YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 31 to 40

Washegari da wuri ta tashi tashiga kitchen domin sake wanke masa zuciya, ahi kuwa duk yadda yaso ya d’aure mata hkn yaki yiwu Dan haka dole ya D’an saki ransa har yayi breakfast yaso kwarai yaga ko gilmawar najma ne saboda kusaan kwanaki goma kenan bai sanyata a idanunsa ba ,Amman duk iya zaman da yayi bai ga alamunta ba ,gashi lokaci na tafiya hk ya tashi ya wuce .

 

***********

Me gidan fu’ad yasamu mahaifin Sajida da zancen inda sam dattijon yaki amincewa da maganar dayazo daita “wannan ai shirmen banza ne ,kuma shine babban abun kunyar da zata aikata arayuwarta ,”Sajida ta auri mijin Me’ad sam ni dai babu hannuna cikin wannan lamarin, “sannan ina rokonka dan girman Allah kar ka sake zuwa min da makamanciyar wannan zance Dan ina ganin girmaka, babu yadda me gidan Fu’ad baiyi da mahaifin Sajida ba,Amman yace sam ba dai da yawunsa ba haka jiki a sanyaye ya tafi..

Ai ko yana tafiya ya rufe Sajida da bala’i ta inda yake shiga bata nan yake fita ba”daman kinsa abin kunya da zaki aikata kenan shiyasa, ki kaki yarda ki sanar da kowaye zaizo neman aurenki, to wannan abun kunyar ba dani ba wallahi, barikiji ingaya miki Me’ad tamkar ‘yar uwa take gareki ..

“daddy ka saurari uzirina ………”babu abinda zan saurara matsawar akan wannan abun kunyar ne kuma bana bukatar a sake tada zance nan ya wuce fuuuuuuu ya nufi d’akinsa kamar zai kifa .

kuka ta rushe dashi tare da d’aura kanta saman cinyar Aunty Nadiya “ki taimakeni aunty wallahi da kyar nasamo kansa ya amince zai aureni gashi dady na neman hanawa .

Aunty nadiya ta d’aura hannunta saman kanta cike da matsanancin soyayya “ki daina kuka Sajida mahaifinki yafiki gaskiya wannan babban abun kunya kike shirin aikatawa arayuwarki.

” ki zauna ki nazarci halakarku da Me’ad zumunci ne me k’arfi tun daga Kan iyayenku har zuwa kanku bai kamata hakan ta faru ba, duniya zata zageki “wallahi Aunty akan auren nan banki duniya ta tatsine min ba, matukar zan rayu da Fu’ad shekara goma ina zaman jiran wannan ranar amman dady nason rusa min farin cikina ta zabura ta mike tsaye cikin matsanancin tashin hankali “da kaina zan sanawar Me’ad d’in. 

“ko shikenan ba ….zan gaya mata yadda nake son mijinta Dan bazan iya rayuwa babu shi …tana gama fad’ar haka ta nufi d’akinta tana wani irin kuka .

*********

Najma tsaye tana faman had’awa NASREEN abinda zataci kafin ta dawo daga school sanye cikin kod’ad’un kaya tun wanda tazo dashi bata sauya ba, sun yage guri ya kai uku gashi babu yadda za’a yi ta d’inke duk inda ya yage ta had’a da d’an uwansa ta kulle hakan yasa, zanin kayan ya dangale mata sosai daman kala biyu tazo dasu daga wannan na jikinta sai wani shima ya tsufa sosai, yayinda Fu’ad da shigowar sa kenan zai shige d’akinsa yayi mata kuri da kyawawan idanunsa cike da tausayawa “wai kamar batare take da masu kudi ba an kasa taimaka mata da wasu kayan.. 

kmr ance Najma ta juyo taga yayi mata kuri yana kallonta take gabanta yayi wani irin fad’uwa ta matsa daga can cikin kitchen din domin boye kanta yayinda har lokacin gabanta bai daina fad’uwa ba. 

Fu’ad ya taka har zuwa bakin kitchen din ya tsaya batare daya shiga ba “Najma tsorona kikeji ko kunyata ? Yayi mata tambyr yana saita kwayar idanunsa akanta. 

Najma tayi saurin girgiza kai “dan Allah kayi hakuri ka daina min magan Aunty batason hakan tace idan na sake yi maka magana sai ta yanka ni gunduwa gunduwa. 

Fu’ad yayi murmushin “Me’ad kenan me rikicin ganga sannan yace “karki damu barazana take miki babu yankaki daza tayi.. 

