YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 31 to 40

Tana isa gurin me’ad wata uwar harara ta banka mata “dan ubanki me nasaki kiyi da kika je kika zauna ko kin tsaya kalle min miji ne yau ma? 

  da sauri najma tace “wallahi aunty ban kalleshi ba shi… “yi min shiru zaman uwar me kika tsaya yi kmr keda gidan ubanki wannan talaka………

 “talaka ai mutun ne mai godiya ga duk yanayin daya tsinci kansa dan yafi mai yin zamba cikin aminci sau d’ari, kuma yadda gidan nan bana ubanta bane kema haka zalika bana naki uban bane, dan haka babu wani me tutiya dashi balle har wani ya gorantawa wani….

 tare suka juyo me’ad da najma duk da me’ad tasan mai yin wannan maganar amman ta kasa hakuri gara dai ta juyo ta sake tabbatarwa zuciyarta. 

 fu’ad ne tsaye kafin daga baya yakaraso zuwa inda suke fuskarsa a d’aure ..ya Matso gareta kmr zai shige cikin jikinta ya kai bakinsa cikin kunnenta. 

“Yarinya zaki gane kuskurenki da kuskuren abinda kika shukawa idan lokacin hkn ya kusa yayi mgnr kasa sosai ta yadda yasan ita kad’ai ce zataji abinda yace .

me’ad tayi shiru tana kallon fu’ad abinda bai ta’ba mata ba kenan yi mata fad’a gaban kowa balle gaban me aikinta ,dan haka cikin ‘bacin rai da daga murya tace “ke jeki kiyi abinda ya kawoki gidan nan da kika yi wani tsaye akanmu kina kallonmu kmr wata tsohuwar mayya……

najma da daman abinda take jira kenan ta bar gurin jikinta na rawa…..

 me’ad ta dawo gefen fu’ad ta tsaya batare data kalleshi ba “fu’ad ina son nagaya maka koda goma ta lalace kasan tafi karfin biyar fu’ad , duk nasan dalilin dayasa kake min irin haka da min kallon gani gani , bakomai bane facce kawai da naki ajiye wannan aikin ne .

“Kasani har kullun bazan gaji gurin gaya maka tasiri da mahimmancin shi wannan aikin da taimakonsa ga rayuwarmu ba.

 duk yadda nake son ka fahimta nassn ka fahimta hkn fiyye da tunanina, kawai so kake ka nuna min qunjinka akaina amatsayinka na d’a nmj me ragamar komai .

“Let me tell you something dakace kaine kake d’aukar salary dina bazan ta kura kaina ba saboda nima Hutu ne gareni na zauna agida naci na sha na kwanta na huta kmr sauran mata masu ‘yanci da gata …,

  “Amman tunda baka d’aukar sama da abinda nake d’aukar ko daidai da salary dina kasawa ranka zuwa aiki dole kuma yanzu na fara zuwa dan idan na zauna bansan me naka salary zai tsinanna mana ba..” and to be your last warning da zaka min fad’a gaban wannan yar iskar yarinyar ,duk abinda zakayi let it be beween me and you , abinda dai kake so ne bazai ta’ba yiwuwa ba na ajiye aikina na zauna agida jiran tsamani daga karshe na dawo bara agurinka kana min wulakanci it can be possible.. ..

“shikenan tunda haka kika za’bawar kanki zakiga ikon Allah zakiga abinda zai faru acikin gidan ,zaki sha mamakina wallahi duk wani takama da gata da jin kai da kikeji ni fu’ad nayi miki alkwarin sai na sauke miki shi ,sai kinyi kuka idanunki akan…..

“babu wani abinda zai faru sai ikon Allah ta katse shi hankalinta a matukar tashe tana haki ,” banida kowa sai Allah kuma kullun inagaya masa duk wani sharrin dakake nufina dashi allah ya meida shi kanka, alkhari dake tattare dakai kuma Allah ya kusantoni dashi..” haba ta yaya ga gsky kiri kiri bazaka yi aiki daita ba kana neman take abinda kasan barinsa a zahirance bazai ta’ba yuwa ba ,kuskure nayi ,na d’aukarwa zuciyata nayi maka laifi ,ajiye duk wani abinda nake ji akaina na baka hakuri me kuma kake so daga gareni ?

