YANCIN KI Page 31 to 40

cikin fushi da bacin rai daba San lokacin daya dira acikin ranta ba tace “haba fu’ad Dan nace ina sonka, ta yaya arziki na binka kake gudu?
“KaSanin bazan ta’ba neman Abu ban samu ba balle abinda zuciyata ta kwallafa rai akai na Jima ina dawainiyya da dakon soyayyarka ,ina sonka kuma sai kazama nawa saboda. Babu ruwana da wata matarka ko dangantar dake tsakaninmu ,bugu da kari dan dady na yana min abinda nake so ,ahalin yanzu babu abinda yafi bukata kmr yaga nayi aure tunda nayi bika ta lallami kaki to zakaga abinda zan biyo baya sbd dole kazama mallakina….
Shima a matukar fusace yace “kin dad’e bakiyi fushi ba ,kuma wannan abinda kikayi yanzu yana cikin abinda yasa bazan so ki ba, idan kina takama da kudi ko wani abu ,to ni banida komai
, ke dadynki ne gatanki ni kuma Allah ne gatana shi zai tsaya min a dukkan lamurana, sannan shine bai doramin sonki ba da ina sonki sajida zan iya aurenki to banasonki ….dan hk karki sake kirana akan wannan banzar issue din ya k’arasa fad’ar hk yana katse kiran ya cillata saman gado ya juya ya kwanta flat tare da dafe goshinsa.
Tsaki taja “har ni zance ina sonshi yaki amincewa, duk da kyau’n da Allah yayi min ga tarin kudi?
“Me matarsa tafini dashi dayake wulakantani akanta ?
“Ai kuwa duk abinda zai faru sai dai ya faru Amman sai na aureka fu’ad koda kuwa zaka mutu byn na aureka……
*********
Daren ranar tarihi ne ya sake maimaita kansa Domin daga me’ad sajida fu’ad duk babu wanda ya runtsa acikinsu kowa da tunani dayake har garin Allah ya waye Dan har gara ma ta kwana yin nafilfili ne …..
*******
Tunda najma tazo gidan take yin abinda ya kawota, tare da kaffa kaffa da kanta ,Dan tasha jin labarin me’ad agurin yayarta ummi, Sam bata da mutucin ga masu aikinta duk kankatar laifi zata iya tozarta mutun akansa, gashi batasan darajar mutane ba acewarta ,shiyasa abinda aka kawota dominsa shi takeyi ,sosai take bawa nasreen kulawa tare da janta ajiki dan har yarinyar ta fara sabawa daita, yau takama ranar asabar , ta tashi da wuri domin killace gidan duk da baya daga cikin abinda ya kawota gidan, sai data share koina ta gyara tazo inda me’ad ke zaune tana tura sakonni a system dinta, sanye cikin wata hadaddiyar Riga da wandon jeans , tayi maseefar kyau cikin kayan sai kamshi ne ke fita ajikinta sam bazaka ta’ba cewar itace ta kawo nasreen duniya ba ,yayinda nasreen ke gefenta zaune tana zuba mata shagwaba iri iri .
Takaraso nesa kadan dasu tare da gaisheta cike da ladabi ,bata ko kalli inda take tsugune ba balle ta amsa mata tacigaba da aikin gabanta.
Najma cikin bakinciki da takacin wanda bata da ikon magana tunda Allah yayi abincinta a wajenta yake dole ta sawa zuciyarta hakuri har ranar da Allah zai yaye mata ahankali tace ” nasreen tashi muje ki sha magani ..”kawo mata nan me’ad tayi mgnr atakaice batare data dago ba.
Nasreen kuwa d’aura kanta tayi a saman cinyar mamanta tana zuba shagwaba “momy…..
“Yes baby what did you want?
“zanci indomi wit egg..
“Sai ki tashi kije ki soma dafa mata abinda ta bukata ko, ta kuma jifanta da wannan maganar atsawace cikin isa da nuna ita din wata ce me iko Akanta….
Najma ta mike ta tashi duk jikinta yana rawa tayi wajen aiwatar da ,abinda uwar d’akinta ta sata ta fito barandar gidan anan taci karo da wani kyakyawan mutun matashi wanda ba sai an gaya mata ba ,tasan mijin aunty ne Dan haka gwiwa biyu ta durkusa har kasa tace “ina kwana…
Fu’ad yayi kuri da ido yana kallonta cikin tsananin mamakin ganin wannan kyakkywar yarinyar wace shekarunta bazasu wuce shabakwai ba amatsayin me aiki ,sosai ya tsura mata idanunsa cike da tausayawa yasan babu da rashi irin na talauci ne ya haifar da hakan gareta, “Allah sarki rayuwa azahirin gsky talauci bai yi ba ,bai sani ba kodan ya fito daga tsantso talakawa ne yasa yake mugu mugun tausayawa talaka ….
