YANCIN KI 1-END

YANCIN KI Page 51 to 60 (The End)

ya tsaya tare da juyo idanunsu ya tsarke cikin juna, atare zuciyoyinsu suka buga, ido cikin ido suke kallon juna me’ad ce tayi saurin d’auke idanunta acikin NASA “uhmmm repeat what you just said now? 

“Yarki ko ‘yata ?ya furta muryasa a kasalance tare da tsareta da kyawawan idanunsa. 

“Tambayarki nake kinyi shiru ,okay kema kin San gaskiya ko wannan property din belongs to me, kmr yadda mahaifinki ke kokari motsa kunjinsa akanki Dan hk sakar min hannun yarinyar..durkushewa tayi agabansa ta fashe masa da kuka “kabar min yarinyata ,idan ka rabani da ita mutuwa zanyi ,Dan Allah kabar min ita ..ahankali ya saki hannun nasreen sakamakon wani tunani dayayi ,barin nasreen zai iya taimaka masa takowani fanni, wallahi this time around zai bawa mahaifinta mamaki zai zame masa kadan garen bakin tula….rungume nasreen tayi ajikinta tana kuka shi kuma ya juya ya isa yashiga motarsa ya bar gidan ..

Bangaren dady kuwa sai zariya yake a parlour’n, ya kai gauro ya kai mari “aikin banza akin wofi kawai wannan yanzu har surukin arxiki ne?

” ina fad’a yana fad’a, koda yake tsiya da talauci babu abinda basa saka mutun yayi ,sai dai ka rubuta ka’ajiye sai na raba wannan auren koda kuwa da karfin ikona ne …..

Mmn sudais ce

????????????????????????

       ‘YAN CINKI

      ????????????????

????????????????????????

             ~NA~

 *AYSHA A BAGUDO*

     ~DEDICATED TO~   

 *AUNTY BASEERA WANNAN PAJIN NAKI , INA MATUKAR GODIYA BISA GA SOYAYYARKI , ALKHAIRINKI,KULAWARKI GARENI ALLAH YA BARMU TARE*????????????????????????

Page 81

…..kai tsaye fu’ad gida ya nufa zuciyarsa na wani irin tafarfasa,yana shiga parlour’n ya fad’a Kan doguwar kujera 3 siter yana fitar da numfashi me gauraye da zafin ciwon abinda surukinsa yayi masa ,ahankali tunaninsa ya cigaba da gudana lokacin daya sautin kukan matarsa yashiga dawo masa tana bashi hakuri”kabar min yarinyata, idan ka rabani daita mutuwa zanyi …”Dan Allah kabar min ita ….

runtse idanunsa yayi sosai tare da mikewa zaune da kyar, gabadaya ilahirin jikinsa yayi mugu mugun sanyi, ga wani irin matsifaffen ciwon da kansa keyi akan furucin mahaifinta ga tashin hankali daya barota ciki , da kyar ya iya bud’e idanunsa ya Mike tsaye yashiga zariya acikin parlour’n dafe da goshinsa , yana tunanin mafuta ” ya Allah ka kawo min hanya me sauki da komai zai daidata gareni ,Allah kar kasa wannan bawa naka yayi nasara akaina …….”ya dade yana zurfafa tunaninsa ,bai San lokacin daya d’auka tsaye agurin ba, kafin daga bisani, ahankali ya d’aga kyawawan idanunsa ya saukesu akan wrist watch din dake d’aure da tsintsiyar hannunsa, karfe shadaya ta wuce da wasu ‘yan mintuna, tsaki yaja “hk kawai wannan tsohon na neman hadasa masa ciwon kai na babu gaira babu dalili ,a sukune yasoma tafiya zuwa d’akinsa yana ‘bal’bale botiran gaban rigarsa yana shiga bathroom ya k’asara cire kayansa gbdy ya watsa Kan kujera . 

Bathtub yashiga ya tsakarwa kansa ruwa, take yaji wata natsuwa ta musamman ta saukar masa tare da bin ilahirin sansar jikinsa ,ahankali kuma yake jin hankalinsa na kara kwanciya ko babu komai yasan halin da matarsa da ‘yarsa suke ,bugu da k’ari yasan inda suke Wanda a duk lokacin dayake da bukatar ganinsu zai gansu, wanka yayi shap shap ya fito kugunsa daure da towel fari ,while dayan hannunsa na rike da wani karamin towel yana goge sansar jikinsa dashi ,byn yagama goge jikinsa white boxer and white singlet ya saka yabi ilahirin jikinsa da turaren daya zame masa jiki ,sannan ya fad’a gadonsa zuciyarsa na matukar bugawa da karfin gaske.

