YANCIN KI Page 31 to 40

“Ba dai mijinta take satar kallo ba?
” inna lillahi wa inna ilaihi rajiun tashiga furtawa acikin zuciyarta gabanta na sake dokawa, yayinda ahankali tashiga d’aga kafafunta zuwa inda najma ke tsaye tana cigaba da kallonsa ,me’ad nagama karasowa bata tsaya wata wata ba ta damki bayan wuyanta batare da tace mata uffan ba ta nufin hanyar karamin parlour daita, sannan ta sakar mata wuya tare da ingizata tana aika mata da wani irin mugun kallo a kaskance, wanda take hanjin colin najma tasoma cakudewa ta hau mazurai jikinta na rawa ,take tayi saurin durkushewa kasa ta dukar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannuwanta tana jiran jin abinda zai fito daga bakin uwar d’akinta .
adduar take aranta Allah yasa bata kamata tana kallon mijinta ba, kafin kace tuni gumi yashiga tsatsafo mata zuciyarta na bugawa kmr yadda na me’ad ke harbawa ,tsawon minti goma najma na durkushe Amman Dan tsabar wulakanci me’ad bata ce mata komai ba ,baya ga idanun data tsareta dashi Wanda ita najma take jin kmr ta tashi ta zura aguje tabar gidan.
sai data gama kallonta a wulakance sannan ta yatsina fuska tace ” ke Dan ubanki me yasa kike kallon mijina?
“na kawoki gidana Dan ki dinga kallon mijina ne?
“Ko daman abinda ya kawoki kenan ki dinga satar kallon mazajen mutane yasa kike yawon aikatau agidajen mutane?
Tayi mata tmbyr tana zabga mata uwar harara. Najma tayi saurin d’ago kanta tana girgiza mata kai ..
“Aiki na kawoki kiyi min ba kallon mijina ba … ?
“Lalura ce yasa nace akawoki min ke Dan ubanki domin ki dinga kula min da yarinyata, Ba wai kishiga hurumin gidana ba Dan I can’t take this nonsense, shara wanke wanke da sauran ayyukan gidan bance kimin ba, kinsa kanki ne non of my business Dan bakurtuwa bace ni zan iya abina , ni dai magani kawai nace kibawa yarinyata akan kaida tare da bata kulawar datace while kudin aikinki kuma momy ce zata dinga bawa iyayenki Dan haka banga dalilin da zai saka ki dinga labe kina kallon min miji ba ko kina son shi ne?
Da sauri Najma ta d’ago ta kalli me’ad cikin mamaki jin furucinta ,”yanzu ita tunaninta kenan ita har ga Allah bawai sonshi take ba ya dai mata kyau ne kawai yasa ta kalleshi .
A matukar tsawace me’ad tace “me nene kikayi saurin kallona, ko karya nake miki ba kallon mijina na kamaki kinayi ba ?
Najma ta sunkuyar da kanta cikin fargaba “wayyohlly Allah ka ceceni meye kaini kallonsa gashi najawo kaina tozarci..?
“Dan ubanki daga yau na sake ganin kin la’be kina kallon min miji sai na miki dukan mutuwa sannan na tattaraki na aikawa iyayenki da ragowar gangar jikinki stupid kawai yara kanana daku sai jarabar iskanci tsiya ,yanzu ma kisawa ranki ba kisamu gidan zama ba ,at anytime zan iya gargad’anki kibar min gida wawiya shasha kawai maza ki tashi ki koma dakinki banason ganin wannan shegiyar fuskar taki..
najma ta tashi duk jikinta yana rawa “kiyi hakuri Dan Allah..
Wunin rana cikin damuwa me’ad ta wuni tana tunanin, ita ba abun ta kori yarinyar ba ace bata da hakuri tacika maseefa,if not da wallahi bazata sake kwana mata agida ba, rarrashin zuciyarta tayi sosai sannan ta dan dawo daidai ….yayinda najma bata sake gangancin kallon fu’ad ba hatta hotonsa dake manne da parlour’n gidan bata kuskuren kallo, da zarar taga shigowarsa take barin gurin, gbdy a matukar tsorace take da matar gidan.