“idan kuma ba raina kake farauta bismilla gani agabanka ka kasheni ka huta daganina a doron duniya is better ka’ajiye komai mu rungume juna da tilon diyarmu da allah yabamu arayuwa abinda ya faru atsakaninmu yana faruwa har ma fiyye damu har bisa ga yanxu banyi girman ba ina sake baka hakuri ka yafe min , fu’ad har yanzu sonka na nan acikin zuciyata bai sauya ba kuma zan rayu da kai koda kuwa baka sisi basoda ba Dan wani abu naka sonka ba ………

  tana gama fad’ar hk ta juya cikin matsanancin ‘bacin inda ta iske najam tana ta aikin sharar dabatasata ba, bata kalli inda take ba tashige ta nufi shashinta ..

washegari 

sajida da me’ad suna zaune Wanda shigowarsu kenan ,najma tashigo inda suke Sajid naganinta ta mike tsaye tana kallonta wani iri “ke lafiya daga ina haka? 

najma tayi saurin zubewa kasa ta sunkuyar da kanta bata sake yunkurin kallonta sajida ba, sai ma fuskantar me’ad da tayi tace “aunty sannu da dawowa sannan ta gaida sajida, sajida batare da ta amsa ba tayi saurin kallon me’ad muryarta na rawa ” ,me’ad ta ina kika samo wannan mahaukaciyar? ta fad’a cikin daga murya …uhm me’ad ta sauke naunauyen ajiyar zuciya kema fa kya fad’a wai nan me kula da NASREEN ce abun kazanta ko? 

najma ta mike zata bar gurin me’ad ta tsayar daita da cewa “ke daga yau karki sake zuwa idan kinga ina da baki kinj ko? 

najma ta kad’a Kai alamar to sannan ta tashi cikin sanyi jiki ta fita ..

sajida ta saukar da numfashi tarasa dalilin data tana ganin yarinyar lokaci daya ta tsaneta ,ta juyo ta fuakanci me’ad “wai ni me’ad menene yake son faruwa agidanki anya babu wani kulli agame da yarinyar nan? 

“me’ad ta ta’be baki “me yasa kikace hk? 

“saboda ina jin tsoron kada abban NASREEN ya ….sai tayi shiru ta kasa karasa abinda take son fad’a. 

sajida nasan abunda bakinki yake son fad’a amman ina son kisani har abada fu’ad nawane ni kad’ai ne kuma mijina ne har tsufa ,masu ajin ma bai sauraresu ba balle wannan abar ,karma ki sake furta wannan kalmar ko hasasho yuwar hkn mijina mijin mace daya ne ..

************

Duk yadda fu’ad yake tunanin yana tausayin najma abun ya zarta hkn ,shi dai akaron kansa yarasa dalilin da tsagwaron tausayin yarinyar ya tsaya masa azuciya ,”tabbas Yasan bai Son yarinyar a Amman yana bukatar ya yantota daga bakar rayuwar datake ciki “amman ta yaya zai soma taimakon nata batare dayasamu wata matsala ba ?

Yayiwa kansa tmbyr da bashi da amsarta kuma bashi da me bashi amsarta .

Yana cikin wannan tunanin yaji ana knocking kofar office, kai tsaye yaba da umarnin shigowa yana me dukar da kansa domin cigaba da aikinsa da tunani najma ya dakatar dashi .

Tashigo office din cike da doki son d’aura kwayar idanunta akansa ahankali ta meida kofar ta rufe har da sanya mata key ,sannan tayi tsaye a guri daya, tana kallonsa tmkr an dasata tsabar farinciki ganinsa datayi ,”yaushe rabon datasanya shi idanunta?

” gbdy ya kulle duk wata hanyar da zata sadasu da juna, shiyasa yau tayi kundin balar biyosa ofishinsa domin tsaida mgn daya me yiwuwa ayita ta k’are .

Jin shiru shiru wanda yashigo bai yi mgn ba yasashi d’ago kyawawan idanunsa masu matukar kyau da tsoratarwa ya saukesu akanta tsaye sanyi cikin after dress baka har kasa ta yane kanta da bakin mayafinta sai wani shaning take ,sai dai daga saman after dress din abud’e yake wanda duk me fuskantarta zai iya hango cikar halittar kirjinta , haka tashigo dashi abude ko kuwa sai da tashigo ta bud’e shi ,shi dai bai sani ba kallo daya yayi mata ya dauke kansa daga kallonta yana mamakin kasada irin nata…fuskarta kunshe da dry tasoma karasowa zuwa inda yake tana girgiza masa jiki da nonuwanta tana gama Karasowa garesa ta koma laulausar tafin hannunsa cikin nata lummmmmm ta lumshe idanunta tana jin sanyi sonshi na ratsata ta koina ajikinta…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button