YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 51 to 60 (The End)

shigarsa d’akin bai fi minti goma ba ya sake fitowa ya nufi inda Khalid yake bayan ya bada umarnin akawo masa abun motsa baki . Yashigo bakinsa d’auke da sallama, Khalid na ganinsa ya sake rusunawa had’e da amsa sallama ,mahafin sajida yasamu guri opposite din Khalid ya zauna 

 yana fuskantarshi, tsawon minti goma yana zaune yana kallon Khalid tare da nazarinsa ,me aiki tashigo rike da tire ta janyo karamin stood ta ajiye tiren akai ta juya .

“meye ne sunanka mahaifin sajida ya fad’a yana gyara zamansa?

 Cikin rawa murya yace “Kha..Khalid ismail money mis road ne sir..” dady ya maimaita sunan saboda yasan Ismail mony mis road, ya jinjina kai kana yace 

“malam Khalid ga abun motsa bakin nan kasoma dashi tukun muyi mgn ”

“a koshe nake dady “kai kuwa kasha ko kad’an ne “ok na gode sosai ,yasa hannu ya tsiyaye tattaciyar ruwan inibi acikin cup ya cur’ba kad’an ya ajiye cup, yana sake gyara zamansa shima ya fuskance mahaifin sajida kmr yadda yayi masa kuri da ido . “Kace Khalid Ismail mony mis road kai din D’an cikinsa ne ?

“Eh …..”ikon Allah”

” me ke tsakaninka da sajida diyata? 

Batare da ‘bata lokaci ba Khalid ya zayyane masa komai .”ka tabbatar kana sonta ?

Khalid yace “sosai ma dady sai dai ita din ce kmr take raina ni a cewarta na….”ka manta da duk wani raini kai dai ba dai kana sonta ba kuma kana da inda zaka ajiyeta ba ?

Khalid ya girgiza kansa alamun Eh ” to ka turo min mahaifinka muyi magana ta kunne da kunne dashi yana gama fad’ar ya Mike “kayi k’ok’arin ka ci duk abinda aka kawo maka sannan ya juya ya fita daga parlour’n, ai ko babu kunya khalid ya zauna ya take cikinsa ,Dan yana son cin irin abubuwan Amman mugun son kudinsa daya gada Gurin mahaifinsa baya bari fitowa yayi yana d’ad’d’agawa security’s kafad’u ,a zuwan shima yanzu wani ne acikin gidan.

*************

 Sajida fu’ad zaune agaban me gidansa, yayinda fu’ad sai faman cika yake yana batsewa tare da zabga mata harara ,saboda ya tsani yadda take zuwa kawo complain dinsa ga uban gidansa, daya zame masa tmkr uba garesa.

Cikin murya kuka tasoma mgn “sir Malik ka taimakeni kar zance aurenmu ya rushe gbdy narasa gane Kan fu’ad aka. ” dakata dakata !! Munafuka ta yaya zaki gane kaina, muguwa azaluma maci amanar kauna?

sir kana kallon yarinyar nan katuwar muguwar makira ce ta bugawa ajarida, kwata kwata batasona da matata, sannan son datake ikirari tana min karya ne…….

“Saboda zaka fadi hk ?

Inji cewar sir Malik “na karyata hkn ne saboda ina dalilina ,Dan da ace son gsky sajida take min da ta tausayawa rayuwata ta gaya min inda matata da ‘yata suke….

Kallonta sir malik yayi “ke kinsa inda matarsa take ne ?

Tayi saurin girgiza masa kai alamun eh ”

“Kaji ko Amman tana kallona agari ina yawo bulayin nemanta ta kasa gaya min to ni kuwa me zanyi dake sajida? 

“Bari nagaya miki wallahi wallahi bana sonki kuma ban taba jin digon sonki a zuciyata ba ,na dai amincewa aurenki ne saboda yanayin da kike k’ok’arin ganin kin sanyani ciki alhalin ni ba ma’abocin hkn bane . Sannan baki son matata sajida..”karka ce wallahi ina ..”short ya buga Mata tsawa “ta ina kike sonta? 

” tambayarki ki gaya min baya ga zuga min ita da kike okay kin d’auka ban sani ba ?

“Kisani bazan ta’ba aurenki ba ,ke ko mutuwa me’ad tayi bazan aureki ba …”karka fad’i sir malik yayi saurin katse shi ” wallahi wallahi aaaaaaaa karka rantse “wallahi bazan aureta ba wannan shine maganata takarshe daita yana gama fadar hk ya Mike ya bar parlour’n, durkushewa tayi agurin tana kuka “Dan Allah kataimakeni kace masa ya dawo duk abinda yake tunani ba hk bane ,wayyohlly Allah kuka take kmr wata karamar yarinyar “ki kwantar da hankalinki zan rarrasheshi zan sa yayi kaffaran rantsuwar da yayi InshaAllahu ke dai ki cigaba da addu’a idan da rabo sai ayi da wannan maganar ya kwantar mata da hankali ta wuce.