********
Shi kuwa fu’ad tunda yasanya najma a kwayar idanunsa yarasa meke damunsa ,shi dai haka kawai take bashi tausayi yana zaune yana tunanin rayuwa da yadda sajida take fautarsa babu dare babu rana duk inda yayi tana biye dashi wata rana har gidan take biyosa tayita satar kallonsa da zarar idanun me’ad zai kai gareta sai tayi saurin d’auke idanunta .
yana cikin wannan tunanin ne yaji sautin muryarta “ina yini abban nasreen tayi mgnr tamkar yadda me’ad Kan kirasa wani lokacin, Yayi Firgigib alokacin da har taje bakin kofar shiga kitchen.
“Zo nan fu’ad ya fadi hakan cikin sanyayyiyar muryarsa me matukar dadi da kashe jkin wanda ya saurara, sannan yacigaba zo nan ki zauna …
Najma tayi saurin juyowa ta kalleshi cike da matsanancin mamakin tana nuna kanta gabanta na wani irin faduwa ,ya d’aga mata gira tare da cewa “kizo nan dake nake karki damu kanwata tamabaya nake son miki in dai bazaki damu ba
Mmn sudais ce
????????????????????????
‘YAN CINKI
????????????????
????????????????????????
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)
page 74
…..sunkuyar da kanta tayi kasa sosai ,sannan ahankali tasoma takowa zuwa inda yake zaune xuciyarta na wani irin luguden bugu da karfi sakamakon idanunsa dataji suna yawo a gbdy sansar jikinta.
har tak’araso kanta na sunkuye akasa batayi kok’arin d’agowa balle ta samu damar kallon idanunsa dake tsare daita,cike da matsanancin sanyi jiki ta samu guri ta zauna a gefensa a takure tana fargaba kada uwar d’akinta tasameta zaune kusa da rabin ranta tashiga uku .
Tsawon minti biyar bai ce daita komai ba illa idanunsa datake ajikinta, jin shirun yayi yawa ne yasa najma tace “zan iya tafiya saboda tsoro nake ji wallahi…..
wannan furucin nata yasa fu’ad yin firgigib dan ya tafi duniyar tunanin ya saukar da numfashi da kyar yana lasar lips dinsa na kasa sannan yace “uhm dama so nake in miki wata tmby, da fatan zan samu gamshiyar amsa?
Muryarta na cracking tace “kar..karka damu kayi duk wata tambayarka sai dai wallahi a matukar tsorace nake takarasa mgnr kmr zatayi kuka ……
“Ki saki jikinki babu abinda zai faru, kafin nace komai yaya sunanki?
“sunana najma ta fad’i hkn tana sake dukar da kanta kasa sosai dan gabadaya wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki da bata ta’ba jin irinsa ba.
“najma ya sake maimaita sunan acikin zuciyarsa ,saboda dad’insa da yaji , muryarsa a tausashe yace “amman ba real name dinki bane ko……?
“uhmmmm hauwa shine asalin sunana”ok hauwa nayi matukar mamakin dana ganki a cikin irin wannan yanayin wanda sam bai dace da yarinyar k’arama kamarki ba, Amman sai gashi na tsinceki acikinsa.
“karka damu da yanayin daka ganni ciki domin duk rayuwar ‘yan gidanmu a haka ta faro, kuma babu mamakin a haka zamu k’are muna aikin bauta Dan tallafawa rayuwarmu, najma ta fad’i hk cikin murya mai rawa ala’mun tana son yin kuka.
fu’ad yaji ya sake narkewa akan kogin tausayinta, dan kamarta kamata yayi ace tana tare da iyayenta ko tana makaranta gurin d’aukar darasi, ko kuma tana d’akin aure amman yanzu gata a wulakance tana aikin bauta a inda bai zama dole asan yancinta ba .
Hakika talakawa na matukar shan wahalar rayuwa, idan ma sun dogara da karatu, sai suyi karatun su gama aiki ya zamemusu wata jarabawa ta musamman me tsananin wuya….
Najma ta matsu ya sallameta kafin me’ad tasanyo kai ta iskesu tare Amman yaki bata dama sai ma idanunsa da tsura mata yana kallonta..
sautin muryar me’ad taji ta kwalla mata Kira dan haka a matukar zabure ta mike tsaye ta fita aguje ta nufi inda take ,dan wani irin maseefaffen tsoron me’ad din takeyi kmr rai da ajali, fu’ad yabi bayanta da kallo cikin tausayawa har ga Allah yake jin tausayinta wanda kusan da wannan zuciyar ya taso na tausayawa talaka ‘yanuwansa ,Sam arayuwarsa bai ta’ba zai aure diyar me kudi ba sai ta Allah takasance dashi ya rikitacciyar matarsa.