Najma tayi saurin kallosa “wallahi zata iya kaga kuma in ta yankani ta yanka banza, kuma na yarda da hakan dan a shekarun baya ta ta’ba watsawa Aunty Ummi yayata ruwan zafi har ta kone a fuska, Fu’ad yaji tausayinsu sosai ,aransa yake sake jin kwad’ayin taimaka mata koda kuwa zai rasa ransa ne ya saukar da naunauyen ajiyar zuciya sannan yashigo cikin kitchen din sosai still idanunsa na kanta “Najma ina son ki taimaki kanki ta hanyar amincewa da aurena domin ina bukatar naganki kina rayuwar ‘yanci… 

Najma tayi saurin kallonsa hantar cikinta na wani irin kad’awa gbdy ta kasa gane manufar maganar sa da inda ta dosa, ya jinjina mata kansa “zaki aureni …?

” ina son taimaka miki Amman gbdy atunani banga irin taimakon daya dace Dana miki ba kamar na aureki .

da sauri Najma ta mike daga tsugunne datayi tana girgiza kai jikinta na wani irin rawa cikin wani irin tsananin tsoro da razana ,yayinda wani irin, azzafan gumi yashiga tsatsafo mata a fuska duk kuwa da AC dake aiki a kitchen d’in…

” Fu’ad ka haukace …. tunda kake furta irin wad’an mugayen kalaman irin na mutumin daya haukace.. 

basai ya juya ba yasan mai yin wannan maganar Me’ad dinsa ce to yaushe ta dawo gidan ?

Yayiwa kansa tmbyr kirjinsa na mahaukacin bugu.. 

ita kuwa Najma tuni ta kame dan azabar tsoro da fargaba Me’ad takaraso gaban Fu’ad ta tsaya idanunta cike da ruwan hawayen bakin ciki ta kalli cikin kwayar idanunsa ,ido cikin ido “fu’ad kabani mamaki kuma bani kunya tunda duk matan duniya babu wacce kagani kake son had’ani daita amatsayin kishiya sai wannan abar wace iyayenta suka dogara daita Amman wallahi baka isa ba dan banga abinda wannan abar tafini ba, banda lalata gidanka dazakayi…. 

Fu’ad ya matso sosai har suna iya jiyo hucin numfashin junansu yana kallon cikin idanunta “hakika me’ad kinyi babban kuskuren sai dai kisani ni fu’ad a yanxu yarinyar karama kmr Najma nake son aure yarinyar karama wace zata min ladabi da biyayyar danake bukata bazata min iko da takama da wani aikinta ba ko nuna min ubanta wani kosa ne a Nigeria , dan nayi alkwarin zan sake auren amman yar mara shi wato yar talaka irina da kuke rainawa saboda ganin kaskancinsu acikinku.. 

“anya fuad dinta bai haukace ba kuwa da har yake furta mata wadan nan kalaman masu yanayi dana mahaukata ?

gbdy me’ad tarasa abinda zatayiwa Najma dan ta huce, dan duk duniya a yanzu babu wanda ta tsana take jin zata iya mata komai kmrta 

 wadda take ganin wani namiji mai hankali komai lalacewarsa bazai iya cewar yana sonta ba, duk kuwa da irin kyawun halittarta, amman sai gashi mijinta wanda duk duniya bata had’ashi da komai ta fifitashi akan komai na rayuwarta iyayenta da komai nata wai shine yake bukatar mallakarta amatsayin mata ta fad’i kalmar a fili.. 

“take Najma ta d’aura hannunwanta duka bisa kanta “wayyohlly Allah nashiga ukuna daman nagaya maka Aunty kasheni zatayi tunda banida gata..

 Me’ad tayi kukan kura ta janyo tunkuyar da ruwan zafi yake ciki yana tafasa tayi kan Najma dashi Najma ta kidemi tayi bayan Fu’ad batasan lokacin data kankameshi ba, tana kururuwa da ihun neman dauki.

Fu’ad yayi saurin rike mata hannu dan yasan halinta zata aika balle yanzu da bata cikin haiyacinta “meye hk Me’ad kike k’ok’arin kashe yar mutane ?

“kina hauka ne ko kin sha wani abu ne ni da kike son yin kisan kai bayan kinsan idan kin kasheta kema kasheki za’ayi, ni Yakamata ki illata ba ita ba saboda ni nace zan aureta .

Me’ad bata sauraresa ba kaitsaye tayi kan Najma dake tsaye tana kuka jikinta na rawa fu’ad yayi saurin riketa ya rankwafar da tunkunyar ruwan zafin ya kelaya a kasa, amman Me’ad bata hakura ba tayo cikin kitchen d’in da gudu ta wawuri doguwar wuka ta biyo Najma ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button