YANCIN KI Page 51 to 60 (The End)

yayinda nasreen ta sakar mata kukan ita baza taje gidan grandpa ba, gara ta kai ta gurin dadynta…..
kukan datake yana ta’ba zuciyarta kuma batason kukanta saboda ,da zaran jikinta ya d’auki zafi shikenan .. ciwonta zai tashi Amman babu yadda ta iya da rayuwata ,hkn datayi shine kwanciyar hankalinta da samun natsuwarta ,duk ita tajawo komai daya faru dasu sai dai bata bakinciki da hukuncin da mahaifina ya zarta akanta …
har suka shigo harabar gidan kuka nasreen take, taki fitowa daga cikin motar sai da me’ad ta zagaya ta fito daita tashiga turturjewa ita sam bazata shiga cikin gidan ba “Dan Allah momy karki shiga dani banason gidan ….plz momy .
alhj ediris dake saman barandarsa tsaye idanunsa ya sauka akansu sai yau yagama k’arewa yanayin yarinyar kallo , kyakkywace kmr me’ad dinsa ,sai dai kusan yanayinta na ubanta ne ,abubuwa kad’an ta d’auko na uwarta ….
Haushi ne yakamashi ganin yadda ake dambe daita akan bazata shiga gidansa ba, to me hkn yake nufi kenan…?
Ransa a matukar ‘bace ya saki wata razananniyar tsawa tare da cewa “ki barta anan kishigo abinki idan bazata shigo ba ,wata irin gigicewa nasreen tayi tare da kwakume me’ad ajikinta “Wayyohlly Allah momy tsoro nakeji …..momy momy tsoro nake ji ki fita dani daga gidan nan tsoro nake ji …..
ahankalin me’ad yayi mugu mugun tashi take hawaye ya balle mata yashiga gudana a saman kuncinta, ahankali ta rungumeta ajikinta tashiga shafa mata kanta zuwa bayan “,cool down my baby nothing wel happen to you, just trust your mom….ki saki jikinki babu abinda grandpa zai yi miki he really loves you rarrashinta ta dinga yi yayinda har lokacin idanun dady ke kansu, ya kasa d’auke idanunsa akansu jiki a sanyaye me’ad ta yunkura tare da d’aukarta ta rungume kasancewar nasreen din bata da wani girma gashi babu kiba sai zallar farin fata da tsagwaron kyawun data d’auko daga iyayenta. …..
suna shiga cikin gidan me’ad ta kwantar da nasreen akan doguwar kujera 3 siter tana shafa kwanta yarinyar ta runtse idanunta gam batason ganin kowa har lokacin bata daina furta “tsoro take ji ba a fitar daita daga gidan .
Me’ad tasamu guri ta zauna a gefen kujerar da momy ke zaune ta zuba uwar tagumi tana zubarwa da hawaye saboda duk abinda ya faru acikin kunnenta akayisa “Sam bataji dadin furucin dady ba ,Amman tasan tana yin wata mgn nata ne zaiyi zafi .
me’ad ta kai hannunta zata cire tagumin datayi kenan suhailat tasanyo kai cikin parlour’n dawowarta kenan daga exam dinta karshe daga shi za’a turasu bautar k’asa.
da sauri ta k’araso ta rungume me’ad tana murnar ganin sai dai ganin yanayinsu ya sanyayar mata da gwiwa tayi tsuru tsuru tana kallonnsu zuciyarta na wani irin bugawa “aunty me’ad momy lfy na ganku wani iri ko wani abu ne ya faru da dady byn fitata?
Kuka momy ta fashe dashi sannan tashiga koro mata duk abinda ya faru .
wata irin zabura suhailat tayi tana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun sai maimata kalmar take hankalinta a matukar tashe cikin tsananin rud’u ,tana duban me’ad da wata irin gigitaccen duba muryarta a sarke tace ” me ya zanyo kikayi mummunar wannan tunanin anti?
Me’ad ta cije le’benta alamun damuwarta ta kai makura “ai kinga irinta ko anti?” kinga irin taurin kan naki ba ?
“gashi zaki yi sanadiyar kashe auren dake kad’ai kika San irin wahalar da kika sha akansa .
“watakilla da kinyi hakuri kin zauna ad’akin mijinki da yanzu duk hkn bata faru ba, Dan nasan ko bade dady zai yafe miki wallahi tallahi matsawar aurenki ya mutu ki sani kin yanki tikitin zawarci na shekara Goma sha…. ko fiyye da hakan ga dai karamin misali nan akan aunty sajida banda sauran mata da basamu sani ba ,me’ad tayi saurin runtse idanunta saboda sunan sajida da suhailat ta ambata.