Ita kam kallon da yake mata ne yasa jikinta d’aukar rawa ta mike da sauri ta bar gurin ta nufi d’akin da me’ad ta nuna mata tun farkon zuwanta gidan ,cikin sauri tashiga store ta d’auki indomin data kaita ta sake dawo cikin rawar jiki da sarsarfa a hanyar suka kuma cin karo da fu’ad wanda ke tsaye a wajen data barshi.
Shi kuwa bayanta yabi da kallo yana ta kallonta duk tausayinta ya cika masa zuciya, Da irin rayuwar data samu kanta ta babu, wanda har yasa take aikatau agidan mutane Dan su samu rufin asiri ..
Tana tsaye acikin kitchen din tana dafa indomin zuciyarta harbawa tare da hasko fuskar mijin uwar d’akinta ,tunda take bata taba ganin halittar data d’auki hankalinta alokaci daya ba kmr shi ,ya had’u sosai babu karya ,duk macen data ganshi taga cikakken njm, ahankali damuwarta ke juyewa zuwa farincikin dabasan dalilin faruwar hkn ba .
Bayan najma tagama dafawa nasreen indomi ta kawo mata har inda suke zaune da me’ad ,ta janyo center table ta d’aura mata sannan ta nufi d’akinta cikin sauri ta kwaso magungunanta ta dawo ta raku’be agefe tana jiran tagama tabata magani , tana nan har tsawon minti talatin tsayuwar jiranta, saboda itama nasreen kmr yanayin uwarta gareta gurin cin abinci ,ana ci kmr ba’a son ci,tana kallonta ta ture plate din gefe alamun takoshi sannan cikin rawar jiki ta nufi dispenser ta tara cup ta tsiyayi ruwa ta dawo tasoma balbale magani ta miko mata cikin rawar jiki Dan batason tayi kuskure agaban uwar d’akinta.
nasreen ta ‘bata rai sosai tana turo bakinta Dan tasoma gajiya da shan magani saboda makoshinta na mata zafi a duk lokacin da zata sha ,” najma bazan shan maganin nan yanzu ba ki bari zuwa anjima am so tired with it..
da sauri najma ta sake matsota “ki d’aure kinji nasreen an san shan magani da wahala amman d’aurewa ake kinji nasreen din ummanta….
me’ad tayi jimmmm Tare da barin abinda take ta D’an juyo ta saci kallonta sannan ta d’auke kanta duk da batason yarinyar sai dai taji dadi sosai da kulawarta ga tilon diyarta.
“amshi ki sha kinji nasreen din ummanta …..
Ta sake girgiza mata kai da kyar dai da rarrashi da komai ta samu ta lallabata sha sannan ita kuma ta tattara magungunanta tayi d’aki dasu.
ta dawo ta d’auke plet Wanda zuwa lokacin me’ad ta bar parlour’n zuwa d’akinta da waya manne a kunneta .
Har zata koma ta zauna kusa da nasreen sai Ta samu kanta da son sake ganin fuskar kyakyawan mijin aunty…
Ahankali ta isa bakin barandar tana lekensa tana waigen bayanta gudun kar me’ad takamata tana kallon mijinta , tana tsaye tana sake tsintar kanta cikin matsanancin farinciki mara misaltuwa, “kai mutumin nan ya had’u fa kmr wani balarabe , anya ma bai had’a jinsi da rabawan asali ba kuwa ?
Tayiwa zuciyarta wannan tambayar tana murmushin jin dadi “kai wasu dai sun marewa rayuwar duniya “shi da matarsa da yarsu masu shegen kyau duk da yadda mutane suke zuzuta nata kyau,ganinsu family din gidan yasa ta raina nata, Dan ko kama kafar nasu kyawun batayi ba ,”ina ma za a had’a?
haka tayita zance zuci tana murmushi kmr wace akayiwa albishiri da samun gidan aljannah.
cikin haka me’ad ta dawo parlour’n ,inda idanunta ya sauka akan najma tana kalle mata fuskar miji batare daya sanin tana tsaye ba..
Gabanta ne yayi wani irin bugawa yashiga dukan uku uku me zata gani yau kuma ?