YANCIN KI Page 51 to 60 (The End)

“Kai kake ganinsa amatsayin matsiyaci Amman ni agurina yafi dangote komai ,tunda bai bar diyata cikin gararin rayuwa ba , kuma babu Wanda yasan matsiyaci sai Allah, haka kawai zaka tsani d’an mutane babu wani dalili ,wallahi duk runtsi bazan yarda ka kashe mata aure ba ,mutun sai kace jahili…
*******
Mahaifin sajida ya nemi Khalid ta waya inda ya ce “masa ya zo ya d’auki matarsa ,ganin tsawon kwanaki uku kenan da d’auri auri ,bai zo ba sannan wani daga cikin daginsa bai tako ba gashin duk abinda yakamata ayi ma amarya a gidanta ya kammala ,hatta gara sai da dady yasa aka cika mata d’aki dashi .
khalida bai yi sanya a gwiwa ba ya shirya cikin had’ad’en kananan kaya wando baki da riga long selve green mai ratsin Baki baki ajiki ,ya gyara kwantacen gashin kansa da yayi askin afro, Dan shi ko irin askin da ango kan yi bai yi ba ,illa bayan keyarsa daya bari aka gyara masa ,yayi wanka turare ta koina ajikinsa kamshi ke tashi na fitina yayinda hannunsa na dama ke daure da agogon fata kafafunsa sanye cikin wasu takalmin Gucci baki ,yayi kyau sosai, kuruciyarsa ta fito Dan kana ganinsa kaga sabon matashi mai jini ajika .
Karfe tara daidai agidan surukinsa tayi masa,kai tsaye ya shigo gidan bai tadda kowa a parlour’n ba ,Dan haka d’akinta ya nufa batare da ya yi knocking kofar ba yasanya kai cikin d’akin.
Zaune ya isketa a gefen gadonta Sanye cikin Riga da siket na atamfar julius Holland ,d’inki yayi mugun amsar jikinta ,domin ya fitar da shape din jikinta sosai ta yadda duk wasu kyawawan halittar na jikinta suka bayyana, sai kamshi dad’d’an turare ne ke fita a sansar jikinta ,sosai tayi zurfi cikin tunanin, tunda aka d’aura aurenta taje diner ta dawo bata sake sanya kafafunta waje ba, haka zalika ko parlour’n kasa bata sake sauka ba ,mahaifin dai yasameta a d’akinta yayi mata nasiha sosai a game da aurenta da Khalid, amma ita Sam bataji zata iya hakurin zama dashi ba, ita ko bazata auri fu’ad ba gara ta zauna babu aure .
yanzu haka tunanin yadda zata soma warware matsalolin dake shirin kunno kai cikin rayuwarta take ,ita ba mahaifiya ba ,gashi bata da yaya ko kanne dukkan wani girma ya tattara ne akanta , bata da mai bata shawara, babban abinda yafi damunta shine yadda zata raba kanta da auren wannan premature din …
wani sauke ajiyar numfashi tayi ta gyara zamanta cikin yanayi na zurfin tunani ,ahankali ta d’ago idanunta sakamakon jin yanayin kamshi d’akin ya sauya ,aiko idanunta ya sauka akanshi tsaye jingine da jikin k’ofar d’akin ya rungume hannunwasa duka a kirji ,yayi mugun tsareta da idanunsa yana kallonta , kallo daya tayi masa ,ta d’auke idanunta akansa Dan Sam batason ganinsa acikin kwayar idanunta, tana jin da Zata iya, da ta tashi ta makure masa wuya ta kashi shege kowa ya huta ..
Ahankali yasoma takowa zuwa inda take zaune ya zauna cinyoyinsu na gugan juna ,tsaki taja had’e da saurin mikewa ta nufi hanyar fita daga cikin d’akin Khalid yayi saurin tare gabanta bai bari ta fita ba ,fuskarsa Sam babu walwala kamar yadda nata mata babu ..
“Malam premature ka matsamin na fita nace bana sonka ko ana dole ne ?
Tsananin mamakinta kawai khalid keyi , shi yanzu meye laifinsa dan ya aureta?
“Tayi play dinsa like a fool sai kuma gashi daga karshe yayi winning dinta. ..
