YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 51 to 60 (The End)

Fu’ad na isa inda yace kabir ya jirashi ya bud’e murfin motar yashiga ya zauna yana fitar da numfashi sama sama , batare da yace komai ba ,shima kabir bai yi yunkurin cewa dashi komai ba yaja motar akan layinsu suka hango ta howar motar dady wanda ke zaune abayan Mota ana tukashi ,”kabir tsaya mu gaisa da dady “inji cewar fu’ad. 

Slow down din motar kabir yayi tare da yin hon , shi kuma direban dady ya ja tsaya ya tsaya saboda gane ko su waye .

Ahankali dady ya d’ago idanunsa domin ganin dalilin tsayuwarsu, gama d’agowarsa ke da wuya idanunsa ya sauka akan fu’ad dake k’ok’arin fitowar daga cikin motar .

 take ransa yayi mugun ‘baci yaja dogon tsaki yana bawa direban umarnin barin gurin ta hanyar buga masa tsawar da tasa ya rikice,” kada ka sake min wannan aikin banza , daga ganin motar wasu matsiyata kaja burki ka tsaya saboda rashin sanin aikinka, ka sani ko baraye ne ma ,Wanda irin haka na faruwa sosai a duniyar nan tamu ,ta inda yake shiga bata nan yake fita ba yana ta faman fad’a.

Direba ya sake rikicewa da mazurai yana duban fu’ad ,shi dai asaninsa surukinsa ne dake aure d’iyar cikinsa,” to me yasa zai masa wannan wulakanci? 

Jikinsa na rawa da bakinsa ya murza sitiyari Dan bai kashe motar ba “kayi hakuri mai gida ba’a za sake ba .

Dady bai kula sa ba ya maida idanunsa kan jaridar dake ajiye a gefensa. 

Fu’ad ya dade tsaye agurin yana tunanin da mamakin abinda yayi wa dady arayuwasa da yasa baya son shi ,da kaunar ganinsa arayuwarsa, kusan minti goma sannan kabir yace ka shigo mu wuce “ya zakayi haka Allah yake lamarinsa,mahaifin me’ad baya sonka ne bilhakki da diyarsa ,ba wai dan rashin airzikinka ba ,Amman ya za’a yi Allah ya rigada ya had’a ,kuma shi kad’ai ya isa ya rabaku da me’ad, “karkayi fushi dashi , kai dai duk runtsi duk wuya karka saki matarka ko dan mahaifinta, matukar kayi kuskuren sakinta to kuwa yayi galaba akanka abinda bazanso kasancewarsa ba kenan .

jiki a sanyaye fuad ya dafe goshinsa abubuwa sun taru sunyi masa yawa .

  kabir yacigaba da magana yana tuki “sai abu naga akan auren wancan yarinyar mai aikinka ,ni bazan hanaka aurenta ba ,Amman fa kasani auren yarinyar bashi ne mafuta ba ,sai ma K’arin damuwa, tunda kana son matarka kuma kai ma kasan tana sonka har yanzu “to meyasa zaka damu kanka akan lallai sai ka k’ara aure alhalin ta gidan ma baka gama daita ba ?

“bazaka gane munufar abinda ke cikin raina ba kabir ni nasan dalilin dayasa kaji nace maka zan auri yarinyar ”

“zan gane idan kagaya min manufar taka ni dai ba wai ina side din me’ad bane kawai ni banason ka k’ara aure ne tention yazo yayi maka yawa duk da yanxu ka taka wani matsayi ,”yanzu dai kagaya min manufarka ta son auren yarinyar?

Batare da ‘bata lokaci ba fu’ad ya zayyane masa komai ,dogon tsaki kabir yaja yana dukan sitiyari motar ” aikin banza kai yanzu karasa taimakon da zaka mata sai na aurenta alhalin zuciyarka bata sonta Anya kuwa wannan maganar taka akwai zahirin gaskiya acikinta? 

“Zahirin gaskiyar kenan na gaya maka kabir bana sonta taimakawa rayuwata kawai zanyi ”

“Karya ne fu’ad kana sonta..fuad ya juyo da sauri ya kalli kabir batare da yace masa komai ba “yes kana sonta mana mamakin kake yi alhalin kasan gaskiya na fad’a maka .

“na rantse maka da girman Allah kabir bana son yarinyar nan taimaka rayuwarta kawai nake son yi tana matukar bani tausayi Amman zance so me’ad kawai nakewa shi, saboda itace macen data had’a duk wani abinda nake bukata, ka yarda dani zan aureta ne Dan taimako ”

“Ok tunda baka sonta taimako ne me zai hana kasamu wani natsatse ka tsaya masa ya aureta ,ba lallai sai kai ba ….

fuad yayi mugun tsareshi da kyawawan idanunsa yana kallonsa kirjinsa na wani irin mahaukacin bugu, zuciyarsa na rawa Wanda bai San dalilin jin haka ba.