“Dole duk runtse muna tare dake me’ad ,ko baki min halicci komai ba arayuwata bazan iya sakinki ba ,da zan sakeki da tuni bamu kawo wannan lokacin ba ,”ka saketa ko mu had’u a kotu maganar dayake tayiwa fu’ad yawo kenan acikin kwalkwaluwa ..dogon tsaki yayi inda zuciyarsa tashiga hasko masa kamannin safwa yayi saurin runtse idanunsa ya d’aura hannunsa akansa tmkr me shirin yi kuka yace” i a m mad iam stupid matukar nayi kuskuren sakin me’ad wa wani katon banza da wofi ..ina sonki matata duk kece silar fad’awarmu cikin damuwa ga wani tashin hankali na shirin afka mana. wayarsa ya janyo ya fara dialling number me’ad domin yaji muryarsa sannan ya kwantar mata da hankali Amman har 5 missed calls bata d’aga ba, tsaki yaja yayi jifa da wayar akan gadon “matsalar kenan taurin kai .

rungume hannunwansa yayi a saman kirjinsa yana kallon saman d’akin ,yayinda zuciyarsa ke hasko masa ita ji yayi hannunwansa daya rungume akirjinsa bazasu wadatar dashi ba ,yasa ya janyo pillow ya matse akirjinsa yana jin tmkr itace rungume ajikinsa, ahankali yana tunaninta ke fixgarsa ya kai hannunsa ya janyo bargo ya lullu’be jikinsa wani irin tsuma jikinsa ke yi tmkr zaki ga joystick dinsa sai mikewa take alamun tana bukatar abincinta wani tsakin yaja mtsssss hade da sanya hannuwansa duka ya dafe saman joystick da kyar yasamu bacci ‘barawo yayi awon gaba dashi cike da matsanancin kaunar matarsa ……

Washegari ya tashi tattare da kuzari da farincikinki yashiga bathroom yayi wanka ya fito ya shirya zuwa office ,gabadaya ya nemi tarin damuwarsa ya rasa sai zallar farinciki dake dawainiyya dashi ,haka ma a office aikinsa yake gudanarwa cike da kwanciyar hankali ,a cewarsa matsalarsa ta kau damuwarsa tak’are tunda yasan inda iyalinsa suke Dan shi Sam bai d’auki mgnr dady da wani mahimmanci ba ……

********

Alhj Ismail money mis road ya samu zuwa gurin mahaifin sajida bisa nemawa D’ansa auren diyarsa , inda har an tsaida magana me karfi atsakanin ,sannan an saka ranar aure nan da wata daya kacal me zuwa, mahaifin sajida ya hana Khalid sanar mata ko kusanta inda take har sai an kawo masa ita amatsayin matarsa ,haka zalika ya hana aunty nadiya ta fad’a mata ko yin wani abinda zai sa tagane .

   Anata shirye shiryen aurenta batare da saninta ba ,itama bata lura da yadda aunty nadiya ke zariya zuwa kasuwa ba ,lamuran gabanta kawai tasa agaba, na yadda zata mallaki fu’ad yazamo abokin rayuwarta, Dan har wata abokiyar aikinta datasan da mgnrta da fu’ad din ,tayi mata alkawarin Zata kaita gurin wani hatsabibin malaminta yayi mata aiki akansa, ta yadda da kansa zai kawo kansa gareta farinciki sajida tayi sosai sannan tace” banason na mallakesa ta wannan hanyar kafila ……”ai kuwa yadda yake da taurin kan nan da nuna isa ,bazaki ta’ba mallakarsa ba sai kin sa an rankwafar miki dashi tukun kisamu kansa “shikenan kafila zan bi shawarki but ki bari na sake tuntu’barsa zuwa nan da two weeks kafin muje nan suka bar mgnr zuwa sanda sajida ta fad’a…

**********

Me’ad tacigaba da zuwa gurin aikinta, sai dai har yanzu wannan lokacin bata iya shiga office dinta, dama cikin ma’aikanta gabadaya Dan chairman ya canza mata wani office kafin sanda za’a gama binciken su mudansir, Amman har lokacin jikinta bai daina mata tirin zafi ba Dan haka ta dawo zaman mota. 

Bangaren su mudansir kuwa, idan ka gansu ba zaka ta’ba ganesu ba ,adalilin dukan mutuwar da policewa suka yi musu, iya azaba an azabtar dasu saboda rashin fad’ar gsky da sukayi, kowane daga cikinsu kanshi yayi wani irin kunburi saboda azabar duka ,bama zaka iya tantance waye mudansir tahir ma’aruf ba acikinsu ,sai da mudansir yaga suna daf da mutuwa sannan yayi bayanin inda malamin dayayi masa aikin yake,kai tsaye gidan bokan da akewa lakani da malami wanda ko kusa bai dace da amsa wannan sunan ba ,saboda mugun aikinsa da kuma irin ta’asar dayake aikatawa, rashin imani had’e da rashin tausayi sune abubuwan da suka baibaye zuciyarsa , bashi da maraba da irin bokayen nan na kan tsaunaka ,domin kuwa kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da rikakken matsafi ne ,koda suka isa sun iske dubbanin jama’a tundaga kofar gidan har cikin gidan masu neman biyan bukata ,mutane na ganin rundunar polisawa na k’ok’arin shigowa kowa yashiga hankalinsa wasu ma tuni suka arci na kare kar a had’a dasu .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button