“duk yadda zaki kai da guduna kaddara ta rigada ta had’amu guri daya ,you are mine sajida, ke din tawace,ina kuma tabbatar miki sai Allah ya taimaka min gurin gefa soyayyata cikin zuciyarki ,so ki daina wahalar min da kanki ,ko kina sona ba kya sona zaki rayu da Khalid har abada Dan bari na gaya miki new gud news har ciki haihuwa Khalid zai miki ….
yadda yayi maganar cike da karfin hali ya bata mamaki sosai sannan ta kasa d’auke idanunta akansa ,Khalid daban yake acikin premature din da take matasa irinsa ,yadda yake gudanar da alamuransa cike da isa da gadara sosai yake bata mamaki ..
wani irin kuka ne kufce mata ,muryarta cike da matsanancin kuka tace “Allah kiyaye min yin ciki da kai ,sannan har abada ni sajida bazan ta’ba sonka ba, I hate you in my life bazan taba sonka ba …shr yayi tare da tsura mata idanunsa yana kallon yadda take kuka muryarsa can kasan makoshi yace “bakya so na ?
Tayi saurin girgiza masa kai ,”but ai ni ina sonki sannan zan ‘bata tsawon rayuwata tare dake ,zan canzaki na canza gurbatacciyar zuciyarki da batasan zahirin abinda ake kira so ba ,Zan tabbatar miki da abaya can ba soyayya kikayi ba shawace take dawainiyya dake ,I love you sajida and I want spend the rest of my life with you I want you to become mrs khalid..dubansa take sosai cike da matsanancin bakinciki kalamansa masu maka da zantukan kuruciyar yara ,bata an kara ba taji ya janyota jikinsa ya rungumeta tsam ajikinsa “ki daina furta ba kya son mijinki Dan baki San abinda gobe zata haifar ba ,ta bud’e bakinta zatayi magana kenan ,ya had’e bakinsu guri daya yashiga tsotsar bakinta da iyakacin karfinsa ,tayi kokarin kwatar bakinta Amman yaki barinta shan bakinta yake kmr zai cire mata baki gashi ya toshe mata hanci dole tasa ta dinga bashi hadin kai ,shi kuma yasamu damar tsiyaya mata miyon bakinsa tana hadiyewa.tsawon minti goma yana rungume daita yana tsotsar bakinta duk da yadda taso kwace jikinta Amman yaki sai daya so Dan kansa sannan ya saketa ya rike hannunta ita kuwa sai numfarfashi take fitarwa na wuya , tana kallonsa ya ciro wayarsa daga cikin aljihun rigarsa yasoma dialling number dady tare da sanyawa a hands free .kira daya biyu dady
Ya d’auka.
Khalid ya gaisheshe tare da gaya masa yazo d’aukar sajida ne ,dady yace” to ..madalla kashigo daga ciki mana ya zaka tsaya daga waje ?
Muryarsa cike da in..ina ..yace ammm ai yanxu haka ina d’akin sajida ,koda nashigo banga kowa ba ,”ok to babu komai Allah yayi maku albarka ya yabaku zaman lafiya ,idan ka tashi ka wuce da matarka kawai ayita hakuri sukayi sallama ,ahankali ya saki tsintsiyar hannunta “ina mayafinki ?
Tayi masa banza ta shiga goge hawayen bakinciki bai tsaya ‘bata lokaci ba ya d’auki hijabin sallarta yasanya mata sannan ya d’auki karamar akwatin kayanta dayayi saura Dan komai akai gidanta, “ki biyoni kawai idan kikayi kuskuren canza min tunanina a yau jikinki ne zai gaya miki , yayi gaba abinsa ai da sauri ta gyara zaman hijabinta tabi bayansa zuwa harabar gidan Wanda har ya saka akwatin a bayan mota .
Da kansa ya bud’e mata gaban mota ta shiga su duka babu walwala a saman fuskokinsu sannan ya zagaya mazaunin direba ya bude yashiga yashiga yasanya seat belt sannan yayi motar key suka bar gidan .
Karfe Goma cif agidansu dake Williams estate yayi musu Dan madaidaicin gida ne ,me shegen kyau ya fito ya bud’e get din gidan sannan ya dawo yashiga motarsa ,yashiga cikin gidan ,yayi parking ya sake fitowa ya bud’e mata kofa “oya madam Dina a office ,tsohuwar matata agidana barkanki da zuwa gidan pre me ma kikace… ?”I want here it again …
tayi masa banza ta fito tana duban yanayin tsarin gidan ” shafa goshinsa yayi sannan yace “ai nasan zuwa yanzu bazaki iya cewa komai ba ,muje daga cikin tukun ya maida murfin motar ya rufe ya matso kusa daita ya riko hannunta suka nufi cikin gidan mai d’auke da dakuna guda uku kacal zagaye da parlour’n babu TV bango, balle kujera a parlour’n da babu ac ,babu komai a parlour’n ta fad’a aranta, ya karaso gareta ya rungumota ta bayanta hannuwansa duka zagaye da cikinta ..