“idan kuma baka yarda ka aura mata wani daban ba saboda wasu dalilai ,to ka aura min ita ,kasan halina kasan komai nawa kasan bazan cutar daita ba ,duk abinda kake so zan mata, ni burina kawai ba wuce kabar me’ad tasamu kwanciyar hankali ba ,idan ka k’ara aure hakan zai sa mahaifinta ya tabbatar mata da rashin damuwar da bakayi daita ba ,haka zalika itama zataji babu dadi aranta ,”kai ko auren ma zakayi kabari komai ya daidaita atsakaninku ,kasanya manya cikin maganar a kawar da matsalarka da mahaifinta, shine kawai abinda zan baka shawara akai bawai kaje ka k’ara aure ba ..

Fuad yayi shiru yana sauraran zantuttukansa ,da wannan tautaunawar suka bar unguwarsu me’ad . 

Shi kuwa dady ransa a matukar dagule ya isa gidan, direba nagama parking ya fito fuuuuuuuu yashiga cikin gidan yana huci tamkar mayunwacin zaki a parlour’n ya iske mumy tana k’ok’arin maida tiren abincin da fu’ad bai ci ba, tana ganinsa tayi saurin shigewa kitchen ,ta ajiye tiren ta fito tana yi masa sannu da dawowa a madadin ya amsa mata sai ya jiho mata tambayar data k’ara rikitar daita ” wannan matsiyacin yaron yazo gidan nan ne?

Mumy takama mazurai tana kallon kowace kusurwa dake cikin parlour’n kafin ya dora da fadin “na rantse da girman Allah zan ‘bata wa kowa rai acikin gidan nan , matukar za’a dinga barin wannan yaron yana zuwa gi ..

“Ban fahimceka ba dady akan me kake magana akai ?

Mumy ta katse masa hanzari.

a fusace dady yace ” ai kinsa ko akan wa nake maganata kar ya sake zuwa min gidana bana bukatar ganinsa cikin gidan idan ba haka zan tashi hankali kowa ‘ya dai tawace bata uban kowa ba .

“haba haba dady wai me yasa kake yin irin haka ne? 

“Edi……mumy takura sunansa Wanda yaushe rabon da takirasa da sunan ” Banason abinda kakeyi min a enough is enough ,”ta yaya zaka yi k’ok’arin hanashi zuwa gidan nan alhalin matarsa da ‘yarsa na cikin gidanka ?

“Akan wani dalili ?

“idan bakason yazo maka gidanka ka bashi matarsa mana ,nifa bazan yarda ka kashe wa yarinyata aureta ba ,alhalin ba samun miji irin mijinta zatayi ba ,shi wanda kake son ta aura me yafi fu’ad din dashi?

” I think kudi ne ko ba haka ?

“Kai yanzu kasan me gobe zata haifar ?

“shima yanzu yasoma taka wani matsayi wanda bakasani ba ko nan gaba zai zatar na safwan .

“Ada naso auren me’ad da safwan Amman ayanzu wallahi tallahi banason shi da me’ad, Dan ko ta aureshi ba zata samu kwanciyar hankali ba ,duk uba na gari bazai so ‘yar cikinsa ta rabu da fu’ad akan safwan ba, babu abinda safwan baya sha ,giya taba kokin da sauransu ,shine kake k’ok’arin kashe mata aure akan shi wallahi bazai yiwu ba takarasa mgnr tana daga hannunwanta sama….

“a she kuwa tabbas zaki had’u da mugun ‘bacin raina , zaki tattara ki bar min gidana matukar akan wannan D’an iskan yaron ne .

 Dan ni komai safwan zai yi arayuwa ni shi nake son me’ad ta rayu dashi ,Dan har yanzu yana sonta fiyye da wancan gaular yaron ,Dan haka tilas na d’auki mataki, Dan me’ad bazata sake cigaba da rayuwa dan wannan matsiyacin ba “waye matsiya? 

Mumy ta jiho masa tambaya ranta na mata suya ….

“Kinsa ko wa nake nufi .

“me yake dashi ?

“Me ya mallaka?

” company’s dinsa nawa ?

“Waye ubansa a duk fanin Nigeria kinga kuwa dole ni agurina ya tabbata matsiyaci Dan duk arziki da zai yi bazai ta’ba kankare wannan sunan agurina ba …

Yana gama fad’ar haka ya wuce fuuuuuu ya nufi hanyar dakinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button