********

Bayan mead ta dawo gida da sati daya , fu’ad yasamu labari tana gidansu ,Dan haka yayiwa gidan diran makiya , inda ya iske dady a parlour’n farko na gidan ya hakince acikin kujera , yashigo bakinsa d’auke da sallama , zuciyarsa babu wani fargaba ko tsoro ya gaishe da dady cike da girmamawa ,Wanda iya sallamar kawai dady ya amsa shima aciki , ya samu guri ya zauna batare da anyi masa izini ba .

parlour’n ya d’auki shiru kusan minti talatin dady bai tambayi abinda ya kawosa ba, hk zalika shima fuad bai yi mgn ba har sanda nasreen wacce tagaji da jiran , tasanyo kai cikin parlour’n Dan shigowar mahaifinta ya faru ne akan idanunta da gudu tashige jikinsa tana murnar ganinsa “I miss you my special dady…..shima rungumeta yayi tsam ajikinsa yana sauke naunayen ajiyar zuciya kana yace “I really miss you too my special bby how are you doing ?

“Am fine dady wani irin sanyin dadi ne yake jin yana ratsashi , yayinda zuciyar dady kad’an yarage batayi bundiga ba ,tsabar takaici da taanarsa ga fu’ad..

 ahankali sautin muryar nasreen ta fito “dady kazo tafiya damu ne ?

“Yes my bby jeki momynki ta fito mu wuce gida “gidan ubanwa kenan zata da kake mgn a gadarance?

“a’a fu’ad ya fad’a cike da matsanancin mamakin dady sannan yacigaba da mgn “wace irin mgn ce hk dady kake fad’a ?

“gidan mijinta mana zata”

” ‘Yarka me’ad ..?

“uhmmmmm ‘yarka ce sai dai ni kuma *matata ce ta sunnah* da duk ragamar rayuwarta ke tafin hannuna… ” yi min shiru , kasani me’ad ‘yata ce kuma ta dawo gidan ubanta bazata sake komawa gidanka tayi rayuwar kunci ba da babu ba ,Dan hk minti biyu kacal na baka ka bar min gida.

 “No no dady kar muyi hk da kai ,banason wata mgn ta sainsa tashiga tsakaninmu da kai saboda har yanzu kana nan matsayinka na uba gare….”dakata malam banason zance banza ni ba ubanka bane kasan ubanka, nima nasan iyakacin ya’yan Dana Haifa ”

“Okay tunda haka kace ina buƙatar *matata* abani *matata* na wuce daita muje tacigaba da rayuwar kuncin da babun da kace. 

Nan fa mahaifin me’ad ya fusata ” baka isa ba ,wannan zance banza ne ka fad’a, ayau kuma ayanzu zaka sauwakewa ‘yata igiyoyin aurenka dake kanta tayi rayuwar ‘yanci ”

“, a matukar fusace fu’ad ya mike tsaye jikinsa na wani irin rawa yana yiwa mahaifin me’ad din wani irin kallon me cike da tsantsar tsama .sannan muryarsa a kausashe yace .

“Wai daddy me kake nufi dani ne,?

” me nayi maka ne daddy me na tare maka arayuwa, kake min irin wannan kiyayyar.?

” shin a rayuwa ba a aure ne ko ba a soyayya ne na taimaka na auri ‘yarka domin mu rufawa juna asiri, after ina sonta, kuma ita ma kasan tana sona, ka bani *matata* kawai mu koma gida mu je mu ci-gaba da rayuwar aure da ita”

 dady yace” baxan ta’ba barin ka tafi da ‘yata koina ba, sannan ina da dalilai da yasa bana sonka , kuma har abada bazan ta’ba kaunar ka ba, saboda ni Safwan nake son tayi rayuwa dashi ba kai ba me digirin zero …….

Ka saketa tun wuri tun bamu had’u a kotu ba taje ta auri Safwan shi ne abinda nake buƙata kuma wannan ne cikar burinna a rayuwa me’ad ta auri safwan…..

Furzar da wani numfashi mai zafi fu’ad yayi sannan lokaci daya ya kwashewa da uwar dry yana furta “Good naji duk abinda ka fad’a amma Ni ina son *matata* kuma baxan ta’ba sakinta ba, kuma ko kotun duniya zaka kai ni ,ka kai ni a shiryena Nike Amman bazan saketa ba , duk runtsi duk wuya duk talaucina muna tare , “dady idan duk duniyar zasu taru akanmu bayan kotun dakace , idan sama da kasa zasu had’u, idan za’a dinga hadari malaiku daga sama bazan saki *matata* me’ad ba, kuma idan har sai na saki me’ad sannan Safwan xai yi Aure,wallahi wallahi wallahi!!! sai dai Safwan ya koma ga Allah bayi aure ba, ko kuma ku yi aure a kan aure” yana gama fadar haka ya juya afusace tare da nasreen ya bar parlour’n, zuwa harabar gidan ,me’ad wace tun shigowarsa gidan ta kasa samun natsuwar zuciya sakamakon nasreen tagaya mata zuwansa ” ta fito aguje tana haki ta rike hannun nasreen dake kuka saboda tashin hankalin daya faru akan idanun “sakar min hannun yarinya ……….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button