YANCIN KI Page 51 to 60 (The End)

taja numfashi da kyar ta fitar kana tace “Kawai mu hakura da juna Dan bazan iya fuskantar mahaifina da wani zance makamancin wannan ba, Domin da amincewata ya aiwatar da komai.
“uhmmmmm ai kuwa zaki had’u da ‘bacin rai mai tsanani Dan bazan juri zuwa gidan nan ba, sannan zan k’ara aure tun da had’in bakinki ake neman ganin bayana. ….
gabanta ya buga da sauri ta bude idanunta fess kan fuskarsa tana kallonsa kmr zatayi kuka.
“ya naga kinyi da fuskarki wani iri,ala’mun ba kya son na kara aure? ” ke bazaki kasance tare dani ba sannan ba kya son wata ta kasance dani ,alhalin kinsa bazan iya d’aukar dogon lokaci batare da mace ba, duk iya tsawon watanin Dana yi batare da mace ba dauriya kawai nake yi …
ya matsota sosai tmkr zai shige jikinta “Dan Allah love kisan abun yi atsakaninmu ,ko ki dawo gareni ko kuma ki taimaka ki sanar dani yadda zan nemi ganawa da iyayen najma na aureta, yayi mgnr yana kunshe dariyar da ke neman subuce masa saboda yadda fuskarta gabadaya ta sauya .
tun da ya sako zance najma, numfashinta ya tsaya , bakincikin maganarsa ta caki kahon zuciyarta, “kenan har yanzu zuciyarsa na Kan yarinyar nan bazai fasa aurenta ba?
Ta jefawa kanta wannan tmbyr tana ambatar sunan Allah tare da zare hannunta cikin nasa ta dafe goshinta dashi tana takaicin yadda ta sakar masa jikinta yanzu ya mora son ransa .
“da tasan zuciyarsa na kan yarinyar har lokacin, ba zatayi sakacin sakar masa jikinta ba, ta dade zaune kafin tasamu tayi control din kanta ,tabbas sai tasa natsuwa in dai tana son komai ya daidaita atsakaninmu da rayuwarsu tana sonshi matuka amman akansa wannan karon bazata butulcewa mahaifinta ba .
ahankali ta yunkura kmr wace akayiwa dukan mutuwa tasoma k’ok’arin mikewa tsaye zata rabe gefensa ta wuce ranta a hade, yayi saurin riko tafin hannunta Wanda yasata tilas tsayawa ta juyo a fusace tana kallonsa, shima ya tsura mata kyawawan idanunsa tsawon minti biyu yana kallonta sannan yace “Nasan bakiji dadin kalmata ta karshe ba, Amman kiyi hakuri babu dadin da kikaji, Akan babu dadin da kika min kuma na yafe miki ,yacigaba da kallonta da kyawawan idanunsa ,ya matso jikinta sosai yana yawo da hannunsa jikinta “a zahiran gsky me’ad bazan iya zama haka babu mace kusa dani, lokaci yayi da zamu sanya karfi da karfi mu magance matsalarmu tare, ni na rasa dalilin dady na son rabumu , Amman gabadaya na lura acikin lamarin kin fi kowa laifi ,domin kece tsanin komai ”
“nasan da haka sai dai kaima kasani kai ne dalilin zuwana gida wanda silar hk ya zame min alkhairi tunda gashi mahaifina ya yafe min ‘bacin ran danayi silar jefashi a dalilin aurenka, ni dai a halin yanzu bansa yadda zanyi ba ,kawai ka sauke min kmr yadda dady ya bukata kaje ka auri ita wacen yarinyar da kake naci ,daman ni tuni nasoma hakura da kai takarasa mgnr hawaye na gangaro mata.
“shhiiiii ba kuka nace ki min ba mafuta zamu nema Dan wallahi bazan iya sakinki ba zance auren najma kuma ni ne nasa kaina, kuma zan aureta bisa taimakonta, sai dai idan Allah bai kaddaro hkn atsakaninmu ba.
Amman kiyi hakuri ki Nemo mana mafuta “ta fixge hannunta cike da matsanancin ‘bacin rai ta yo baya kad’an ta fuskance shi “hakuri fa kake bani ?
“Hakuri na koma gidan na sake bijirewa umarnin mahaifina kake nufi ?
“ko kuma hakuri da zance k’ara aurenka dakake sake tabbatar min ?
Ya d’anyi gyaran murya sannan yace “ina baki hakuri ne Dan inganta rayuwarmu, ki saurareni ina bukatar muyi magana takarshe dake ,babu musu tasamu guri ta zauna tana haki shima ya k’araso ya tsugunna agabanta hannunsa dafe da gwiwowinta ” ki godewa Allah daya takaita aurena da sajida, Dan na samu labarin aurenta, nabsani auren sajida zai fi miki ciwo da tsayawa arai akan najma,dan haka ki yarda ki amince min da auri najma ko babu komai ina bukatar taimakawa rayuwata..
