda tabarshi yana tunanin abubuwan sa suka faru tsakaninsa da sajida, sosai lamarin ke bashi mamaki da daure masa kai “wai yau shine ya sha bakin wata mace ,macen ma aminyar matarsa , ya Jima zaune abun na ta’ba zuciyarsa, lamarin ya maseefar tsaya masa arai, ahankali ya Mike ya fito daga d’akinsa yana cigaba da tunani zai aureta ne kmr yadda me gidansa ke bukata ko kuwa zai dojewa aurenta ne ?
Yana fitowa ya ga wulgawar najma ta nufi d’akin nasreen bai ga fuskar yarinyar ba ,sai bayanta ya hanga doguwa ce Amman ba can ba ,kad’a kansa yayi sannan yashige kitchen coffee ya had’awa kansa ya fito rike da cup din yana kur’ba har yak’araso parlour’n ya zauna tare da d’aukar remut ya kunna tv ya canza channel zuwa CNN yana zaune har 12:00 dot kuma har lokacin zuciyarsa ta kasa samun natsuwa, ya sake mikewa yashiga d’akinsa yana shiga ya iske wayarsa na kara yakarasa cike da sanyi jiki ya d’auka yana duba screen din wayar wata number yagani wace bai Santa ba da kmr bazai d’auka ba saboda bai cika d’aukar wayar da baisani ba Amman dai zuciyarsa ta umarceshi daya d’auka
Mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
Page 73
…….Sautin muryar sajida yaji ta doki cikin dodon kunnenshi, Wanda hakan ya saukar masa da jin wani yanayi na daban sakamakon tuno moment dinsu na dazu, goshinsa ya Dafe yana me Jan dogon tsaki tare da furta “matsala……..
Bangarenta itama naunayen ajiyar zuciya ta sauke lokacin dataji sautin muryarsa sai dai taji haushi abinda ya fad’a ,Amman sai kawar da hakan ta kwantar da muryarta sosai tace “na ta kuraka ko ?
“Am really sorry nima banso hakan ta kasance ba ,na kasa bacci ne sakamakon tunaninka daya addabi ruhina, shiyasa kaga kirana a daidai wannan lokacin,but kai me kakeyi da bakayi bacci ba har yanzu…?
Tayi masa tambayar tana sake kamkame wayar a kunenta tana jin is like suna makale da junansu ..
Fu’ad lumshe idanunsa yayi yana jin wani sabon yanayi a game daita wanda bai San ko na mene ba ,yana bin ilahirin jikinsa tare da kaiwa kowani shashi na gangar jikinsa ziyara , yayinda duk wata kafar gashi dake kwance ajikinsa suka soma mikewa,ahankali har suka mike duka , ya furzar da iska me dumi ta bakinsa “wai meke damuna ne ?
Ya tmbyi zuciyarsa yana shafa sumar kansa sannan yasamu guri ya zauna daga gefen gadon yana bud’e idanunsa , cikin murya me cike da kasala yasoma kira sunanta “sajida …..meye matsalarki dani dakike kok’arin shiga rayuwa?
“I think na gaya miki ki fita harkata ina son matata and bazan iya kara wani aure a halin yanzu ba ,kuma ko auren zanyi not you sajida saboda gbdy bakya daga cikin tsarin matar danake so ….dan hk tun wuri ina umartarki da ki bar rayuwata plz tun tunanina bai soma canzawa akanki ba.
Pillow ta janyo ta manne akirjinta ,tana yadda zuciyarta ke wani irin beting fastly “me yasa kake nacin na bar rayuwarka fu’ad a halin ina sonka fiyye da komai a duniya ?
” me yasa baka sona fu’ad?
“Na mallaki duk wani abinda cikakken nmj yake bukata daga kyakkywar mace ,why why da bazaka soni ba fu’ad..?
“tabe baki fu’ad yayi kmr yana gabanta sannan yace “ina ruwana da wani kyawunki ,wallahi idan za’a jeramin dubunku ba abinda zanyi daku saboda matata fiki komai danake bukata, sannan ba kyau akeyiwa ba ,hali akewa, wallahi in dai nace miki kin tsarinki yayi min zan aureki nayi miki karya sajida , kawai saboda babu kyau wulakanci ne yasa kikaga nake raga miki, domin duk wanda yace yana sonka yagama maka komai arayuwa, to be your last warning sajida da zaki kirani arayuwarki saboda banason hkn sannan bana bukatar mu’amula dake…..
“Haba fu’ad me yasa kake min haka ko dan nace ina sonka….?
“Exactly…abinda kika fad’a haka ne ,saboda kince kina sona yayinda ni kuma bana bukatar hakan ,zanso ki fahimta hakan azahirance , saboda idan kika lura ni dake bamu dace ba duba ga yadda kuke da matata,sannan Baki min ba Dan hk ki barni na karashe sauran rayuwata da matata bana bukatar wata sabuwar matsala ayanxu so Dan Allah kiyi hakuri ki janye kudirinki akaina ni yanzu ba soyayya bace a gabana ..