Suhailat tacigaba da mgn ” kin guji mijinki Dan zai k’ara aure ke yanzu a tunaninki idan aurenki ya mutu mara mata ne zai zo yace yana sonki zai aureki?
Sam ki canza tunani ki koma kibawa dady hakuri ya janye wannan furucin NASA …suhailat takarasa maganar da sheshekar kuka Wanda ya k’ara dama lisafin me’ad har ta kasa kuka illa girgiza kai kawai datake kmr wata kadangaruwa..”take ciwon so yashiga dawainiyya daita a zaune datake ahankali ta sake runtse idanunta gam fu’ad zuciyarta tasoma hasko mata ,” ta yaya zata iya rabuwa dashi ? Anya kuwa bata yaudari kanta ba ? Ta bude idanunta tare da zubawa suhailat ido gbdy ta kasa mgn suhailat ta sauke wata ajiyar zuciya mai bayyanan ne ciwo akirji “bari naje nasamu dady Dan Allah ya sausauta rayuwarma guda na wace ,idan da sauran zama tsakaninku sai rabo yazo ya kasheshi azo ana kuka…..
ganin ta yunkura ta Mike me’ad tayi saurin meidata mazauninta “kiyi hakuri suhailat karkije ni kad’ai nasan kunci Dana shiga a sanadiyar fushinsa gareni, yau nasamu da kyar ya sauko har ya sake amincewa dani amatsayin diyarsa, Dan Allah karkiyi abinda zai sa a sake maimata tarihi fu’ad dai ni na kawoshi nace ina sonshi a yau kuma nace banasonshi …..
dan kowa ya d’auka wata halaka ko dangantaka bata ta’ba shiga tsakaninmu ba ..
tana gama fad’ar hk ta mike hawaye nabin kuncinta tashige d’akin momy ta fad’a kan gado, ta kwanta ruf da ciki ta fashe da wani irin gigitaccen kuka “na barka bari na har abada kai din ma baka cancanci na sake butulcewa mahaifina akanka ba ,kai din maci amanar kauna ne gareni Allah yasa rabuwarmu tazama alkairi a rayuwata Allah ya had’a kowa da rabonsa na alkairi…..
**********
Bangaren mahaifin sajida kuwa daga gidansu me’ad kai tsaye gidansa ya nufa ana k’ok’arin bud’e masa get idanunsa ya sauka akan Khalid da wasu daga cikin security’s din bakin get ke dambe dashi na lallai sai an barshi yashiga gidan ,ai kuwa ana k’arasa bud’e masa ,atare suka shiga gidan .bayan direbansa yayi parking a inda aka tanada domin ajiye motoci da sauri ya fito batare daya rufe murfin motar ba ya k’araso bakin kofar da mahaifin sajida yake ,ya bud’e masa kafafunsa yasoma sanyowa waje sannan gangar jikinsa ta bayyana inda gbdy security’s suka caaaa akansa kowanensu na rusunawa cike da girmamawa shima Khalid yakaraso yayi kmr yadda sukayi mahaifin sajida yabishi da kallo yana tunanin inda yasansa Amman duk tunaninsa yayi bai gano inda yasan yaron ba ,juyowa yayi ga security ganin K’arin bayani yake nema daga garesu yasa suka shiga rige Rigen gaya masa abinda ke tafe da Khalid ya jinjina kai yana sake karewa yaron kallon tsab yaro ne karami sosai Dan nesa ba kusa ba yasan sajida ta girme masa zatayi kani kusan na uku dashi hannun mahaifin sajida ya d’aga musu alamun suka gamansu sannan yace wa Khalid “biyo yaro ,yana gaba khalid na biye dashi abaya har cikin wani rantsentsan parlour’n dayaji kayan more rayuwar duniya yace ya zauna yana zuwa ,shi kuma yak’arasa ciki ,Khalid ya zauna tare da yin balance yana murza tafukan hannuwansa tsanyi ac Dana murna na ratsashi tmkr Wanda akayiwa albishiri da an bashi auren sajida.
Mahaifin sajida nashigowa parlour’n sautin muryarta yasoma jiyowa cikin fad’a “Dan iskan yaro kawai ko me zanyi da kai ?
“me zan ci da kai yaro karami da kai sai tsaurin ido ,okay Dan kaga ranar farko kayi nasarar shigowa, shine yau ma ka kwaso jiki kazo Allah yasa suyi maka dukan mutuwa su karairaka useless kawai, tana ganin mahaifinta tayi saurin waske tana susa tsakiyar gashin kanta sannan tayi masa sannu da zuwa ,ya amsa ransa a sake sannan yashiga d’akinsa bayansa tabi da kallo tana adduar Allah yasa bai ga Khalid ba .