“da siffan aurenta ne kawai zaka iya taimakawa rayuwata?
Fu’ad na sanka over 10 year’s, nasan abinda zakayi da abinda zuciyarta keda tabbaci akai ,ka fito fili kace min kawai kana son wannan yarinyar Amman ba wai taimakonta ba , kana dai cewa taimakonta zakayi is better fu’ad kace min mead son yarinyar najeyi zan aureta, zanfi yarda akan taimako, dan idan taimako ne, akwai hanyoyi daban daban da zaka iya taimakonta dashi, ba lallai sai ta hanyar aurenta ba, well duk abinda kayi babudamuwa, dan for me right now bani da wata matsala daita da kai karon kanka, ruwanka ne ka aureta ko ka fasa aurenta ” what I need from you shind ka sauke min aurenka nasamu free arayuwata dan…. ”
“dakata plz ya mike tsaye daga durkuson dayayi agabanta cikin fushi yasoma mgn ahankali “na fuskanceki me’ad da fuskantar inda kika dosa akaina ,kina son na sakeki kisamu free ki auri safwan ko ba haka ba ..?
“Kina son ki barni ki aure wancan tantirin dan iskan daya kasa d’auke zuciyarsa akanki ? Ya fad’i hk yana fuzar da iska mai zafi .
“ki fito ki fad’a min kina son safwan kawai ,ba wai umarnin mahaifinki ba ”
“no abban nasreen ka fuskanceni ,banason safwan tun farko, karka manta nice da kaina na gujeshi da aurensa gabadaya, tayi mgnr a matukar gigice tana k’ok’arin kamo hannunsa cikin nata “ba nufina ka sakeni Dan na auri safwan ba,ina son mu rabu ne dan samun natsuwar mahaifina..
ya fixge hannunsa a matukar fusace “wata biyu kacal na baki ki tattara ki dawo gareni idan ba haka ba wallahi zanyi k’arar mahaifinki kotu tun shi bai rigani ba .
ya juya yasoma taku dan barin d’akin .
yana fita ta rushe da wani irin kuka jikinta na rawa ,ta isa jikin window d’akinta ta tsaya hawaye na gangaro mata.
Shi kuwa lokacin daya fito parlour’n ya iske mumy tana faman zariya hannuwanta duka goye a bayanta gashi ta had’a uwar gumi ,tana ganinsa ta saki naunayen ajiye zuciya muryarta cike da in ..ina tace “ha..har ka fito ?
“Na fito momy akwai damuwa ne ? Yayi maganar yana shafa sumar kansa.
“No babu komai ta fad’i hkn tana Allah Allah ya bar gidan.
“ya isa gurin nasreen dake kwance Kan doguwar kujerar daya barta bacci yayi awon gaba daita ya shafa suman kanta yayi kishing dinta a goshi sannan yayi mumy sallama ya fice daga parlour’n, tsab ya gama karantar yanayin mumy da abinda take nufi dashi Amman shi bashi da cause da kowa ,kuma duk lokacin da yayi masa dadi zai zo gurin iyalinsa.
Adaidai habar gidan ya tsaya ya fito mai gadin gidan da hannunsa sannan ya koma jikin motar me’ad ya jingina jikinsa tare da rungume duka hannunwasa a faffad’an kirjinsa, mai gadi ya k’araso inda yake da sauri ya rusuna cike da girmamawa ya gaisheshi ,fu’ad ya amsa “ammm malam sule wata yar tambaya nake son maka idan bazaka damu ba ”
Sule mai gadi ya gyara tsayuwarsa sannan ya tattaro duka natsuwarsa ga fu’ad yace “yalla’bai Allah yasa nasani “kasani ma akan tsohuwar mai aikin gidan nan ummi nake son yi maka tambayar “ina ne unguwarsu ?
Sule mai gadi yayi shiru yana sauraronsa har sai daya ji ya takaita zancesa sannan yace ” apapa suke zaune wuraren bandir, ana gidansu yake nan dai sule ya bashi full addres din da zai samu najma sannan ya fita ta karamin get yana masa godiya ,duk wannan tautaunawa da sukayi akan idanun me’ad sukayi shi ,hankalinta yayi mugu mugun tashi duk da batasan maganar da sukayi ba Amman jikinta ya bata address din najma ya tambaya ta fashe da wani sabon kuka “wayyohlly Allah ina son mijina ,ina son kasance tare dashi muddin rai banason rabuwa dashi Amman bazan iya jurar yin abu biyu akansa ba ,sa’bawa mahaifina da kallonsa tare da wata suna rayuwa irin wace muke yi dashi ba ,ya Allah ka saisauta min ,ka kawo min karshen wannan damuwar da nake ciki ,ka cire zuciyar mijina akan wannan yarinyar ,Allah ka canza zuciyar mahaifina ,ka saukar masa da natsuwa ,kasanya masa hakuri akan lamarina da mijina haka tayita kuka tana addua ..